CHAPTER 2

1.4K 163 14
                                    

Kuma na gano wani Abu ashe dalilin da yasa kowa baya son na shine ina da kambun baka. Zul yace menene kambun baka? Tace nima ma haka taji ance.

Tashi yayi daga jikinta ya janyo manya manyan jakan ganye Wanda ta hada ma ko wani dabba kuma kowa da nasa. Kowa zai fita ya Nemo abin ci amma babu Wanda zai ci nashi har se ta dawo. Ta karba ta gani sai a hada guri daya a ci kowa da kowa a tare.

Daya bayan daya dabbobin suka dawo ciyawa suka kasa samowa saboda ayi ruwa komai ya jike hakan yasa tsuntsuwa daya tace a ciri gidan ta yarinyar tace ah ah baza a ciri gidan ta ba. Bude jakar fatan da take fita dashi tayi ta dauko tace wannan itace waraka (paper) yau da safe ta Tsinto sa rubutun ajami da ke kai take shafawa.

Taga ana wani Abu da shi ne da wani kara in an dangwali bakin ruwa amma batasan menene ba. Kofar gidan sarki ta tsinto sa kuma manyan gari kadai ke da shi sauran a tsimma suke abin. Gafiya ne yace ko de tsafi suke yi da shi?

Tace menene tsafi yace nima ban sani ba kamin ya fice da sauri saboda kiran da matar sa tayi masa cewa diyar su bata da lafiya. Daidai zai shige cikin rami tace toh mude bazamu iya zuwa gidan ka ba sai mun aiko muku abin ci.

Jeruwa sukayi yayin da ta hada kan itace ta dauko duwatsu guda biyu ta gurza har sanda ta tada wuta. Daura tukunyan tayi ta zuba ruwa rafi Wanda aikin zul ne kawo ruwa.

Wani tsimma ta ware, farin gari ne a ciki tace shekaran jiya na Sato mana tana dariya suma dariyan sukayi. Tace wai abin dandano ne bari mu gwada sawa. Tace in saka kadan ko dayawa? Zul yace kadan. Wani bushiya tace a juye duka.

Yarinyar tace toh yanzu duk Wanda ya yarda a saka kadan ya matsa gefen zul, dayawa kuma suje gefen shibi. Guda uku ne suka ce gefen ta hakan yasa yarinyar ta zuba kadan. Zafin da ya fara damun hannun ta yasa ta fahimci bazai yuwu ta rike tukunyan har ya dahu ba.

Saukewa tayi ta jingina suka fara nazarin yadda za'ayi tukunyan ta zauna da kanta. Har sun fara tunanin ko de kawai a ci abin cin yadda yake ne saboda yunwa da take kwakular su.

Zul ya Mike da sauri yace a daura akan dutse sai a kewaye dutsen da wuta. Ko da suka gwada hakan baiyi ba. Yarinyar tace toh me zai hana a kara dutse sai a saka wutan a tsakiya? Shewa sukayi kowa da irin sautin sa saide gaba daya ko wannen su tasan me suka ce sabanin sauran mutane da ke jin hakan a matsayin kuka.

Ganin biyun bai zauna ba yasa suka kara wani, a karo na farko suka taba ganin mukubur. Dafe kai yarinyar tayi saboda Sara Mata da yake yi tare da jin kamar ta taba ganin mukubur da wasu hotunan da take gani a kanta na bakin ciki. Kwanciya tayi tana kokarin tuna wani Abu daga cikin yarintarta. Abu daya da ta sani shine ta sha wahala.

Fuskan wani yaro guda Wanda zai kai shekara 14 kawai take gani Wanda tana da hotan sa da a Zane a wajen ta kuma shi ne ya bata. Abu huda da ta sani shine yayi Mata halacci kuma yaya take ce masa. Saide wasu abin bazata iya tuna su ba. Zaman jiran abincin dare akayi Dan yau ba'ayi na Rana ba saboda bata dawo da wuri ba hakan ne yasa suke jin yunwan da na fada.

Nan fa tsintsaye suka fara bada labarin yadda suka saci shinkafa a gonan mai gari. Dariya suka dinga yi harda kwantawa da daga kafa sama duk a cikin dariya😂ba abinda ke bawa yarinyar dariya kamar sanda wani dogari yayi kokarin harbo su ashe bai San bushiya na bayan sa ba tayi masa wankan kaya a mazaunai akayi fada dashi za'a cire masa a gaban sarki😂

Kamin mu Garzaya mu tattari ya namu ya namu mu fada masarauta, nasan kuna kusan me yasa ba ta da suna? Saboda tana da shekara hudu da wata 8 aka kore ta daga garin bata cikin mutane ba'a kiran ta da sunan ta sannan bata iya nagana ba yanzu saboda bata yi.

MASARAUTAR UNTO

Fitowan sa daga wanka kenan ya dauki rigan sa ya zira domin zai tafi wasa wuka da suka Saba yi duk karshen wata saboda motsa jiki daga nan sai suci abinci da mai martaba sa'ad wato mahaifin su

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Fitowan sa daga wanka kenan ya dauki rigan sa ya zira domin zai tafi wasa wuka da suka Saba yi duk karshen wata saboda motsa jiki daga nan sai suci abinci da mai martaba sa'ad wato mahaifin su.

Jakadan sa ne ya shigo durkusawa yayi domin ya masa fadan ci yarima mai jiran kujera yarima umar farouq yace masa ya mike. Miko masa kayan da zai saka yau jakadan yayi yarima farouq yayi masa nuni da gado. Har Izuwa yanzu bafadan bai dago ya kalli yarima ba sanin cewa babu tufafi kammalalliya a jikin sa.

Dukda cewa kaf masarautan hatta mai martaba baya kallon fara'ar yarima kamar yadda jakadan sa Ali yake kallon fara'ar sa hakan ba yana nufin yarima baya rufe ido ya ci mutuncin jakadan bane in har aka tabosa.

Shiyasa duk yadda suke shiri ko da wasa jakadan baya bari raini ta shiga tsakanin sa da uban gidan nasa.
Hannu yarima ya daga masa amma da shike kansa a kasa yake bai gani ba. Kafa yariman yasa ya shuri Alin hakan yasa shi fadin afuwa nake nema wajen yarima Allah yasa ba laifi nayi ba.
Tsaki yarima yayi yace zan saka wando ko shima zaka sakamin ne?
Cikin rawar kafa Ali yasan inda dare ya masa. 

.....

Tafe suke izuwa fadan sarki yarima ya hade rai akan dokin sa kuyangu da bayi russunawa suke suna  masu kaskantar da kai tare da miko gaisuwa. Gaban kowa ne ya tsinke lokacin da aka ji ya ce "ku dakata" cikin kakkausar murya.

Cak bafadun dake biye da shi da jakadan sa Ali kowa ya tsaya. Saukowa ya fara kokarin yi bafadu biyu suka hade hannun su akan ya taka ya sauka.
Kafa yasa ya hankade fuskan ko wannen su har sanda suka fadi.

Wani bawa ya dosa take zuciyar bawan nan ta tsinke Dan yasan yau in baije lahira ba toh tabbas tashin kiyama ce ta zo ta. Da sauri bafadu suka dago da wannan bawa dake russune kanshi na taba kasa, suka gofanar dashi a Kan guiwowin sa.

Kallon Ali yariman yayi hakan yasa  alin hanzartawa ya iso. Yana kallon nunin da yariman yayi masa ya fahimci me ke gudana hakan yasa ya ciro takalmin yariman daga kafan sa amma yana tsoron ya mika masa, yarima ya rike takalmi ? Da sake a zancen.

Jin shiru alin bai aikata komai ba yarima yace ko zaka sa ne? Da sauri yace tuba nake ran ka shi Dade, saide ina gani ba dacewan yarima bane ya rike takalmi. Murmushin gefen baki yayi kai da ka gani kasan ya shaka da zance karban takalmin yayi yace har mu isa fada kayi ta Marin kanka.

Takalmin da akayi ta da fatan zaki da 'kashi dake hannunsa ya dinga zabgawa wannan bawan a fuska har sanda bakin sa fashe, bai daina ba sanda hakorin sa ya fita. Yar da takalmin yayi daya daga cikin fadawan da ya ture fuskan su me suna gambo. Babban rigar sa ya saka ya goge takalmin tare da ajiye wa wajen kafan yarima.

Yarima umae kuwa wukan da ke makale jikin sa ya zaro ya ja baya tare da sawa a dago masa da fuskan bawan a hankali ya karta ❌ a goshin sa. Ba tare da furta komai ba ya hau saman dokin sa. "A kiyaye " shine abinda ya fada kamin suka dangana zuwa fada yana me kara hade rai tare da kankace idanu sai kace bakin kura.

TOH MUN DAI JI KADAN DAGA SASHIN YARIMA FA, SHIN ME ZAKU IYA CEWA? KODE YANA DA DALILIN YIN ZALINCIN NE?

INA TSIMAYIN COMMENTS DINKU,AYI VOTE FA

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now