Chapter 38

6.3K 509 53
                                    

Al-Hasan ibn Ali reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
"Leave what makes you doubt for what does not make you doubt. Verily, truth brings peace of mind and falsehood sows doubt"
Source: Sunan al-Tirmidhī

************

FAROUQ AL-HUSSAIN RESIDENCE
(GIDAN ZARA)

Kwance take a kan gadonta tana ta kuka.

A rayuwar Zara babu abinda ta tsana irin fushin Farouq.. Mugun tashin hankali take shiga.

Tabbas tayi nadamar abinda tayi domin kuwa ta gane cewa babban kuskure tayi. A matsayinta na matar aure bai kamata ta fita ganin wani ba tare da mijinta ya sani ba.. toh amma ai ba zuwa zata yi ta ga Mahmood don tana son shi ba har yanzu, she was only going to end everything between them. she wanted to explain this to Farouq but he refused to listen to her! why would he when tayi mishi laifi???

"Zara you are a fool, shouldn't you have just ended things with him on phone??? yanzu ga abinda na janyo ma kaina" ta fada cikin kuka.

Gaba daya ta rasa yadda akayi tunaninta ya gushe da har tayi wannan wautar... haka ta cigaba da zagin kanta tana kuka.

Tana nan kwance tana ta kuka ne cikinta ya fara yi mata ciwo... tun tana ta jurewa har dai abu ya fara fin qarfinta...

Haka ta dinga juye-juye a kan gado.

Zara dai ta sani sarai al’adarta ce ta zo..

Ni kuwa nace wrong timing!!

Da qyar ta lallaba ta shiga bathroom tayi wanka sannan ta kimtsa kanta.

Drawers din dakinta ta shiga budewa tana neman maganinta amma babu. Daga baya ne ta tuna cewa ya qare and she forgot to get it.

Jiki a sanyaye ta koma can gefe bisa tiles din dakin hoping zata ji sanyi...

Zara dai haka ta cigaba da juyi a qasa. Aikuwa bata taba jin zafin da take ji yau ba.. its definately because she is worried akan fushin da Farouq yayi da ita.

Wuraren qarfe daya na dare ne da ta kasa jurewa ta miqe jiki a sanyaye ta fita don neman taimako a wurin Farouq.

A daddafe ta qaraso dakin shi ta bude qofar sannan ta shiga.

Kwance yake a kan gadon shi, idanuwan shi a rufe amma ba bacci yake yi ba. Ya ji shigowarta  amma bai motsa ba balle ya bude idanuwan shi.

Zara wadda tayi zaton yana bacci kuwa sai ta kasa tayar da shi.

Gani nayi ta kwanta a qasa yayinda ta cigaba da juyi.

Farouq dai yana jinta amma yayi watsi da ita... Sossai ta bata mishi rai a yau. Just when he thought things will get better between them... why does she have to invite the guy to his house??? atleast ai ko bata girmama shi ba yakamata ta girmama matsayinta na matar aure. Is she this crazy????

Zara dai ta kasa jurewa at this point don haka ne ta tashi ta nufi gefen gadon shi tace “Ya Farouq”

No response!

BA SON TA NAKE BA | ✔On viuen les histories. Descobreix ara