Chapter 14

6.2K 494 25
                                    


Abu Hurayra reported that the Messenger of Allah, (PBUH), said, "Anyone who believes in Allah and the Last Day should not harm his neighbour. Anyone who believes in Allah and the Last Day should honour his guest. Anyone who believes in Allah and the Last Day should speak well or be silent." [Agreed upon]

**********

CENTRAL HOSPITAL
MAITAMA ABUJA

Farouq ne zaune a gefenta kan gadon da take kwance yayinda ya qura ma na'urar EKG din da take monitoring bugun zuciyar ta idanuwa.

Ya sani sarai qin kula ta da yayi ne ya sa ta shiga damuwa da har ciwon ta ya tashi.. He didnt know this was gonna happen, if he had known he wouldn't have ignored her the way he did.. Right now, he blames himself for everything and he pray she wakes up soon.

Gani nayi ya qura mata idanuwa.. a tsakanin dan lokaci kadan ta rame sossai.

"please wake up Zara"

Hannunta ya kamo ya riqe a cikin nashi yana ta shafawa a hankali yayinda yake ta addu'a..

Zara wadda ta dan motsa ce ta bude idanuwanta tace "Ya Farouq.."

Da sauri ya miqe tsaye still holding her hand yace "hey, you are awake??"

"Ya Farouq please kayi haquri..."

"Sssshhhh, how are you feeling?? ina ke yi miki ciwo??" Ya tambaye ta instead yayinda yake qoqarin sakin hannunta amma tayi sauri ta riqe shi gam.

Magana ta fara yi amma sam baya jin ta.. Babu shiri ya zauna kusa da ita tare da matsawa daf da ita don ya ji abinda take fadi.

Abba da Mamy wadanda suke kallon su ta gilas na ga suna murmushi..

"Babu shakka Farouq yana affecting rayuwar yarinyar nan, from labarin abinda ya faru da kika fadi mun dukda bamu san asalin me ya hada su ba I am sure a dalilin shi ne ta kwanta..."

"Ai tunda ta farfado zamu ji koma meye Abba... ni kam gani nake lokaci yayi da zamu cika burin mu akan su, ko ya ka gani??"

Abba yayi murmushi yace "nima ina tunanin hakan, bari ta kammala school dinta kamar yadda ta buqata, daga nan sai ayi proceeding"

A bangaren su Zara kuwa tana nan riqe da hannun Farouq yayinda ta kwanta a bisa.. she kinda used his hand slightly as a pillow..

Gaba daya har ta gama magana bai fahimci abinda take fadi ba.. a tunanin shi qila irin sabbatun nan na masu ciwo take yi.

Ita kuwa rufe idanuwanta tayi kamar tana bacci yayinda take shaqar qamshin turaren shi da take masifar so while enjoying the moment of having him stay close to her... Asali dai tayi hakan ne don bata so ya tafi ya barta.

Farouq dai gaba daya ya zama uncomfortable zaune a wurin don kuwa ya sani sarai su Abba suna kallon su... how can she use his hand as pillow??

he really should get himself outta this.. he thought!

Bakinshi ya kai saitin kunnenta yace "na san kina ji na, idan baki sakar mun hannu ba I will slap you"

Da sauri ta bude idanuwan ta tana kallonshi kamar zata yi kuka tace "toh idan na saki kar ka tafi ka bar ni.. please"

Farouq dai jin ta sassauta mishi riqon da tayi mishi ne ya zare hannunshi da sauri yayinda ya miqe tsaye.

"Yaaya ina zaka je??? please stay mana" ta fada tana yunqurin tashi zaune

"Zan fadi ma su Mamy kin farfado ne.. just lie back down"

Murmushi na ga tayi sannan ta koma ta kwanta yayinda ta sa mishi idanuwa har ya fita daga dakin.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now