EPILOGUE

9.6K 692 179
                                    

"The evidence that is specified in the Holy Quran in the clear words that human beings were created in pairs and hence you will end up with someone who belongs beside you"

***********

BAYAN SHEKARU UKU

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
ABUJA

Kwance yake akan makeken gadon dakin shi yana bacci.

Ji yayi ana ta birkita mishi gashin kanshi yayinda ake ja mishi gemu.

Idanuwan shi a rufe yace “please Baby angel, let me sleep mana”

“Abbu..”

Murmushi yayi tare da bude idanuwan shi ya gan ta zaune a gefen shi.

It's his daughter Amna...

Kumatun ta ya ja sannan ya janyo ta yayi hugging dinta yace “hello my Gorgeous Amna, how are you?”

“fine”

“where is your Ammi?”

“Ammi”

Girgiza kai na ga yayi yana dariya sannan yace “okay, I shouldn’t expect an answer from her, right??”

Zara ce ta shigo dakin riqe da Amal a hannun ta.

“hmmm, finally she has succeeded in waking you up”

Farouq wanda ya tashi zaune yana murmushi yace “ai na san da gangan kika kawo mun ita”

Amal ce ta miqa hannu wurin shi tana fadin “Abbu..”

Zara wadda ta miqa mishi ita ce ta matsa ta sakar mishi kiss a kumatu tace “good morning babylove, how was your night?”

Yana murmushi yace “thanks to you it was fantastic”

Tana dariya ta birkita gashin kanshi yayinda ya lumshe idanuwan shi..

Amal da Amna dai maqalewa suka yi a jikinshi kamar maguna...

Gani nayi yana girgiza kai yayinda ya kalli Zara wadda take ta yi mishi dariya.

“I am in trouble, yaran nan ke suka biyo wurin son jiki, na ga alama nan gaba kadan zaku qarasa ni”

Zara wadda ta zauna a kan gadon tana dariya ce tace “son ka muke yi babylove”

Kashe mata ido daya yayi yace “nima son ku nake yi ‘yan mata na, where is Hanan?”

“kasan Hanan ai, tana can tana directing masu aiki akan yadda zasu yi setting table, yanzu ma we came to fetch you ne”

“Ah okay, bari inyi wanka first”

Yana tashi kuwa su Amal suka fashe da kuka, kamar kullum wayoyin shi ya basu suna ta wasa da su sannan ya lallaba ya gudu yayinda Zara take ta yi mishi dariya.

**********

Zara dai ‘yan biyu ta Haifa mata wadanda suka ci sunan Mahaifiyarta da Mamy wato Zainab da Labiba amma ana kiran su Amal da Amna. Yaran Zara farare ne tas sannan kyawawa gwanin ban sha’awa.

***********

Su Farouq ne suka shigo dinning room din... Yana riqe da Amal yayinda Zara take riqe da Amna.

Hanan wadda ta gan su ce ta rugo a guje tayi hugging Farouq tace “Abbu good morning”

Kumatun ta ya ja tare da fadin “good morning my chubby bubbly, how was your night?” 

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now