Chapter 33

6.3K 464 32
                                    

Abu Umamah reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
"Whoever loves for the sake of Allah, hates for the sake of Allah, gives for the sake of Allah, and withholds for the sake of Allah has perfected the faith."
Source: Sunan Abu Dawud

***************


CUNNINGHAM MARQUEE EVENT CENTRE
ABUJA

Motar Amarya ce ta shigo harabar wurin yayinda 'Yan matanta da kuma abokan ango ke tsaye suna jira...

Ko da Sadiq ya faka motar sai na ga ya dauki wayar shi yayi dialing lambar Farouq.

“Ya Farouq gata nan na dauko ta”

Shiru ya dan yi sannan yace "Okay sir"

Bayan ya kashe wayar ne Hafsat tace “toh babes, ni dai bari in qarasa in dan yi coordinating kafin ki fito, sai mun hadu”

Hafsat tana fita daga motar ne Farouq ya shigo tare da kunna wuta.

"Wooow" na ji ya fada yayinda ya sa mata idanuwa babu qyaftawa..

Tana murmushi tace "what??"

Farouq na ga ya kalli Sadiq wanda ya zuba musu idanuwa ta mirror yana so ya ji me zai ce...

Buga kafadar shi yayi yace “guy, your job is done, I need some privacy please”

Sadiq ya fashe da dariya yace “sorry bro, I wanted to hear your flows ne I swear but I guess I will have to wait till another time... bari in tafi toh”

Bayan ya bude qofar ya fita ne na ga Farouq ya matsa daf da ita yace "Kin ga kyan da kika yi kuwa???"

Murmushi tayi tace "Yaaya kai ma fa kayi kyau sossai"

Hannunta na ga ya kamo yana shafawa... Wani irin mugun sanyi Zara ta ji yayinda zuciyarta take bugawa....

“na taba fadi miki cewa kin fi ko wacce mace kyau a duniyan nan?”

Zaro idanuwa tayi tace "What??"

"Yes Zara, You are very very beautiful... ban taba ganin macen da ta fi ko kyau ba"

Cike da murna da farin ciki tace "Nagode sossai Yaaya... I swear this means alot to me"

Hanunta da yake riqe da shi ne na ga ya kai saitin bakinshi ya sakar Mata kiss sannan yace "Let's go... everyone is waiting"

Zara dai tunda ya sakar Mata kiss a hannu ta kasa motsi... Haka ta bi shi da idanuwa har ya bude qofar shi ya fita....

within few seconds ta ji ya bude qofarta sannan ya miqa Mata hannu yace "let me help you.. come"

Murmushi na ga tayi sannan ta miqa mishi hannu ya taimaka mata ta fito...

Aikuwa Zara tana fitowa na ga Farouq yayi freezing a tsaye...

he was only checking her out by moving his eyes form her head to toe....

Gaba daya hankalinshi ya tafi a kallonta wanda ta kula da hakan... Snapping fingers dinta tayi saitin fuskarshi tace "Yaaya what happened?? na ga kana ta kallona ne... Kayana basuyi kyau ba ne??"

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now