Chapter 37

6.3K 581 70
                                    

Abu Huraira reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
"Avoid what I have forbidden for you and do what I have commanded you as much as you are able. Verily, the people before you were destroyed only because of their excessive questioning and differing with their prophets"
Source: Ṣaḥīḥ al-Bukhārī

***********

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
(GIDAN ZARA)

A yau wuraren qarfe goma na safe Zara ta fito harabar swimming pool din gidan.. she came out to stretch her legs.. Ni da nake kallonta sai na ga kamar tayi nisa cikin tunani.. Infact, she looked confused.

Mai karatu a yanzu dai Zara ta fara thinking twice akan barin gidan Farouq... she doesnt want to leave his house saboda yadda yake masifar kula da ita, he cares about her sossai, yana barinta tayi duk abinda take so, he treats her like a princess. She so much enjoy staying around him. At this point in time she has decided akan lallai bazata iya barin gidan Farouq ba saboda kamar yadda Mamy ta fada zata fi jin dadin zama da shi fiye da wurinsu, its actually true.

Farouq wanda yake working out a Gym dinshi ne ya hango Zara ta Glass wall na Gym din.

Asali dai ana hangen premises na swimming pool area daga Gym din a dalilin Glass wall da yake bangare daya na Gym din. Wanda yake cikin Gym din yana iya ganin swimming pool area din clearly but wanda yake waje baya hangen komai a cikin Gym din sai reflection.

Cike da mamaki ma ga Farouq ya matsa jikin glass wall din yana kallonta...

"what's she doing there???" ya tambayi kanshi because ya sani sarai Zara bata zuwa swimming pool area don bata iya swimming ba.

Aikuwa Zara tana tafe bata ankara ba sai tayi tuntube da resting chair din da ke gefen swimming pool din yayinda tayi missing steps dinta...

Ni da nake tsaye a gefe sai na hango Zara ta saki ihu yayinda ta afka cikin pool din...

Farouq wanda komai ya faru akan idanuwan shi ne na ga ya bude qofar da zata yi linking dinshi to the pool area ya fito da gudu yayinda hankalinshi yake a tashe...

A lokacin da ya qaraso kuwa Zara ta riga ta nitse a qasan pool din... ba tare da bata lokaci ba ya fada cikin ruwan don ceto ta..

Within few seconds na ga ya fiddo ta sannan ya kwantar da ita gefen pool din yayinda yayi turning kanta gefe saboda ruwa ya fita daga hancinta da bakinta... after a while kuma na ga ya mayar da kan nata to the normal position.

Ajiyar zuciya ya saki yayinda na ga yana kallonta briefly... he looked confused!

Wata ajiyar zuciyar ya qara saki sannan na ga ya kai bakin shi bisa nata ahankali ya fara bata Mouth-to mouth resuscitation tare da matse hancin ta, kunnuwan shi ya kai saitin bakinta tare da qura ma qirjinta idanuwa don ganin breathing movement dinta.

Haka ya dinga yi mata har kusan tsawon minti uku sannan na ga ta yunquro yayinda ruwa ya dinga fitowa daga bakinta.

Idanuwan Zara a rufe yayinda take kakarin amayar da ruwan da ta hadiye.

Farouq wanda yake riqe da ita ne yake ta jijjiga ta tare da shafa bayanta yana fadin “sorry my Baby angel, I am here”

Bayan ta fitar da ruwan da ta hadiye ne ta fara qoqarin yin magana yayinda yayi saurin dakatar da ita...

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now