Chapter 44

7.2K 525 97
                                    

Abu Tha’laba al-Khushani reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
"Verily, Allah has made duties obligatory, so do not neglect them. He has set limits, so do not transgress them. He has made some things sacred, so do no violate them. He has remained silent concerning things as mercy for you, not out of forgetfulness, so do not search them out."
Source: Sunan al-Dāraquṭnī

***********

CENTRAL HOSPITAL
ABUJA

Farouq ne zaune tare da daya daga cikin Medical laboratory technicians na asibitin mai suna Kennedy wanda zaiyi running mishi DNA test.

Kennedy yayi mishi alqawarin dawo mishi da result din before evening.

Farouq warned him akan baya so a samu kuskure ko alama and kennedy assured him there wont be error.

Bayan Kennedy ya fita ne Ruqayya ta shigo ofis din.

Farouq dai yana ganin ta ya ji zuciyarshi ta lalace gaba daya... Gaba daya Ruqayya ta fita a ranshi.

Itama din dai gani nayi ranta a bace...

“Honey meyasa tun jiya ina ta kiran ka a waya baka answering? asali ma tunda ka bar asibitin nan baka dawo ba. Ka manta cewa ka bar Junior a asibiti babu lafiya? You couldn’t even come to check on him this morning. Is Junior’s wellbeing not important anymore?”

Farouq wanda ya qura mata idanuwa sossai yake mamakin kanshi... How did he even end up with her?? what was he thinking when he married her??? he cant believe she cooked up a story and he bought it without investigating it thoroughly....

"Honey i am talking to you"

Gani nayi yayi dan murmushin takaici sannan yace “I had a serious headache jiya, how is Junior doing?”

“Ba wani nan. Kawai wannan fitinanniyar ta hana ka fitowa...."

Yana danna laptop dinshi na ga ya girgiza kai ba tare da yace komai ba.

"dama ina so in tambaye ka, wai me yake damun Junior ne?”

“Its fever”

“toh amma yaushe za’a sallame shi, Na ga ai ya samu sauqi kuma wallahi ni na gaji da zaman asibitin...”

“Zuwa yamma insha Allah...” ya fada sannan ya miqe yayinda ya cigaba da fadin “....bari in je in duba patients dina and I will come check on Junior afterwards”

Haka Ruqayya ta sa mishi idanuwa har ya fita yayinda take mamakin attitude dinshi... Farouq has changed, something is wrong... what could it be?????

**********

Ko da Farouq ya shiga duba Junior ya tarar da su Mamy, ya zauna yayi wasa sossai da Junior sannan anyi hira da shi normal....

Hatta Ruqayya da take tunanin akwai wani abu sai kuma ta ga kamar babu... He was super normal with her. Maybe she misunderstood him earlier...

Is it????

********

Da yamma Farouq yana zaune a ofis dinshi Kennedy ya kawo mishi DNA test result din sannan ya fita.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now