Chapter 28

5.7K 442 55
                                    

Mu’adh ibn Jabal reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
Allah the Exalted said: My love is obligatory for those who love each other for My sake, who sit together for My sake, who visit each other for My sake, who spend on each other for My sake.
Source: Musnad Ahmad

***********

Tun daga lokacin da Farouq ya shirya plan din auren su ne Zara ta kwantar da hankalin ta.

A yanzu haka ta qagara lokacin bikin ya zo ayi a gama har su rabu ta koma ma Mahmood dinta.

Wannan kenan!

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

LATE ALH UMAR JIMETA MANSION
MAITAMA ABUJA

Zaune yake rungume da ita suna ta hira kamar kullum.

“ina gimbiyar taka, na ji ta shiru bata fito ba? ko bata tashi daga baccin bane?”

Kafin yayi Magana ne Zara ta fito cikin rigar material doguwa har qasa. Gashinta buzu buzu wanda yake a tsefe, da gani kasan ma ya kwana biyu bata taba shi ba.

Kallon Farouq tayi sannan ta kalli Granny tace “ina kwanan ku”

Granny ce ta amsa yayinda Farouq ya bi ta da idanuwa babu ko qyaftawa... babu shakka tayi mishi kyau ne!

Zama tayi akan kujerar da take nesa da su sannan ta dauki remote ta canza channel zuwa tashar Zee Tv.

Granny ce tace “yau na ga ikon Allah, Yanzu muna zaman mu muna kallo zaki zo ki dauki remote ki canza mana tasha?? Mu muka ce miki muna son kallon India?”

Zara ta turo baki tace “toh wai ba fa kallon kuke yi ba, hira fa kuke yi”

Granny ta kalli farouq tace “wannan matar taka bata jin Magana”

Murmushi yayi yace “yi haquri Mi Lady”

Agogon hannun shi ya kalla yace “ina ganin fa anjima zan koma Abuja”

Da sauri Zara ta kalle shi yayinda ta ji Granny tace “haba dai anjima, ai baka isa ba sai ka qara kwana biyu don kuwa na san idan har ka tsallake ka tafi bazaka qara waiwayo ni ba musamman idan ka auro wannan gimbiyar”

Farouq na ga ya kalli Zara wadda ta turo baki sannan yayi murmushi ya sakar ma Granny kiss a goshi yace “haba dai Mi Lady, ai na kusan dawowa nan gidan da zama, ke ce number 1 remember? I love you soo very much”  

Granny wadda ta kalli Zara ta kula ran ta ya baci.. ko meyasa??? Oho! 

“lafiya kike kallon mu? ko kishin ne ya motsa?”

“Allah ya sawaqe inyi kishi da ke, idan dai Ya Farouq ne nace miki na bar miki”

“qaryar banza, kamar bamu san lokacin da ciwon ki ya tashi ba har kika suma saboda yayi aure”

Farouq ne ya sa ma Zara idanuwa yayinda duk ta bi ta rude...

Cikin muryar kuka tace “haba Granny, ni na fadi muku haka?”

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now