Chapter 11

5.9K 457 27
                                    

Jabir also reported that the Messenger of Allah, (PBUH), said, "No Muslim plants something without what is eaten from it being sadaqa for him. Even what is stolen from it is sadaqa for him. And no one visits it without that being sadaqa for him." (Muslim)

**********

KHALIL MANSION
MAITAMA ABUJA

Hafsat ce zaune a kan gadon dakinta tana magana da Galiafahad a waya. Galiafahad dai wani shahararren fashion designer ne wanda ake ji da shi a qasar Dubai. they are actually discussing about her wedding dress wanda zai dinka mata..

Bayan ta gama wayar ne ta kalli Zara wadda take latse-latsen wayarta tana murmushi.

"Babes wai ban tambaye ki ba, me kike shirya mana ne na Birthday? Kin dai san ba haka nan zaki bar mu ba ko?"

"labarin da muke yi kenan da Sweetie, yace zai yi organizing party, I don't know whether to agree or not"

Hafsat ta bata rai tace "idan dai Mahmood zai hada party toh bazan je ba"

Zara ta ajiye wayarta a gefe ta kalli Hafsat tace "haba bestie, wai meyasa ba kya son Sweetie ne? the other day ma fa sai da ya tambaye ni"

"babes ni fa ba wai shine bana so ba, I don't like him with you ne... baku dace ba gaskiya"

Zara ta fashe da dariya tace "ke ai kin dace da Ya Muky"

"yi haquri qawa ta"

************

Wuraren qarfe takwas na dare ne Zara ta bar gidan su Hafsat.. A kan hanyar ta ne ta biya Frozenscoop don siyan Ice cream.

Ko da ta shiga ta siya ta fito tana shirin yin reverse ne wani mai mota ya shigo wurin da gudu, dayake waya yake bai kula da motar Zara ba sai ya gabza mata da qarfin tsiya.

Ihu Zara tayi a dalilin kan ta da ya bugu da steering yayinda qafarta ta taka birki.

Nan da nan mutanen da suke harabar wurin da wadanda suke ciki duk suka fito suka taru yayinda ake ta yi ma mutumin fada tare da bashi rashin gaskiya.

Zara dai ko fitowa daga motar ta kasa yi... Dafe kanta tayi yayinda jikinta yake ta rawa.. babu shakka she is still in shock!

Mutumin da ya buga mata ne ya qwanqwasa mata gilas din motar ta don ya bata haquri domin kuwa barnar da yayi mata yasan bazai iya biya ba.

Its actually an expensive Mercedes Benz! One you can hardly find around in town!

Zara wadda ta sauke gilas din tana kallon mutumin har ya gama magana bata san me yace ba..

Gani nayi ta daga mishi hannu sannan ta ja gilas din motar..

Mutanen da suka taru sun so ta fito su ga yanayinta amma ko alama bata bi ta kansu ba.

Hannunta na rawa ta janyo wayarta tayi dialling lambar shi... Wayar tana daf da tsinkewa ne yayi picking

"Hello, Ya Farouq don Allah ka zo"

A lokacin ya baro asibiti kenan yana kan hanyar zuwa gida.

Cike da masifa yace "are you mad? In zo ina?"

Fashewa tayi da kuka tace "yi haquri yaaya, I had an accident yanzun nan, ina frozenscoops. I am confused and i dont know what to do, I just... I am...."

Hankalin shi a tashe yace "subhanalillah, hey are you okay?"

"I dont know, please ka zo"

Daga nan ta kashe wayar ta kifa kanta wanda yake yi mata bala'in ciwo a kan steering...

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now