Chapter 9

5.9K 520 15
                                    

Abu Muhammad al-Hasan ibn 'Ali ibn Abi Talib said, "I memorised from the Messenger of Allah, (PBUH): 'Abandon anything that gives you doubt for what gives you no doubt. Truthfulness is peace of mind and lying is doubt." (At-Tirmidhi)
 
***************

AL-HUSSAIN MANSION
MAITAMA ABUJA

Washegari Da safe Mamy tana zaune a dinning room tana breakfast ne Farouq ya shigo.

Ahankali ya zagayo ta bayan ta ya rufe mata idanuwa yana murmushi.

Hannuwan shi ta shafa tana murmushi tace “My Prince”

Ya zare hannuwan shi tare da duqowa yayi mata kiss a kumatu yace “oh my Mamy, nayi missing dinki sossai”

Kujerar gefen ta ya ja ya zauna

“Nima haka my prince. Ya gajiya? Hope dai ka huta sossai?”

“yes Ma”

“madallah, How is Ruqayya?”

Ya janyo plate zai zuba abinci ne yace “she is fine... Abba bai dawo ba?”

“I think sai zuwa jibi insha Allah”

Haka dai suka cigaba da cin breakfast dinsu suna hira.

Zara ce ta sauko sanye cikin wani crazy pencil jeans da wata sleeveless top. Sossai tayi kyau...

“Mamy ina kwana”

“lafiya lau princess”

Farouq dai ko kallonta bai yi ba.. Hankalinshi gaba daya yana kan plate din abincin shi.

Kujerar da take gefen shi ta ja, kafin ta zauna tasa hannu ta birkita gashin kanshi tace “Ya farouq good morning”

Bata jira ya amsa ba ta dauki fork ta sa a plate dinshi ta dauko plantain ta kai bakin ta.

Mamy wadda take kallon su kuwa sai murmushi take yi.. addu’a take a ranta Allah ya cika musu burin su akan Farouq da Zara.

“meye haka? Baki da manners ko?” ya fada ran shi a matuqar bace.

Cikin shagwaba tace “Ya Farouq me nayi kuma?”

Tsaki yayi ya ture plate din ya kalli Mamy yace “Mamy I am off”

Mamy ta kalle shi cike da mamaki tace “har ka qoshi?”

“eh Mamy, I will check on you later” ya nufi wurinta yayi mata kiss a kumatu yace “I love you”

Mamy dai ta gane cewa saboda Zara ne Farouq ya tashi.

Hawaye na ga sun fara wanke ma Zara fuska yayinda ta sa hannu tana ta sharewa.

Da sauri Mamy ta taso ta rungume ta tana fadin “My Zara meye abin kuka kuma? Kin san halin shi ba tun yau ba, me zai sa ki damu kan ki? Qyale shi ki ci abincin ki, bana so kina sa ma ran ki damuwa saboda ciwon ki”

“Mamy meyasa Ya Farouq baya sona? Am I not his sister? I care about him but he doesn’t, why?”

“ba haka bane, on the contrary Farouq cares about you a lot, kawai bai iya expressing feelings din shi ba ne and you know it”

“toh amma..”

“qyale shi ki ci abincin ki, yaushe ne tafiyar ku Dubai?”

“jibi ne insha Allah Mamy”

“toh Allah ya kaimu”

Farouq dai ya fita cike da haushin abinda Zara tayi mishi, yarinyar gaba daya ta zame mishi matsala a rayuwa. He doesn't even know how to handle her anymore!!

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now