Chapter 5

6.1K 547 17
                                    

Anas reported that the Prophet, (PBUH), said, "None of you can truly be said to believe until he wants for his brother what he wants for himself." (Agreed upon)

***********

CIGABAN LABARI

MUKHTAR ABUBAKAR MANSION
MAITAMA ABUJA

Farouq zaune a falon Mukhtar suna buga game kamar kullum. Idan ka gan su a gaban TV toh fa labaru suke kallo ko kuma game suke bugawa.

Mukhtar ne yace “wai yanzu abokina idan ka tafi Germany dinnan har wata shidda zaka yi?”

“wallahi kuwa abokina, I really have to be part of the course, I am going to miss you guys”

Mukhtar yayi murmushi yace “and she will miss you the most”

“toh ai da ita zan tafi, after all bazan tafi Germany inyi wata shidda in bar ta anan ba”

Mukhtar ya girgiza kai yace “I am talking about Zara abokina”

Farouq yayi tsaki wanda daga nan bai sake yin Magana ba.

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

AL-HUSSAIN MANSION
MAITAMA ABUJA

Zaune take a qaramin falon Mamy inda ake fama da ita wurin kitso. Mai kitson duk ta bi ta jigata a dalilin rashin natsuwar Zara.

Kamar kullum idan aka yi kadan sai tace a tsaya ta huta.

A lokacin ne Farouq ya shigo gidan, dawowar shi kenan daga asibiti shine ya biyo don ya duba jikin Abba wanda ya dan yi rashin lafiya.

A gajiye ya shiga gidan domin kuwa surgery yayi har kala uku a yau din.

Ya tarar da Mamy a babban falonta inda take kallon labaru. Bayan sun gaisa ne yace “Mamy Abba fa? Ya jikin nashi?"

“yana daki yana bacci, da sauqi babu laifi”

“Allah sarki Abba, I am sure stress ne yayi mishi yawa...”

“there is no doubt.. He has been busy fa tun kafin bikin ka. ko tafiye tafiyen nan da yake yi tsakanin qasashe ai dole ya gaji”

Farouq yayi murmushi yace “ban taba ganin hardworking mutum ba kamar Abba, I am so proud of him”

Kafin Mamy tayi Magana ne suka ji ihu da qarfin tsiya wanda har sai da Farouq ya toshe kunnuwan shi.

Cike da mamaki ya kalli Mamy yace “meye haka mamy??”

Mamy tana murmushi tace “Zara ce ake yi ma kitso, kasan haka ake fama. Yinin yau haka zata qarasa shi a gaban mai kitso”

Tsaki ya ja sannan yace “wallahi Mamy yarinyar nan ta raina mutane, da girman ta zaki qyale ta tana wannan shirmen? is she a child???”

“haba Farouq idan tace yana mata zafi ai dagaske yana mata zafin ne”

Girgiza kai yayi yace “toh a aske gashin mana kowa ya huta” Mamy ta fashe da dariya tace “a aske gashin ta zama kamar namiji? Haba Farouq”

Wani ihun Zara ta sake yi wanda yasa Farouq ya miqe yayinda Mamy take fadin “kada dai ka bata mata rai don na san halinka”

Kwance ya tarar da ita kan kujera yayinda mai kitson tana zaune tana jiranta ta huta kamar kullum.

Ga kitso dai an yi rabi yayinda rabin kan yake a tsefe.

"what is happening here?” ta jiyo muryar shi kamar daga sama.

Da sauri Zara ta miqe tana kallon shi.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now