Chapter 45

7.1K 514 118
                                    

Sahl ibn Sa’d al-Sa’idi reported: A man said, “O Messenger of Allah, tell me of a deed which will make Allah and people love me.” The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
"Renounce the world and Allah will love you. Renounce what people possess and people will love you."
Source: Sunan Ibn Mājah

***********

ALHAJI ABUBAKAR BULAMA MANSION
MAITAMA ABUJA

Zaune take a dakinta yayinda tayi nisa a tunani.
Ruqayya dai ta zama confused akan komai da yake faruwa, ta rasa gane komai. Tunda Farouq ya auri Zara ya canza gaba daya. Gaba daya yarinyar ta janye shi. Yanzu haka tunda ya dauke ta suka bar qasar bai qara waiwayo ta ba.

A yau wata daya kenan da su Farouq suka yi tafiya. Wata daya rabon da ta gan shi, ko a waya baya kiranta... idan ta kira kuma it goes straight to voicemail.

Hajjaju ce ta shigo dakin ta tarar da ita cikin wannan halin... itama jiya ta dawo daga Dubai. A kwanakin nan bata samun zama sossai.

“wai ni kuwa in tambaye ki, har yanzu ba’a gama gyaran gidan naki bane ko kuwa wani gidan zai canza miki?”

Ruqayya wadda ta saki ajiyar zuciya ce tace “wallahi hajjaju ban sani ba, rabo na da Farouq yau kusan wata daya kenan, ko a waya baya kirana”

Cikin tsananin mamaki Hajjaju tace “shine baki taba fadi mun ba?”

“toh Hajjau kullum ba kya nan”

“Ke dauki waya ki kira mun shi muyi Magana, wannan ai wulaqanci ne” Hajjaju ta fada a fusace.

Ruqayya wadda ta fashe da kuka ce tace “ai baya qasar”

“what? Tare da matar tashi ya tafi?"

"Haka na ji labari"

"Amma dai kin bani kunya wallahi, ya za’a yi ace ‘yar qaramar yarinya ta qwace miki miji? Aikin banza”

Haka Hajjaju ta fita daga dakin tana ta masifa.

Ruqayya tana kuka tace “na shiga uku”

Gani nayi ta janyo wayar ta tana qoqarin kiran Musty ko ta samu sauqi..

Musty dai yau sati daya kenan da aka daura auren shi. A yanzu haka tun ranar da aka daura auren nashi bai sake bi ta kan Ruqayya ba.

Sai da ta kira wayar shi sau uku sannan akayi answering.

Ga mamakinta kuwa ba muryar Musty din ta ji ba. Muryar mace ta ji...

Cike da tsananin tashin hankali tace “ina mai wayar?”

“baya kusa, da wa nake Magana?”

Cikin mamaki Ruqayya ta bi wayarta da idanuwa sannan ta mayar a kunnen ta.

Cikin masifa tace “nace ki ba mai wayar, kina da hankali kuwa?”

Itama cike da masifa tace “what? How dare you? Who the hell are you to talk to me that way?”

Ruqayya ta ja tsaki cikin bacin rai tace “uwar dan shi... and you???”

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now