Chapter 1

11.8K 921 44
                                    

Abu Hurayra reported that the Messenger of Allah, (PBUH), said, "This world is the prison of the believer and the paradise of the unbeliever." (Muslim)  

*************

THUMBAY HOSPITAL
DUBAI

Kwance take a kan gadon asibitin, babu abinda ke motsi a jikin ta sai qirjinta wanda yake hawa da sauka a hankali. An jona mata na’urar EKG wadda take monitoring din motsin da zuciyar ta take yi a kowane daqiqa. Hannun ta na dama dauke da Cannula na drip.

Ahankali ya bude qofar dakin suka shigo tare da likita yayinda wata murse take biye da su a baya.

Idanuwan shi ya sauke a kanta yayinda hankalinshi yake a tashe.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon likitan yace “So Dr. Zayyad when can she leave?”

Dr Zayyad ya kalli Zara wadda take kwance yace “it all depends on when she wakes up, it might take days or even weeks”

Shafa gashin kanshi yayi cikin tsananin tashin hankali yace “can I stay with her for a while?” Dr Zayyad yayi murmushi yace “why not? I will be in my office incase you need me even though I am certain that she is safe with you”

Murmushi na ga ya dan yi sannan yace “how so?”

“you are her doctor, remember?”

Girgiza kai yayi yace “but you are in charge here”

likitan yayi dariya tare da bugun kafadar shi sannan suka fita tare da Nos din suka bar shi a tsaye yana kallon ta.

A hankali ya nufi gadonta ya zauna a gefe sannan ya qura mata idanuwa.

Bai taba tunanin cewa a rana irin ta yau zai zo Dubai ba, sai gashi Zara tayi sanadin zuwan shi babu shiri.

A duk lokacin da ciwon Zara ya tashi wani irin mugun tashin hankali yake shiga wanda shi kan shi bai san dalili ba. Yanzu haka ko da ya qura mata idanuwa addu’a kawai yake yi akan Allah ya bata ikon farfadowa da wuri.

Yayi kusan minti goma sha biyar yana monitoring din EKG machine din, Ajiyar zuciya ya saki sannan ya kai hannun shi ya dan taba hannun ta na hagu.

Kamar wadda aka yi ma shocking ta zabura ta riqe hannun shi gam.

idanuwan ta a rufe ta fara fadin “Ya Farouq.. Ya farouq… ya…”

“ssshhhh”

Bude idanuwan ta tayi wadanda suka yi jajawur tana kallon shi yayinda shima yake kallon ta.

Murmushi tayi mishi wanda ya mayar mata da harara yace “how are you feeling?”

Da sauri na ga tana bin dakin da kallo sannan ta kalli hannun ta da yake dauke da drip tace “me ya faru da ni? Ya akayi na zo nan?”

Fuskar shi a murtuke yace “they found you lying unconscious and so they brought you here..”

Ajiyar zuciya ta saki yayinda ta fara tuno halin da ta shiga a lokacin da ta zame ta fadi.

Wata na’ura ya danna wanda cikin seconds kadan Dr Zayyad tare da Nurse dinshi suka shigo.

Ganin Zara a farke ya ba likitan mamaki matuqa domin kuwa bai sa ran zata farka nan da kwanaki uku ba ma a yadda yanayin jikin nata ya nuna.

Ko da ya qaraso murmushi yayi yace “welcome back Mrs Farouq”

Cike da mamakin abinda suka ji likitan ya ce ne suka kalle shi da sauri... Farouq fuska a murtuke yayinda Zara take ta murmushi.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now