Chapter 16

5.9K 497 9
                                    

Abu Hurayra reported that the Messenger of Allah, (PBUH), said, "It is better for one of you to take a rope and carry firewood on his back than for him to go to a man to beg from him who then gives to him or refuses to." [Agreed upon]

**********

Farouq ne zaune cikin motar shi yayinda yake kallon Zara cike da mamaki...

How dare she command him to do something??

Kusan tsawon minti Goma sha biyar suna kallon juna yayinda suka qi matsawa daga inda suke.

Wata zuciya ce tace yayi tafiyar shi ya barta a nan yayinda dayar ta bashi haquri akan ya qarasa wurinta.

Tsaki yayi sannan ya ja motar zuwa inda take, kashe mishi ido daya tayi tana murmushi sannan ta zagaya ta bude ta shiga.

Aikuwa tana shiga ta sa hannu ta kunna wutan motar ta kalle shi..

"wow, Ya Farouq kayi kyau dayawa, I am jealous”

Farouq wanda ya juyo zai fara yi mata masifa akan kunna wutar da tayi ne na ga yayi freezing while staring at her beautiful face... Zara tayi masifar kyau, infact bata taba yi mishi kyan da tayi ba a yau din. Babu shakka her make-up artist did a fantastic job.

Zara wadda ta sa mishi idanuwa ce tace "Ya Farouq nayi kyau, I know... shall we???"

Wayancewa yayi yace "Kashe mun wuta"

"Allah sarki Yaya ka barshi a haka mana inyi ta kallonta, i swear kayi kyau sossai"

Wani irin kallo yayi Mata Wanda yasa tace "Okay fine" sannan ta kashe wutan.

Daga nan ya ja motar yayinda ita kuma ta fara latsa wayarta...

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

PEACHVINE MARQUEE EVENT CENTRE
ABUJA

Farouq da Zara ne suka fito daga motar yayinda na ga tana ta qoqarin gyara rigarta wadda take jan qasa.

Ba tare da ya jira ta ba ya nufi entrance na hall din yayinda na ga tana biye da shi a baya cikin sauri don kuwa yayi Mata nisa.. Gashi dogon takalmin da ta sa is not allowing her to catch up with him..

“Ya Farouq please wait for me” ya jiyo muryarta a bit far away from him.

Juyowa yayi ya hango ta a bayan shi tana tafiya da qyar.

Tsaki ya ja sannan yace "Unbelievable"

A lokacin da ta qaraso daf da shi ne ta dan yi missing steps dinta sai kawai ta sa ihu a dalilin kusan faduwa da tayi...

Farouq ne yayi saurin riqe ta...

Idanuwan ta a rufe yayinda jikinta yake ta rawa tace “thank you big brother, da na fadi kuwa sai na karye”

“open your eyes and move ko in jefar da ke a nan wurin, crazy girl.. Kina tafe ba kya kallon gaban ki”

Murmushi tayi tace "Sorry Ya Farouq"

Maimakon ta sake shi kamar yadda ya umurce ta sai gani nayi ta qara riqe hannun shi gam forcing him to walk side by side with her..

“...Ya Farouq ba wai bana kallon gaba na bane, takalmin da na sa ne dogo shiyasa fa”

“kinsan bazaki iya tafiya da shi ba wa yace ki sa shi?” ya fada cike da masifa.

Zara wadda take enjoying conversation din nasu tana murmushi tace “toh ai idan ban sa shi ba riga na zai ja qasa sossai”

A lokacin har sun shigo hall din suna Magana da juna basu san attention din mutane ya dawo kansu ba.

MC ne ya shiga praising dinsu a matsayin su na babban qawar amarya da babban abokin ango.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now