Chapter 7

6.2K 491 21
                                    

Abu Hurayra reported that the Messenger of Allah, (PBUH), said, "The strong man is not the one who throws people in wrestling. The strong man is the one who has control of himself when he is angry." (Agreed upon)   

***********

Ruqayya dai samun kujera tayi ta zauna ta fashe da kuka yayinda ta dafe kai tana tunanin qaryar da zata yi ma Farouq domin kuwa rabuwa da shi is not an option for her.

Bata taba sanin cewa Farouq ya gane ba, sannan abinda ya fi bata mamaki shine yadda bai fadi mata ba sai yanzu.

Sai kyarma take yi yayinda take ta kuka. Bata ankara ba sai ganin shi tayi ya fito daga wanka inda ya cigaba da shirin shi hanakali a kwance.

Bayan ya kammala ne ya haye gadon shi ya kwanta.

Ruqayya ta miqe tsaye jiki a sanyaye ta nufi wurin shi tana share hawaye ta zauna a gefen shi tace “Honey let me explain what happened please listen to me”

Farouq wanda ya qagara ya ji bayanin ta yace “I am listening”

Ajiyar zuciya ta saki sannan ta fara bashi labari kamar haka:

A lokacin da mahaifi na ya rasu, ni da Hajjaju mun kasance mu kadai a gidan mu, sai mai gadi a waje. Bayan ya rasu da wata biyar ne watarana da daddare ‘yan fashi suka kawo mana hari har cikin gida. Sun kashe maigadin mu inda suka samu damar shiga har cikin gidan mu. A lokacin ne..”

Kasa qarasa labarin tayi yayinda ta ta fashe mishi da kuka..

Da sauri Farouq ya tashi zaune cike da tausayinta ya janyo ta ya rungume yana fadin “its okay, you don’t need to go further”

Ajiyar zuciya Ruqayya ta saki yayinda ta ji dadin kalaman shi.

A duniya zata iya yin komai don ta kasance matar Farouq, she cant afford to lose him. Right now ta tabbatar yayi buying qaryar da tayi mishi..

Cikin sanyin murya ne tace “Honey, Zara..”

Yana shafa gashin kanta yace “Zara what? Zara qanwa ta ce, she is my baby sister so relax, babu abinda yake tsakanin mu”

Qara rungume shi tayi yayinda take cike da farin ciki marar misaltuwa.

Aikuwa a wannan daren for the first time soyayya lafiyayya ta gudana tsakanin Farouq da Ruqayya domin kuwa Farouq ya cire duk wani zargi a ran shi ya rungumi Ruqayya a yadda take.

Ruqayya kuwa kamar ta zuba ruwa a qasa ta sha don farin ciki.. she has sealed the problem!

************

Bayan su Farouq sun wuce Germany da sati daya ne Sadiq ma ya koma makaranta.

Kamar kullum gidan ya koma daga mamy sai Zara domin kuwa Abba kullum yana tafiye tafiye. Idan har yana Nigeria ma ba’a ganin shi sossai domin dai yanayin aikin nashi baya bashi lokacin kan shi balle na iyalin shi. lokutta kadan ne zaka gan shi a gida cikin iyalin shi.

Zara dai har yanzu tana nan tana aika ma Farouq hotunan ta kamar kullum tare da bashi labarin abubuwan da take yi. A bangaren Farouq kuwa ko ya gani baya yi mata reply sannan ita kuma bata damuwa da hakan.

***************

BAYAN WATA SHIDDA

AL-HUSSAIN MANSION
MAITAMA ABUJA

Kwance take a kan gadon ta tana ta baccin ta cikin kwanciyar hankali.

Qarar wayar ta ce ta tashe ta daga baccin da take yi. Tsaki tayi sannan ta janyo pillow ta toshe kunnen ta da shi. Haka wayar tayi ta ringing tana tsinkewa bata daga ba.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now