Chapter 8

6K 556 20
                                    

 Jarir ibn 'Abdullah reported that the Messenger of Allah said, "If someone does not show mercy to people, Allah will not show mercy to him." (Agreed upon)    

*************

WANENE MAHMOOD TAFIDA??
Mahmood Tafida ya kasance yaro a gidan Senator Isah Tafida, Mahood ya taso cikin gata na iyaye domin kuwa babu abinda ya nema da ya rasa.

Mahaifin shi ko a bangaren siyasa ba’a son shi domin kuwa duk wata kafa ta cin hanci da rashawa a bayan Isah Tafida take.

Asalin Mahmood ya faro karatun shi a qasar America inda har ya kai mataki na uku amma saboda rashin mayar da hankali da iskanci na shaye shaye da neman mata da ya sa a gaba ne aka kore shi daga makarantar.

Da wannan ne Mahaifin shi ya dawo da shi Nigeria inda ya saka shi a Nile University.

Mahmood dai ko da ya dawo Nile bai canza hali ba. Abokanen shi Munir da Nura suma ‘ya’yan manya ne a garin Abuja wadanda halayen su ya kasance iri daya. A kullum zaka gan su a club da ‘yan mata inda suke sharholiyar su har asuba.

Duka wata uku kenan da Mahmood ya shigo Nile University inda yayi tozali da Fatima Zara Al-Hassan wadda ta kwanta mishi a rai.

Wani ikon Allah Mahmood bai taba son wata mace ba kamar yadda yake son Zara. A tunanin shi zai iya barin halin shi idan har ya samu Zara.

A dalilin iya tsara ‘yan mata ne yasa ya siye zuciyar Zara. Hafsat dai bata son Mahmood ko kadan domin kuwa bata yadda da halin shi ba, a kullum tana kan ba qawar ta shawara akan ta rabu da shi amma sam Zara ta qi. Abu kamar wasa dai Zara da Mahmood sun qulla soyayya mai qarfi a tsakanin su.

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

CIGABAN LABARI

NNAMDI AZIKWE INTERNATIONAL AIRPORT
ABUJA

Da yamma ne Mukhtar ya je airport domin dauko Ruqayya. Yana nan zaune yana jiran isowar jirgin su ne wayar shi ta fara ringing. Ko da ya duba sunan abokin shi ya gani.

“abokina how far, gani a airport ina jiran wifey dinka fa”

a dayan bangaren Farouq yace “okay my friend, kar ka manta gidan nan da na maka bayani zaka kai ta, that’s her new house”

Mukhtar yayi dariya yace “ai bazan yi kuskuren kai ta Villa ba besides ba ita ta tsara yadda take so wannan din ya kasance ba? her bad”

Farouq ya fashe da dariya.

Sun dan taba hira kadan sannan ya ji ana bada sanarwar isowar jirgin.

Bayan sunyi sallama ne ya miqe don tarbar Hajiya Ruqayya.

Tafe take cikin qasaita da isa, tafiya take kamar bata so ta taka qasa. Sanye take cikin wata doguwar jallabiya baqa mai shegen kyau.

Idanuwan ta sanye da glasses ta riqe hand bag dinta yayinda wani ma’aikacin airport din yake biye da ita da akwatunan trolley dinta.

Ganin Mukhtar da tayi ne yasa ta dan yi murmushi sannan ta qarasa wurin shi.

Yana murmushi yace “Hajiyar mu barka da isowa”

Cikin isa tace “yaya na, mun same ku lafiya?”

“Alhamdulillah”

Daga nan ne yayi musu jagora zuwa parking lot inda ya faka motar shi aka saka akwatunan ta a boot sannan suka shiga ya ja.

************

Bayan sun hau kan hanya ne Mukhtar yace “ya kika baro oga?”

“he is fine, cant wait for him to join me”

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now