Chapter 28

5.7K 442 55
                                    

Granny ta kalli Farouq tace “Zaka yi fama da wannan yarinyar domin kuwa kishi gareta na bala’i, ba tun yau nasan ta ba”

Ta kalli Zara ta cigaba da fadin “...sai ki daura damara domin kuwa mata biyu zaki tarar”

Zara dai ranta a bace ta tashi ta bar musu falon...

************

Farouq dai yana ji yana gani Granny ta hana shi komawa Abuja.

************

Da daddare Zara tana zaune gaban Vanity mirror na dakinta daure da towel yayinda take shafa body oil a jikinta ne wayarta tayi ringing..

Mahmood ne!

Tana murmushi tayi picking call din...

“cutie yi mun kwatancen gidan...”

A yau dai Mahmood ya sanar da ita he is coming to Adamawa just to see her.. she was so happy to hear that. Hakan ya tabbatar mata da lallai yana sonta!

“Wow, I really cant believe you came to Adamawa just to see me... I am soo happy zan gan ka”

"Me too my Cutie, ai bazan iya jure kwanaki ban gan ki ba.. I just had to come"

**************

Farouq ne kwance a kan cinyar Granny suna ta hirar su da bata qarewa. Idanuwan shi a rufe yayinda take ta shafa fuskar shi cike da so... Gaba daya duk jikokinta ta fi son Farouq.. Bala'in son shi take yi kamar yadda shima yake bala'in sonta.

Gani nayi Farouq ta bude idanuwan shi da sauri a dalilin qamshin turaren ta da ya ji.

Zara ce ta fito all dressed up looking so very beautiful...

Farouq ne ya sa mata idanuwa babu ko qyaftawa.. she looked very beautiful!

“ina zaki je ne haka na ga kin ci gayu?”

“Mahmood ne ya zo...”

Zuciyar Farouq ce ta buga a dalilin kalaman Zara... Wani mugun kishi ne ya taso mishi amma ya danne. Da sauri ya rufe idaniwanshi yayinda zuciyarshi take zafi.

"Mahmood?? kin manta cewar aure zakuyi da yayan ki??"

"Granny please understand, Mahmood left everything he was doing a Abuja ya zo Adamawa just to see me fa.. besides ai ga Ya Farouq din anan, I am sure he wont say No"

Granny wadda ta zama super confused kasa magana tayi... She actually expected Farouq to say something amma yayi shiru.

"Granny sai na dawo"

Haka ta wuce ta fita yayinda Granny ta bi ta da idanuwa cike da mamaki..

“Yanzu kana kallo a gaban ka ta fita ganin wani qato and you didn't say anything????”

Murmushin takaici yayi ba tare da ya bude idanuwan shi ba yace “toh me zan ce mata Mi Lady?”

Granny ta girgiza kai tace “anya son da kake yi mata zai bari ka dinga tsawata mata kuwa? Kada fa ka biye mata tana abinda ta ga dama..”

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now