WASU MATAN

1K 84 14
                                    

Zaune take bisa tabarma tana tsintar shinkafar hausa yayin da take sauraron wakar hamisu breaker, a gidan redio da yar k'aramar salulata.Akalla baza ta wuce shekara talatin da takwas ko Arba'in ba sai mita takeyi "oh ni Saudatu,Ni wallahi na gaji da wannan rayuwa..
Ace ko y'ar shinkafar ga ta gomnati dai mallam ya sayo mana mu tuka amma yakiya,a'a ko da yaushe sai dai yace ........

" Mssstwwsss" Ta karashe maganar tna jan dogon tsakii,a lokacin da aka turo kyauren gidan tare da sallama , ciki ciki Inna Saude Ta amsa sallamar yayin da naga wata mata shiyar budurwa wadda baza ta wuce shekara goma sha bakwai ba ta fito daga cikin wani madaidaicin daki sanye da wata kodaddiyar Atamfa tayo wurin wannan mutumen da ya.........

Da sallama ya shiga cikin palon,kamar yadda ya sani hakkan ne ko yanxu , zaune take bisa kujerun da suka k'awata dakin tana charting a wayar ta kirar IPhone 12 plus ,karar talkamin da taji ne alamun an shigo yasa ta dago kanta tare da daga yasunta tayi waving dinai 👋 ma'ana (HI) ta ci gaba da chart.......

Da cups ya fara cin karo daga shigarsa cikin gidan nashi.....
Ko ina a hargitse yake, chan kayan wanke-wanke ne tsulii guda ba'a wanke ba,
kayan wanki ma duk a yashe suke ,
ga mallek yayi kashi bata zubda ba,
wani kololon bakin cikine ya tokare masa wuya a lokacin da ya ............

A duniya bata tantamar kaunar da Abban Khaleel Ke ma ta, shiyasa bata sama ranta cewa ita daya zata zauna dashi kamar yadda WASU MATAN Keyi in miji na son su sosai.

Guiwar ta tana sanyi ne a duk lokacin da ta tuna cewa uwar mijin ta ba san ta take yi ba .

Bawai tana tsoron kishiya bane, a'a tana dai tsoron abunda zai rabata da mijinta abun alfaharinta.

A wannan zamanin da muke ciki mutane ba tsoron Allah a cikin zukatan su bata san wacce za'a kawo mata ba.
Tasan halin WASU MATAN ba imani gare su ba shiyasa take jin tsoro.
"hmmmmm"ta sauke gwauran numfashi,
"Ina sanka fiye da kaina mijina" "nima ina sanki sosai umman khaleel"
ya fada yana kwaikwayon muryarta....

Ku Antayo domin jin yadda labrin yake

Zeesardaunerh ce💜


WASU MATAN✔Where stories live. Discover now