GIDAN KASHE AHU

By Maryam-obam

114K 3.7K 396

Labari ne akan yanda duniya ta lalace yara kanana suke zuba bariki, ba tare da sanin iyayensu ba...... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
17
16
18
19
21
20
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
Final

22

1.9K 108 11
By Maryam-obam

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 22*

Mas'ud sun Isa garin Zaria very late dan haka kai tsaye hotel ya nufa domin ya kama daki, a matukar gajiye yake sosai, burinshi bai wuce ya ganshi a kwance ba Yana hutawa ba, koda ya kama daki, saida yayi wanka kafin ya Kira waya aka kawo mai abinci, bayan ya ci ya samu ya kwanta Amma gaba daya baccin yaki daukanshi, sai faman juye juye yake ba komai yake tunani ba sai ranan daya afka ma yarinyar da bataji ba Bata gani ba duk saboda malaminshi yace mishi sai ya aikata hakan kafin ya haye......... Kalmar Innalillahi wa Inna ilaihira jiun ya furta tare da fadin maina aikata haka? Maina aikata na cuci kaina da kaina

Haka yaita sakawa da warwarewa tabbas bazai taba samun salama ba har Sai yaga wannan yarinyar ya roki gafararta tare dana iyayenta, domin yasan duk inda take tana kullace dashi haka ma iyayenta, bazai taba manta fuskanta ba har abada

Washe gari tunda Afrah ta tashi da asuba Bata koma bacci ba, jin jikinta take wani irin sakayau kaman an cire mata wani abu mai nauyi a jikinta, Aysha ce ta kalleta tare da fadin ya jikin naki

Ta amsa da Fadin da sauki, sai dai gaba daya jikina ji nake kaman an cire mun wani abu, jina nake babu nauyi

Aysha tace sai hakuri dama haka zakiji kafin daga baya ki koma normal ...... Nocking sukaji wanda yasa Aysha tashi ta nufi kofar tare da budewa

David suka gani sanye yake da kananan kaya, yayi matukar kyau hannunshi yasa agogon rolex, Amma wannan karan baisa chain din daya saba sawa ba, kamshin turaren shine ya cika dakin idonshi nakan Afrah

Aysha ta gaidashi ya amsa tare da tambayarta ya jikin Afrah din??

Tace da sauki

Karasawa yayi kusa da Afrah tare da zama dan nesa da ita Yana kallonta, lokaci daya duka suka bude baki wajen gaisuwa

Jin sun hada baki yasa sukayi murmushi, yace ya jikin naki

Tace naji sauki, hope kaina jikinka da sauki

Yace eh da sauki, in ina tare dake bana jin wani damuwa tare dani

Murmushi tayi..... Aysha tace bari inje in dawo inada lecture, Afrah tace ok sai kin dawo

David ya dauko kudi ya Bata tare da fadin tayi kudin mota, bayan ta amsa tayi godiya tare da fita

David kallon Afrah yayi tare da fadin kinyi breakfast kuwa??

Kaita girgiza mishi alaman a'a,

Yace why? Mai yasa bazaki ci abibci kisha magani ba, telephone din yayi dialing tare da fadin abunda za'a kawo

Bayan ya gama wayar ya zauna Yana ta janta da fira har aka kawo abincin taci sannan ya tambayeta ina maganinta? Nuna mishi tayi da hannunta tashi yayi ya dauko maganin tare da ruwa ya kawo mata, tare da Bata maganin tasha, saida ta gama ya amsa sauran ruwan ya ajiye, sannan ya kalleta tare da fadin Afrah ina son muyi magana mai matukar muhimmanci

Kallonshi tayi taga ita yake kallo dan haka ta dan juyar dakai inda lokaci daya taji ya ruko hannunta komai ya tuna kuma ya saki hannun nata oho, magana ya fara cikin wata irin murya kaman mai rada.....

Afrah inaso ki sani ina Miki son so, wanda nake burin inga na mallakeki, Afrah ban taba jin ina son wani abu ba a duniya kaman yanda nake sonki......

Ganin hawaye a fuskanta na zuba yasa yayi shuru yana kallonta..... Bai ce mata komai ba sai kallonta da yakeyi cikin tashin hankali da damuwa, wani irin ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin David dan Allah ka musulunta muyi aure dan Allah David Ina sonka bazan iya ruwa ba tare dakai ba ina mutukar sonka, da farko ina tsoran ka musulunta saboda nasan ba lalle bane dangina su amince ka aureni ba, Amma a yanda nakeji yanzu zan iya fada da kowa domin in sameka, wlh David sonka Yana tafiya dako wani jini dake gudana a cikin jikina, rayuwa ta bazata taba samun nutsuwa ba muddin ban sameka a matsayin miji ba.......

Hannunshi yasa ya fara share mata hawaye wanda hakan yasa tayi shuru tana kallonshi wanda takeji kaman ta rungumeshi ko zata samu nutsuwa

David jin tayi shuru yasa ya fara magana kamar haka, Afrah na tabbata ina sonki sai dai sonda nake miki bana jin zan iya canza addini na ba, domin na yarda addinina shine gaskiya ba naki b......

Cikin kuka tace wlh david addinina shine Gaskiya, ka yarda dani zan baka cikakken hujja akan hakan indai......

Yace ya Isa Afrah ki tsaya ki saurare ni tare da abunda zan fada

Shuru tayi Amma idonta na zubar da hawaye cikin damuwa da fargaban maganan David din

Yaci gaba da fadin Afrah ni nasan irin sonda nake miki bana wasa bane ina sonki da gaskiya a yanzu haka na yanke ma kaina hukuncin daya dace dani kuma naga shine hanya mafi haske a tare da rayuwa ta da kuma lahira ta, Afrah am now Muhammad...... Da sauri ta tashi tare da fadin what???

Lokaci daya ta fara girgiza kai tare da fadin David plz...... Yace Afrah plz stop calling me david bani da alaka da wannan sunan na fada Miki yanzu ni musulmi ne kaman ki

Afrah cikin kuka ta daga hannu tana fadin Allahu akbar Allahu Abkar Allah na gode maka, yau wannan ranan ta zame mini kaman wacce aka cemin an bani komai a rayuwa lallai Allah abun godiya ne..... Dan shuru tayi sannan tace David....... Oh sorry Muhammad bari dai in dinga cewa Md murmushi yayi yace duk yanda kika ce my baby but nafi son a dinga kirana da Muhammad din

Tayi murmushi tace ok Muhd mai yaja ra'ayinka har kabar addininka ka dawo musulmi

Yace Afrah wannan ciwon naki yasa na dawo musulmi, cikin rashin fahimta take kallonshi alaman Bata gane mai yake nufi ba, yaci gaba da fadin Afrah nasan ba zaki san sanadin wannan ciwon naki ba, Amma bari In fada miki, aljanu sun shigeki wanda na Kira pastor domin su...... Nan dai ya Bata labari tare da Fadin tunda malamin Nan ya miki addu'a kika warke na gasgata addinin musulunci, kuma nayi imani dashi, yau da safe naje gidan Malam inda nayi mishi bayani tare da neman Karin bayani akan addinin musulunci kuma Alhamdulliah na gamsu da bayanin da yayi mun sosai wanda na mudulunta a yau dinnan, sannan anjima zanje masallaci domin in amsa shahada a bainar jama'a

Afrah wani irin runguma tamai tana kuka tare da fadin Allah na gode maka da kasa wanda nake so ya gane gaskiya gaskiya ce.......

Dan janta yayi daga jikinshi Yana kallonta sannan yace Afrah akwai abunda yake damuna sosai

Cikin tashin hankali tace mai yake damunka David

Yace na tabbata Dad Dina ne ya turo miki Aljanu domin ya cutar dake tabbas Afrah ina sonki kuma bana son inga wani abu ya cutar dake bazan iya jura ba

Afrah tace David naji na gani komai zai faru bazan taba barinka ba, sai dai in bakai zaka juyamin baya ba, Amma duk ruwa da iska bazan taba barinka ba, naji na amince komai zai faru toh ya faru Amma bazan taba barinka ba, koda kuwa zan rasa rayuwa ta......

Hannushi yasa ya toshe mata baki alaman tayi shuru wani irin ajiyan zuciya suke saukewa su duka biyun cikin damuwa tare da kaunar junarsu

A hankali muhd yace Afrah ina son in aureki cikin wannan watan indai iyayenki zasu yarda, inaso mubar kasar gaba daya inaso inyi nesa da Dad Dina bana bukatar zama a wannan kasar domin bazan so wani abu ya sameki ba, tabbas in hakan ya faru bazan taba yafewa kaina ba

Afrah tace na amince za muje kaga iyayena muyi musu bayani nasan mahaifina zai fahimta

Muhd yace shikenan sai mu shirya muje idan kin warke koh

Tace A'a muhd na fi son muje gobe inaso inga mun wuce wajan

Murmushi yayi tare da fadin shikenan Allah ya kaimu sai muje, tace Ameen

Garin kano yau an tashi da sanyi kasancewar anyi ruwa jiya da daddare sosai wannan shine silan da yasa garin ya dauki sanyi mai dadi da shiga cikin zuciya

Sallaman hjy Fatima sukaji a lokacin Zainab na wanke wanke a tsakar gida, mama kuma na daki ita da Abba, amsawa zainab tayi tare da gaidata Amma ina hjy Fatima ko ji batayi ba domin a zuciye tazo gidan

Kai tsaye cikin falon gidan ta shiga inda taga su Abba da mama suna gaidata Amma ina Bata gaisuwar tasu take ba domin a hasale tazo gidin magana ta fara da fadin toh shanyayye mara zuciya yanzu har ni zance Afrah ta dawo gida amma taki dawowa saboda ta raina ni kai kuma ka kasa magana saboda an shanye ka, toh bari kaji ko ta dawo ko Bata dawo ba gobe Saturday za'a daura mata Aure ita da wanda nake burin ta aura dan haka saiku zauna cikin shiri kudi ta mika mishi a leda gashi milliyan biyar ne sadakin Afrah ne saika bata inta dawo har takai bakin kofa ta juyo tare da fadin gobe karfe biyu za'a daura auren saika shirya a babban masallacin dake anguwar mu tana fadin haka tabar gidan

Gaba daya daga mama har abba babu wanda ya iya furta koda wata kalma gaba daya shuru sukayi mama ce tayi cikin daki da sauri tana kuka

Abba ganin haka yasa yabi bayanta tare da fadin miye amfanin kukan da kikeyi

Cikin tashin hamkali tace wannan wace irin rayuwa ce? Yanzu tsakani da Allah bani da iko akan yaran dana haifa? Mai yasa yan uwanka suka tsaneni mai yasa suka kasa yadda da kaddara burunsu kullum su kuntata min nida yarana na, Toh bari kaji wlh wannan karan nima bazan yarda ba, inada iko akan yarana wlh bazan taba bari a daura ma Afrah aure ba muddin Bata so

Abba cikin mamaki yake kallon mama lokaci daya ya sauke ajiyan zuciya sannan yace kiyi hakuri inaso ki sani komai yayi farko Yana da karshe kuma duk mai hakuri Yana tare da Allah wlh nida kaina abunda ya faru yau ya girgiza ni, toh Amma Yana iya ban taba zata Yaya zata yanke irin wannan hukuncin ba....

Mama tace wlh kaji na rantse maka koh, muddin Afrah Bata so nima bazan yi shuru ba, domin na tabbata danginka basa kaunata dan haka su daina mun iko akan yara, abunda sukemin ya isheni haka......

Ganin hawaye tayi na zuba a fuskar Abba cikin tashin hankali take tambayarshi maiya faru

Bai Bata amsa ba yaci gaba da hawayenshi, gaba daya hankalinta ya tashi sosai, itama cikin kukan ta fara magama kaman haka, kayi hakuri nasan ko baka fada ba magana ta ne ya saka wannan kukan ina mai baka hakuri akan ka share hawayenka domin wannan hawayen da yake zuba daga idonka bala'i ne a gareni tabbas nasan abunda nake fada gaskiya ne kuma akan gaskiya nake, Amma idan shurun nawa shine zai saka farin ciki wlh na hakura suje suyi duk abunda ya dace tana fadin haka wani irin kuka mai karfi ya kufce mata tare da shessheka......

Abba yace Allah yayi miki albarka sai dai wannan kukan naki Yana nuna min maganan da kikayi ba har cikin zuciyarki yake ba

Da saurinta ta tsagaita da kukan da takeyi sannan tace wlh har cikin raina nake na hakura na barma Allah zabi, ina mata fatan Alkhairi

Abba ya rungume mama Yana shafa mata baya, tare da godema Allah daya bashi mata mai hakuri da sanin ya kamata mai kuma jin maganarshi

Zainab itama tana falon duk tana jin abunda yake faruwa itama hawayen takeyi tare da tausayin iyayenta da yar uwarta wacce bata san abunda akeyi shirin yi ba

David ya dade a wajen Afrah kafin daga bisani yace mata bari yaje ya dawo, zaije masallaci wajan malam, baiso ta fita ba Amma ta kafe wai tana son ta mike kafa tare da fadin Babu mai ganinta haka ya yarda ta rakashi Amma bai bari ta fita can waje ba, yace ta koma daga reception

Komawa tayi tana tafiya a hankali

Dai dai lokacin ya bude kofar dakinshi domin Yana son fita, caraf idonshi ya sauka a kanta cikin tsananin tashin hankali da firgici ya fara nuna ta tare da matsawa kusa da ita Yana fadim baiwar Allah dan Allah ki tsaya ki saurare ni.....

Tsayawa tayi tana kallonshi cikin mamakin yanda taga Yana kallonta, tare da fadin lafiya kuwa?

Yace na dade ina nemanki sai yau Allah yasa na ganki.......

Kasa ya zube yayi kneel down a gabanta

Afrah da tunda ta ganshi gabanta yake faduwa, ganin ya tsugunna yasa gabanta ya tsananta da Fadi tare da fargaban mai yake shirin faruwa da ita haka.......

Zuwan Aysha ne yasa Mas'ud kasa magana

Aysha ta karaso tana fadin Afrah lafiya maike faruwa

Mas'ud a kasan zuciyarshi ya nanata Afrah

Aysha ta kalleshi tare da fadin Kaman Hon Mas'ud dan majalisar tarraya

Kai ya daga mata tare da fadin eh

Tace wow wlh A tv na taba ganinka a cikin majalisa kana magana tun daga lokacin..... Sai kuma tayi shuru ta nisa tare da Fadin ashe zan iya ganeka a fili

Tashi Mas'ud yayi Yana kallon Afrah da take a tsorace tare da fadin idan bazaki damu ba inaso inyi magana dake ki bani number dinki

Kasa magana tayi sai Aysha ce ta bashi number din afrah din

Tafiya yayi inda gaba daya zuciyarshi take ta mishi saka da warwara akan Afrah din tabbas nina lalata ta domin na tabbata a budurwa na sameta dan haka dole in aureta.........




Maryam Obam

Continue Reading

You'll Also Like

40.7M 1.1M 42
When Arianna marries billionaire Zach Price to save her family, she doesn't expect to fall in love with a man who'd always consider her a second choi...