GIDAN KASHE AHU

By Maryam-obam

114K 3.7K 396

Labari ne akan yanda duniya ta lalace yara kanana suke zuba bariki, ba tare da sanin iyayensu ba...... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
17
16
18
19
21
20
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49

Final

552 20 8
By Maryam-obam

As Jin zantukan bakin Afrah yake kaman a mafarki domin baiyi zatonsu daga gareta ba a dai dai wannan lokaci ba, tabbas mahakurci mawadaci, a hankali ya furta kalman Alhmdlh tsarki ya tabbata ga Allah, lallai yau nafi kowa sa'a Afrah ban taba tunanin Jin kalman so a bakin kiba, kullum da wannan tunanin nake kwana nake tashi ashe zaki furta min rungume ta yayi sosai a jikinsa Yana sauke wani irin ajiyan zuciya tare da fadin zan zame miki gata zan nuna miki cewa lallai kin zaba masoyi mai kaunarki........ Tun daga wannan rana Afrah da As suka Killa sabuwar rayuwa, yayin da suka kara shakuwa da junansu sosai, tabbas duk wanda ya gansu yasan suna cikin kwanciyar hankali da Kuma kaunar junansu abun su gwanin sha'awa hutun Afrah ya kare sun koma America, inda As yake Shirin sama ma Zainab gurbin karatu itama a can domin ta dawo gurinsu da zama

Ta gefen Zainab kuwa ta rame tabbas sai yanzu take ganin laifin kanta na saurin fadawa soyayyar Mohd, ta tabbata Afrah yake so ba ita ba, kuma duk abunda yakeyi tasan yana biye mata ne soboda Afrah din, a yanzu ta burinta ya cika na ganin ta hada kan yar uwarta da mijinta sai gashi ita kuma tana kokarin rasa farin cikinta, Mai aikin gidansu ce ta bude dakin inda ta gaida Zainab tare da fadin mama tace in fada miki kina da bako a waje

Dan Bata fuska tayi sannan tace sau nawa nace miki in zaki shigo mun daki ki fara Neman izinina kafin ki shigo mun?? Cikin rawar murya mai aikin tace kiyi hakuri insha Allah Hakan bazai kara faruwa ba, Zainab Bata kulata ba sai tashi da tayi domin taga waye bakon da yazo wajanta har kuma mama ta amince akan taje, hijab kawai ta daura akan doguwar rigan dake jikinta ya fita kai tsaye Dan karamin bukkan dake gidan ta nufa tana Isa ta ganshi wani irin murmushi ne ya bayyana akan fuskanta Shima sakar mata murmushin yayi tare da tashi tsaye kuma karasawa tayi har inda yake inda take mishi sannu da zuwa tare da fadin Bismillah ka zauna mana duka cikin harshen turanci take maganan

Zama yayi bayan itama ta zauna yace Zainab maiya sameki haka? Naga kin rame sosai

Dan murmushi tayi wanda ake cema yafi kuka ciwo, sannan tace babu komai

Kura mata ido yayi lokaci daya Kuma ya sauke ajiyan zuciya sannan yace nasan akwai wani abu dake damunki, inaga zuwa yanzu mun kai matakin da ni dake babu boye boye

Magana ta fara da fadin ba komai bane yake damu naba sai tunaninka, tunda ka tafi kullum Ina cikin zullumi ko zaka dawo ko ba zaka dawo ba, zuciyata ta kamu da sonka da kuma kaunarka, tabbas nayi rashin hankali da har na bari nayi mugun kamuwa da sonka, nasan ba zaka taba sona ba domin ka bama yar uwata zuciyarka Kuma...... Dakatar da ita yayi da hannunsa tare da fadin karki kara fadin haka, Zainab karki manta Afrah matar aure ce taya zanci gaba da sonta bayan Hakan haramun ne

Inaso ki sani da farko naso Afrah son da ban taba tunanin zanyi ma wani irinsa ba, sai dai kuma Allah yayi ba matata bace ita, matar wani ce, tun zuciyata tana ganin kaman zan sameta wani rana harna cire rai da Hakan na mika duka lamura na ga uban gijina Kuma Alhmdlh wlh yanzu babu kowa a zuciyata sai ke, ke kadai kawai nake kallo baki da maraba da Afrah sai dai kawai ta nuna miki haske, Zainab na dade da kamuwa da sonki abunda yasa kike tunanin kaman bana sonki nasan kina da kikayi shuru kuma waya ban cika kira ba abubuwa ne suka faru....... Nan ya bata labarin komai harda musuluntar mahaifiyarsa

Zainab tace Allahu akbar, wlh nayi matukar farin ciki dajin wannan labari, Allah ya kara haskaka addinin musulunci da musulmai a duk inda suke, Mohd ya amsa da Allahumma Ameen

Shuru ne ya biyo baya inda yayi ajiyan zuciya sannan yace mata yana son ya koma America, Kuma yana tunanin yanda zai barta a nan, tace karya damu itama zata dawo nan da zama domin a yanzu ana shirye shiryen komawanta ne, yaji dadin wannan labarin inda ta tashi tace bari ta kawo mishi abun motsa baki, yace mata a'a baya bukatar komai domin kafin tazo mama ta bashi yaci abinci bayan na gama ne na dawo nan yanda zan samu Daman yin magana dake sosai, sannan na fadama mama komai harda musuluntar mahaifiyata Kuma tace zata fadama Abba inya dawo munyi magana da ita sosai, yanzu abunda ya rage shine muji wani hukunci Abba zai yanke a kanmu

Zainab tace insha Allah za muji alkhairi da yardan Allah.

Koda Abba ya dawo mama ta mishi bayani yaji dadin musuluntar mahaifiyar muhd inda yace zai iya bashi auren Zainab Amma yayi hakuri inta kammala karatu sai ayi bikin, Hakan yayi ma Zainab da muhd dadi sosai tun daga wannan lokaci suka kara shakuwa da juna tare da matsanancin son junansu

Muhd bai taba rike jikin Zainab ba, domin yasan yin Hakan haramun ne a yanzu wanda yayi baya ma duk da a lokacin baya cikin addinin musulunci Shima yana Neman Allah ya yafe mai, soyayya suke mai tsafta kaman yau tana zaune a daki kiranshi ya shigo cikin wayarta dauka tayi cikin sakin fuska tare da fadin my dear Ina cikin tunaninka kiranka ya shigo cikin wayata, murmushi ya saki daga bangarensa tare da fadin nida tunaninka ya dameni ai gashi na kiraki, bama wannan ba Ina hanyar zuwa kano inaso kimin tuwon semovita niyan kuka, sannan Kuma inaso in fada miki harda mum Dina zamu zo

Ai wani dariya ta saki cikin Jin dadi tare da fadin dagaske ko wasa

Dariyar Shima yayi tare da fadin dagaske nake, Dan shagwabe murya tayi tare da fadin shine baka fadamun tun jiya ba, Amma banji dadin Hakan ba gaskiya Amma ba damuwa inaso idan Kun karaso ka fadamun Dan ni da kaina zanma mum abincin da zata ci ban yarda taci nako inaba plz

Yayi dariya tare da fadin an gama madam, kashe wayar yayi inda ta tashi tayi kitchen bayan ta fadama mama cewar Mohd zaizo Kano harda mahaifiyar sa, zata daura musu abinci mama tace toh tasa mai aikinsu ta tayata, bayan sunje kitchen din suna aiki itama mama ta fito tasa hannu Kun San ance idan hannu yayi yawa yanzu za'a kammala aiki duk yawansa, cikin kankanin lokaci akayi abinci kala uku da abun sha, anyi ma Mohd tuwo kaman yanda ya bukata itama mum dinshi aka mata sakwara da miyan Egusi da yaji nama da Ganda hadi da dry fish, sannan akayi mata biriyani da farfesun kazan hausa, sannan sukayi zobo da Chapman

Bayan sun kammala suka Taya Mai aikin gyara kitchen din sannan Zainab tayi daki tayi wanka tasa wata rigan atamfa hadi da daura dankwali tayi kyau sosai, a zatonta zai kirata yace zaizo ya amshi abincin Amma sai taji sabanin haka, inda mama ta kirata tace ga Mohd da mahaifiyarsa sunzo, hijab ta dauka ta fito falon inda ta gaidata cikin girmamawa mahaifiyar Mohd ta amsa tare da kamo hannun Zainab tana ta saka mata albarka, inda suke ta fira da mama kaman sun saba, mahaifiyar Mohd tasa jallabiya baki da gyalenshi, tabbas ita da kanta tana Jin dadin shigarta sabanin wacce takeyi da, nan mama tace suci abinci mohd dai kunya yaita ji, inda mahaifiyarsa taita santin abincin haka dai har suka kammala aka kira sallah la'asar Mohd yayi masallaci mum dinsa Kuma tayi a dakin mama, suna fira har Abba ya dawo suka gaisa inda mahaifiyar Mohd ta kawo maganan aure Abba yace babu matsala ai ya riga ya bashi, Hakan yayi mata dadi inda take fada musu tare da danta zasu koma America da zama zasu zauna na kwana biyu a kano kafin su daga zuwa can, Abba yayi musu fatan alkhairi kana taba Zainab tsarabar data kawo mata haka taba mama itama, da zasu tafi Zainab ta dauko mata hijab din da tasa aka kawo mata kala har biyar mum din mohd nata saka mata albarka

Mahaifin David wato Mohd ya samu labarin musuluntar matarshi Hakan ya matukar bata mishi rai gashi sun bar kasar, duk wani abu da zaiyi na sihiri yayi Amma abu yaki aiki, Asiri gaskiya ne kuma yana ci, toh Amma yakan kama wanda yake sakaci da azkar idan mutum ya rike Allah yana kokarin kiyaye hakkin Allah toh tabbas duk wani mugun abu idan akayi mishi toh bazaiyi tasiri ba, ganin labarin musuluntar matar tashi ya baza ko ina yasa yace ya saketa ita ba matarshi bace yanzu tare da fadin babu shi babu David suba komai nashi bane yanzu hakan yasa ya samu salama wajan Yan uwansa mabiya addininsa Amma sun kudirin aniyar duk ranar daya canza magana toh za su dauki mataki a kansa, wannan kenan

Afrah ce zaune akan cinyar As tana ta faman zabga mishi shagwaba tana fadin ita gaskiya duk wani alama da mace mai ciki takeji toh itama tana ji.....

As dariya yayi tare da fadin ai nasan tun tuni na baki baby, bandai fada bane kawai so nake saikin fahimta da kanki, Dan turo baki tayi tare da fadin uhm bari muje nasan jirgin su Zainab ya kusa sauka, kallon agogon hannunsa yayi yace saura 30 minute ya iso bari muje yanzu kar sis tazo taita jira

Dariya Afrah tayi tare da fadin da kaga yanda ake turo baki wajanta kuwa, shima dariyan yayi suka fita gaba daya inda sukai mota kai tsaye airport suka nufa sun Dan Jira ma wani lokaci kafin jirgin ya sauka aka fara fitowa, Aida gudu Zainab ta fada jikin Afrah tana murna, duka sai tsalle suke inda As ya seta bakinsa dai dai kunnen Afrah yace karki manta bake daya bace kina jijjiga mun baby, dukan wasa takai mai yasa hannu a wajan yace aush sannan ya kalli Zainab yace sis welcome to America Zainab tace thanks my inlow dariya sukayi inda yaja mata akwatinta sukai mota

Zainab ta fara karatu yayin da Afrah kuma take shirin zana jarabawar karshe, cikinta yana ta girma Zainab nata faman mata dawainiya As yace zasu koma Nigeria ta haiyu Amma Afrah tace ita Sam a nan kasar zata haiyu harta mama tace ta dawo gidaa tace a'a ita a nan zata haiyu inta dawo gida dawa zata bar kanwarta mama tace ga mahaifiyar Mohd tana kasar Afrah tace ma mama ita ayi hakuri anan take son haiyuwa badan mama taso ba ta kyaleta, itama mum taso su dawo ganin Afrah Bata Ra'ayi yasa sukace su zasu zo tunda taki sai kace ita a kasar aka haifeta

Mohd da Zainab ne manne a waya Yana fada mata irin kewarta da yayi tace dazu fah mun hadu, dariya yayi tare da fadin bana gajiya da ganinki Zainab, tabbas ada idan akace zanso wata mace bayan Afrah zan karyata Hakan, har gani nake idan ban samu Afrah ba bazan iya rayuwa ba, tabbas nasan Allah ya jarabamu ne mu duka nida ita munsha cewa idan bamu samu junanmu ba babu amfanin rayuwarmu sai gashi ta auri wani kuma tana rayuwa cikin Jin dadi nima gashi Allah ya bani ke, tabbas Allah ya jarabtamu ne yaga ya zamuyi sai gashi nida ita duk bamu mutum ba, sai yasa Koda yaushe bawa ake son ya dinga fadin cewa Allah ya zaba masa abu mafi alkhairi Zainab inda zaki yarda dani da sai ince miki sonda nake miki a yanzu yafi wanda nayi ma Afrah ina matukar kaunarki jini da tsoka sonki yabi ko ina a cikin jinin jiki na, buri na shine Allah ya mallaka min ke, ba fariya ba ko alfahari ba zaianb indai na rasaki ban tunanin zan kuma soyayya sai dai in Allah ya kaddara Amma ban tunani

Ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin Mohd, da farko na fara soyayya dakai Dan in nuna ma Afrah cewa Ina kaunarka dole ta cireka cikin ranta ashe yaudaran kaina nake, na kamu da matsanancin sonka, ina son ka sani insha Allah kaine mijina a wannan duniyar tabbas idan Allah yasa mukayi aure sai na jera kwana 7 Ina azumi domin nuna farin ciki da godiya ga Allah daya mallaka mun kai a matsayina miji

Wani irin murmushi yayi tare da fadin Ina nayi alkawari tare zamu fara mu gama tare indai mukayi aure, dariya suka saki a tare, inda yace mata gobe in zata dawo daga skull zai kaita wajan mum dinshi tana ta damunshi wai tayi missing dinki

Dariya tayi tare da fadin wlh nima nayi kewar mum sosai haka dai sukayi sallama badan sun so ba, tana kashe wayar taga Afrah da As a bayanta suna dariya As yace wannan soyayya haka, an gaisheki, hannunta Afrah ta kama tace Zainab duk naji abunda kika fada ma Mohd tabbas kin tabbata yar uwa ta gari kuma irin yar uwar da kowa zaiyi fatan samu, saboda ki hada ni da mijina kika fara soyayya da Mohd, bani da bakin da zan miki godiya Allah ya biyaki, tabbas naso Mohd ban taba tunanin zanzo As ba sai gashi Allah ya sauya komai cikin kankanin lokaci babu komai cikin Raina sai kaunar miji na, AS yace na gode Zainab Allah ya kara muku son junanku ke dashi

Cikin Jin kunya ta amsa da Ameen Afrah tace lah babu ko kunya da gudu tabar musu wajan duka suka bita da dariya

Zainab na zuwa gidan su Mohd tana Kara ma mum dinshi karatu duk da tana zuwa islamiya da Kuma malami dake zuwa gidan yana koyar dasu harda Mohd din kuma alhmdlh suna saurin dauka sosai, mahaifiyar Mohd tana kara son Zainab sosai itama Afrah tana zuwa wani lokacin Amma ba sosai ba saboda tayi nauyi tadai kammala exam dinta Kuma ta fita da first class haka kawarta Nadia itama wanda suka kara shakuwa

Afrah tunda taga cikinta nata Kara girma kullum Bata da aiki sai rubutu a cikin wani littafi idan As ya tambayeta na miye sai tace tana rubuta duk wahalan da cikin yake bata ne inta haiyu Yaron ya girma ta bashi labari, As yayi dariya yace aiki ya ganki Afrah wani zubin yaita tuna mata wasu abubuwan da tayi yace ta rubuta haka za suyi tayin drama gwanin sha'awa

Khadi da Sady ne zaune gaban wani malami inda khadi take bayyana mishi irin sonda take ma As nan malamin ya dakatar da ita inda ya fara buga kasa saiga hotan As ya bayyana ai cikin razana tace shine Malam

Bokan yayi dariya tare da fadin kin sameshi kin gama, zansa ya aureki kota wani hali Amma dai Zaki kashe kudi sosai tace babu damuwa nan tace ya fadi duk abunda yake bukata nan ya fada tace gobe zata kawo sauran bayan ta bashi kudin jakarta inda suka tashi suka fita khadi na tuki tana fadin ai harya aureni ya gama tunda wannan malamin yace Sady tace sai kace fadar Allah

Khadi ta tamke fuska tace komai zaki fada baki ga har hotanshi ya nuna mana ba, aike daga ganin wannan ma kin san aure dani da As an gama an wuce wajan babu Kuma mai hanawa wlh kuma sai..... Ai bata kai ga karasa magana ba sukaci karo da wata trailer inda motarsu taita kundun bala taita juyi lokaci daya kuma ta kama da wuta innallilahi wa inna ilaihira jiun abunda mutane keta fada kenan, aiko da aka kashe motar gawarsu aka gani duk sun kone bama a gane ko su wanene su, tabbas rai bakon duniya a lokacin da khadi take hango ta auri as kuma take ikirarin babu wanda ya isa ya hanata aurenshi sai gashi Allah mai cikakken iko ya nuna mata iyawarta tabbas sai yasa ake cewa komai mutum zaiyi yace insha Allah, sannan Sady Kuma an mutu bata nemi iyayenta ba koda yake shi Allah gafurul Raheem ne mai yafiya ne akan bayinsa, sannan ba'a shiga tsakaninsa da bayinsa Allah kasa muyi kyakyawan karshe duniya ba komai bane wlh muji tsoran Allah a lokacin da kake kokarin Killa sheri ko wani makirci Allah ya dauki rayuwarka mai zaka fada mishi?? Shifa duniya kyale kyalen banza ne komai ka samu a duniya mai karewa ne, karka bari rudin duniya ya dibeka ka dinga ganin kaman zaka dauwama a cikinta, idan kana tunani da nazari ya kamata ka dinga tambayar kanka ina wance yake ya rasu tun kana Jin labarin mutuwar wasu kaima nan gaba naka za'a Bada, wlh duniya ba tabbas kullum kara girma muke kamata yayi ace muyi ta istigifari muna Neman gafarar Allah




Yau a kasar America an tashi cikin wani irin iska mai kama da za'ayi ruwan sama, gashi garin hadari ya hadu Amma saiya washe sai kuma ya kara haduwa ya washe, tun daga safiyar wannan rana Afrah take jinta wani iri ga murdawan ciki, As ya lura da ita Dan haka yaki fita Amma basu bari Zainab ta gane ba Dan sun fara exam kuma yau zasu gama jarabawar, da zata tafi skul har tana tsokanan Afrah tana ce mata na kosa ki haiyu ki bani baby din ya taso a hannu na nida mohd

Afrah tace kin zama mara kunya ki dawo da wuri dai Dan yau su mum da mama za su zo harda abba da hajiya fatima, Zainab tace toh wannan zuga haka Allah ya kawo su lafiya dole in dawo da wuri, Zainab tana tafiya As ya kaita asibiti ana zuwa akace haiyuwa ne, nan akai labour room da ita har su mum suka sauka a kasar suka zo asibtin Afrah bata haiyu ba, kowa hankalinsa yayi matukar tashi sosai, Afrah Kam tana can tayi matukar jigata ganin jikinta yayi laushi yasa akace C's za'ayi mata domin bazata iya haiyuwa da kanta ba haka As yasa hannu kafin ayi mata suka lekata ta glass din dakin da take suka ganta duk ta had'a zufa ta rame lokaci daya Amma duk da haka ganinsu yasa ta sakar musu murmushi kowa jikinsa a sanyaye Amma ganin tayi murmushin yasa suka Dan samu kwarin giwa, nan aka fara mata C's wanda aka dauki wajan awa biyu da wani abu har Zainab ta dawo itama inda a lokacin Dr ya fito yake fada musu an samu nasaran cire yara mace dana miji Yan biyu ita kuma mamansu Allah yayi mata rasuwa

As dariya ya saki tare da fadin Dr bana son wasa inda ya tura kanshi cikin dakin da Afrah take ganinta yayi a kwance idonta a lumshe ga yaran data haifa a gefen gadonta an kwantar dasu akan karamin gado, a hankali ya fara fadin Afrah ki tashi Kiga abunda kika haifa Amma ina shuru ko gezau batayi ba, nan ya fara jijjigata shima shuru iyayensa ne suka shigo kowa na hawaye wanda a dai dai lokacin yaran suka fara tsala kuka

As fadi yake Afrah ki tashi Kinga suna kuka, dad dinshi ne ya rikoshi tare da fadin As Afrah ta rasu ba zata tashi ba, Aida sauri ya fisge hannunsa daga hannun mahaifin nasa Yana fadi kaima ka yarda da karyan wannan Dr din kenan Dad, haka As yaita sambatu saida Dad dinshi ya mareshi sannan ya dawo cikin hayyacinsa tare da fashewa da kuka mai karfi kaman karamin yaro ita Kam Zainab ta kasa kuka idonta ya kafe yayi kanana saita kalli Afrah dake kwance ta kuma kalli yaran dake hannun mum da hajiya fatima sai kuma ta kuma kallon Afrah, ita gani take kaman mafarki take bata dada tsinkewa ba saida taga ana saka gawar Afrah a makara ana shirin sata mota nan ta kuma shiga rudani tare d fatan ta farka daga cikin wannan mummunan mafarkin da takeyi mara dadi,

A nan kasar America aka birneta inda mum tace ashe a nan kasarta yake sai yasa taki yarda ta dawo gida, Allah sarki Afrah Allah ya gafarta miki, yaran sunci suna Afrah da Abubakar sadiq inda As yace Hakan yake so, sai fah a sannan Zainab ta fashe da kuka inda ta dauki macen jaririyar ta rungume tana kuka Nadia ma taji mutuwar Aminiyarta haka itama Aysha tabbas rayuwa babu tabbas, As Kam babu abunda yake tunawa sai sanda Afrah take cewa ya rabata da wanda take so Insha Allah kaima saika rasa abunda kake so sai kaji yanda naji wani kuka ya kuma fashewa yana fadin Afrah mai yasa kika tafi Mai yasa kika barni kece buri na kece wacce nake kauna mai yasa kika shammace ni ban taba kawo mana rabuwa ba kuka yake kaman yaro karami........

Ranar da akai uku duka suka tarkata sukayi Nigeria harda Zainab danta gama exam sunyi hutu, gaba daya rayuwa suke cikin rashin Jin Dadi, As Kam Koda ya dawo kulle kanshi yake kullu a daki baya zuwa ko ina yaran kuma suna wajan Mum an daukar musu mai reno itama Zainab tana Abuja domin bata tunanin zata iya nesa da yaran yar uwar tata shi Kam As tasa yaran yake a gaba yaita hawaye mum in taga haka taita mishi nasiha

Haka dai rayuwa taci gaba musu cikin radadi da rashin Jin dadi, har hutun Zainab ya kare ta koma makaranta, inda a nan ne hajiya fatima ta kawo shawaran hada Zainab da As aure, wai dan ta rike yaran yar uwarta, duka iyayen bangare biyu sunyi na'am da batun domin suma tun bayan rasuwar Afrah suke ta tunanin hakan

Inda akace shifa Yaron da yake neman Zainab ya za'ayi dashi, akace sai aje har can America ayi mishi bayani zai fahimta

Haka dai aka yanke dama shi As ya gaya musu zai koma America da zama bazai iya da zaman nan ba, Shima bai San da maganan auren da ake son hadawa ba, haka suka shirya duka suka tafi, inda a ranan ne aka fadama As Amma yace shi Sam bai yarda ba Amma da aka mishi bayani babu mai kula mai da yara sama da Zainab sannan ita kanta Afrah inda tana raye zata so hakan badan yaso ba ya amince, itama aka sanar da ita ranar saida ta suma kusan sau uku domin bata taba zaton Hakan ba sai gashi kuma an kawo mata maganan,

Koda aka samu mum din Mohd aka mata bayani ta fahimta tace indai matarshi ce zai aureta in kuma ba matarshi bace babu yanda suka iya Koda labarin ya iske Mohd kasa furta komai yayi inda yake ta kukan zuci Koda ya tashi zai fita sai fadi yayi kasa inda cikin tashin hankali akai asibiti dashi

Koda labari ya iske su mum nan sukai asibiti As Kam gani yake inya auri Zainab hakkin Mohd zai kama shi tabbas bai masa adalci ba, inya rabashi da Zainab dakin Afrah ya shiga na cikin gidan inda yaga littafinta da tayi rubutu akan labarin cikinta dauka yayi yana hawaye inda ya bude ya fara karantawa yaga ta fara kamar haka wannan cikin ina gani kaman bazan tashi ba, tabbas Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi naso ace zan rayu da yara na da mijina abun kaunata, Amma Kash ina gani da wuya Hakan ta faru Ina wannan rubutun ne badan nasan zan mutu ba ko zan rayu ba, inna mutu shikenan inna rayu inna dauko zan karanta zanyi ma kaina dariya ince tsoron nakuda yasa ni rubuta hakan

Ya mijina idan na mutu Dan Allah ka cika mun buri na, na ganin kanwata abun kaunata mai son ganin farin ciki na ta auri mohd Dan Allah ka taimaka ka tsaya ruwa da iska ka tabbatar sunyi aure in kamun wannan ka gama mun komai

Sannan sai alfarma ta biyu inaso inna mutu in kuma na tashi shikenan idan na mutu inaso ka auri kawaye na su biyu Nadia da Aysha dan Allah nasan ba zaka so haka ba in kayi min haka ruyina zai kwanta cikin salama, ban fadi hakan ba dan bana sonka na fadi hakanne domin ance ka soma kanka abunda kaso ma Yan uwanka, Koda ina raye zanso ka aurensu Amma nasan ba lallai ka amince ba tunda yanzu bana duniya ka cika mun burina dan Allah sannan abunda na haifa in ya rayu kaba Nadia da Aysha su kulan mun dashi domin nasan zasu rikesu da amana Dan amincin mu ya wuce yanda kake tunani, Dan Allah mijina nasan a lokacin da kake karanta wannan takardan nawa kanayi kana kuka, Nima a lokacin da nake rubutawa ina rubutawa ina kuka Amma in ban mutu ba zan karanta maka nasan zakayi mun dariya sosai, in kuma na mutu shikenan Dan Allah ka cika mun buri na Dan Allah sannan inaso karka manta dani a rayuwarka kullum ka dinga mun addu'a sannan inka auri Aysha da Nadia yara na ba zasuyi maraici ba kaima haka plz my baby..........

Ai fashewa yayi da kuka bayan ya gama karantawa inda ya tashi ya figi mota ya nufi asibtin dasu mum dinshi sukaje wanda aka kwantar da mohd hannunsa dauke da takardan, Koda ya karasa yaga mahaifiyar Mohd da iyayensa a waje inda mahaifiyar Mohd keta kuka, nan yace ina Mohd dad dinshi yace yana cikin wani hali sai aman jini yake yi mum din Mohd ta tsugunna tana rokon As akan ya ceci rayuwar danta ya bari ya auri Zainab karya mutu

Jikin kowa yayi sanyi inda As ya dagota tare da fadin ta kwantar da hankalinta domin kuwa abunda ya kawo shi kenan akan maganan auren Mohd da Zainab, nan ya mika musu littafin hannunsa hajiya fatima ke karantawa duka cikin harshen turanci tayi rubutun kowa babu abunda yake sai kuka nan da nan akace a daura musu aure inda mahaifiyar David tace dad din As ya amsa auren Mohd nan ya amince suka tafi masallaci aka daura auren da amaryar da angon duk basu sani ba, bayan an daura mum da As suka nufi gida suka tawo da Zainab a mota mum take mata bayani zo kuga murna wajanta

Koda suka karasa asibitin kai tsaye dakin da yake ta nufa dan dama likita yace yana ta kiran sunanta aje a kawo ta, tana shiga ta ganshi bakinsa duk jini haka ma ya bata rigansa rungumeshi tayi tana kuka, inda tak fadin Dan Allah ka tashi karka tafi ka barni da aurenka a kaina ka tashi yanzu na zama matarka dan Allah karka mutu ka barni

Jin Karan oxygen dinshi tayi yana kara sosai Aida sauri likitan ya shigo aka fara Dubashi hannunsa na rike dana Zainab dr yace gaskiya kuna son juna tabbas daya kara wasu lokuta inda baki zoba ban tunanin zai tashi, alluran bacci aka mai inda Zainab take nan zaune dashi yayi baccin wajan awa uku ya farka kuma alhmdlh jiki da sauki koda ya tashi taga idonsa biyu da sauri ta rungumeshi tana kuka shima kukan yake tare da kara matseta tana fadin yau na zama matarka nan ta bashi labarin komai Alhmdlh kawai yake ta furtawa tare da yima Afrah addu'a

Kwananshi uku a asibiti aka sallameshi kuma zainab ce take kwana dashi, tun ana asibiti yake nuna mata tsantsar soyayya, mama tace ta zauna wajan mijinta Allah ya basu zaman lafiya sun kuma fara azumin da sukayi alkawari na sati daya idan sukayi aure

As Kam baisha wahala wajan Aysha da Nadia ba duba da wasihar kawarsu aminiyarsu kuma yar uwarsu ta bari yasa sukayi na'am aka daura aure rana daya Aysha uwar gida Nadia Amarya suna kula da Afrah karama da As karami sosai kuma sun hade Kansu sosai suna zaman lafiya As Kam Yana kokarin musu adalci kullum kuma yana ma Afrah addu'a

Mohd yaje wajan mahaifinsa a Najeriya inda ya mishi Koran kare kuma yayi alkawarin kashe dan nasa ta hanyar bakin sihiri, duk da an gargadeshi aikin akwai hatsari yace ayi nan aka tura ma Mohd bakin aljani ya kashe sa Amma da yake koda yaushe yana cikin ambaton Allah yasa bakin aljanin ya koma kan mahaifin nasa inda ya kashe shi hmm.mmmm rayuwa in zaka gina Ramin mugunta ginashi gajere watakil kaine zaka fada

Mahaifin Mohd dai an mutu kafiri daga duka alama baida rabo, Mohd yayi kukan rashin uban nasa Kun San ance iyaye iyaye ne duk yanda suke


Mahaifiyar Mohd ta samu wani babban malami ta aura inda suke zaune a America Zainab ta kammala karatunta inda take ta fama da laulayi ciki Amma kullu cikin tsoro take kar itama ta mutu Mohd kullum cikin karfafa mata giwa yake akan zata haiyu lafiya har cikin ya isa haiyuwa ta haifi yarta mace Mohd yace an samu Afrah As yaji dadin Hakan inda ya kashe ma yarinyar kudi an samu Afrah biyu a family

As bashi da abokin shawara sai Mohd haka shima Mohd din, har business dinsu sun hada yanzu komai tare sukeyi Nadia ta haifi namiji Aysha ce dai bata haiyu ba Hakan bai dameta ba tunda ga yaran Afrah haka suke rayuwa bama ka gane yaran waye a cikinsu

Zainab da Mohd kullum cikin nunama juna kauna suke haka rayuwa ta kasance musu cikin Jin dadi da walwala ....... Toh Nima dai bari ince Alhmdlh a nan na kawo karshen wannan littafi Mai suna gidan kashe ahu Ina fatan ya kayatar kuma ya ilimantar

Sai mun hadu a sabon novel dina mai suna ALAMAR MU  labari ne da zaizo da wani salo na daban Kar dai ku bari a baku labari

Continue Reading

You'll Also Like

40.8M 1.1M 42
When Arianna marries billionaire Zach Price to save her family, she doesn't expect to fall in love with a man who'd always consider her a second choi...