Dad din David yace I don't knw ki tambayi yarki gata ita da take kwance, bari kiji inyi warning dinki akan yarki game da....... Shigowar police dakin yasa dad din David yin shuru inda police din suke tambayar likita ko marasa lafiyan na raye??

Nan Dr ya amsa musu tare da bukatar suje office dinshi inda ya ce gaba daya kowa yabar dakin ba'a bukatar kowa a wajen. Sannan ya bada umarnin a canza masu daki a kaisu dakin mutum biyu.

Dad din David yace yana son tafiya da danshi, Dr yace yayi hakuri ya farka su gani, badan yaso ba ya amince, danshi a duniya yanzu jinshi yake kaman ana daba mishi wuka na ganin Afrah kusa da danshi kwata kwata baya kaunar yarinyar ko kadan musamman da yake ganin tana kokarin rabasu da dansu da suke masifar kauna, mai tsananin musu biyayya mai son addininshi, wanda gashi ta sanadin haduwa da ita yana neman kaurace musu, wanda suke ganin bazasu taba barin hakan ya faru ba indai suna numfashi a doran kasar nan.

Bayan sun fita su duka kowa da abunda yake tunani, dukansu babu wanda yayi tunanin cin wani abu, sai dai daga an kira sallah suje suyi, wajajen karfe biyar da wani abu suna nan zaune bakin kofar Inda su Afrah din suke suka ji karan faduwar abu dukansu da sauri suka fada dakin, Afrah ce ta farka garin ta juya shine ta fadi, ai tuni da sauri suka nufeta sai sai kafin kowa ya karasa AS ya nufeta tare da daukota cak ya mai da ita kan gadon sai dai wani abun mamaki idonta a rufe yake har yanzu

Iyayen David kam da suka shiga gefen dansu suka nufa suka tsaya suna kallonshi cikin so da kauna, tare da tausaya mishi irin halin daya shiga ciki

Maganan Afrah ne yayi taking attention din kowa dake wajan inda take fadin David plz don't leave me, I can't leave without you ina sonka kaine rayuwa na dan Allah karka tafi inaso mu mutu tare mu...... Ai lokaci daya ta bude idonta tana wani irin uban zufa tana kallon dakin dama mutanan dake cikinsa ai hango David tayi da sauri tazo zata tashi amma hjy fatima ta riketa shi kam AS tunda yaji abubuwan da take fadi duk wani jinin dake jikinsa ya tsaya cak, ya koma kaman wani gunki a waka wajan, bama shi kadai AS din ba harta iyayen Afrah din sun girgiza da jin wannan munanan kalaman nata, eh mana munanan kalamai mana domin sarai dagaske tasan addininta ya haramta namiji christian ya auri mace musulma.......

Fisge fisge Afrah take tana fadin let go of my hand, amma ina Hjy Fatima taki sakinta, ganin haka yasa ta saki wani uban ihu da sai da dakin ya amsa saboda irin karan ihun data saki, wanda hakan yasa Dr din shigowa da sauri domin Nurse tunda taga sun shiga ta kira Dr, aiko yana shigowa yaga suna ta riketa tana kokarin fusge hannunta, ganin Dr din yazo inda suke yasa suka saketa, aiko tana ganin haka ta ruga da gudu ta nufi inda ta hango David kwance ta kankameshi sosai a jikinta tana wani irin sauke Ajiyan zuciya tare da fadin plz wake up David I can't live without you, ina sonka wlh zan mutu in ban kasance dakai ba, rayuwa ta babu amfani indai bana tare dakai dan Allah ka tashi.......

Gaba day daga iyayen David har nata kowa kallonsu yake, shi kam uban gayya wato AS tun sanda ta nufi David gaba daya ganinshi ya dauke mishi daga idanunsa domin wani irin abu ne yazo mishi tun daga kwakwalwar kanshi zuwa yatsan kafarshi yana mishi wani irin zugi da radadi, ji yake kaman ana tsige mishi jijiyar dake manne a jikinsa saboda tsabaragen tashin hankali, da firgici tabbas inda za'a iya gwada jininshi a dai dai wannan lokaci toh tabbas yayi mugun hawa.......

Mahaifin David ne da yayi wurgi da Afrah yasa AS ya dawo cikin hayyacinsa

Bayan yayi wurgi da ita ya kalli inda take a kwance a kasa ya fara magana kaman haka, you will die, domin bazaki taba samun yaro naba, bazan taba bari dana ya rabeki ba, koda zaki mutu a gaba na, I hate you I hate to see your face, koda zanyi yawo babu kaya wlh zanyi akan in bari yaro na ya aureki

Afrah cikin kuka ta fara yun kirin tashi amma ta kasa saboda jiri takeji sosai, amma saboda irin son David da takeyi yasa bakinta yaki mutuwa inda take fadin dan Allah Dad you can punish me but karka rabani da David, David ya musulunta saboda muyi aure.......

What mum din David da Dad dinshi suka hada baki wajen tambaya

Afrah tace eh ya musulunta sunanshi Muhd dan Allah...... Ai shakar da mum din David ta mata ne yasa ta kasa karasa maganan da tayi niyan fada, tuni akayi kansu inda aka fara kokarin jan mum din David din inda akai nasaran kwatan Afrah din wacce idonta ya fiffito waje don wahala, inda Dr ya fara musu ihu akan duka su fita....... Maganan David yasa duka suka juya, inda Afrah duk da jikinta babu kwari yasa ta nufeshi tana fadin Muhd tell them za muyi aure ka fada musu......

David wani irin kallo yake mata na mamaki, wanda yake nuna Dad dinshi da hannu alaman yazo inda yake aida sauri ya karaso inda Dad din nashi yake fadin my son.....

Afrah kokarin taba David din take yasa ya furta heeey don't touch Me tare da kallon Dad din nashi yana tambaya wacece ita Dad who is she????

Afrah wani irin abu ne ya bugan mata kirji, lokaci daya kuma ta fara murmushi tare da fadin David plz kabar wasa wannan ba lokacin wasa bane, tell them we are in love za muyi aure, nice Afrah dinka nice zaka Aura......

Duka tana maganan ne cikin turanci

David ya kalli mahaifinshi tare da fadin Dad wannan anya ba mahaukaciya bace tare da saka hannu sa a kanshi alaman yana mishi ciwo, hadi da lumshe idonshi ya fara sosa kanshi......

Afrah matsawa tayi ta kamo Hannunshi ta fara magana kaman haka, David nice Afrah kalleni am your lover kace bazaka iya rayuwa ba tare dani ba, kalleni dakyau mai yake damunka ne david dan Allah David ka daina wasa.

Wani irin tureta yayi tare da fadin ke wacece bani da hankali ne da zan auri mace musulma ban sanki ba ban taba ganinki ba, inada mata classic one mai yasa zan soki? Mai yasa zanso mace musulma? Tell me?

Afrah cikin kuka ta fara fadin David karka mun haka ban taba son kowa ba kaman yanda nake sonka, dan Allah karka yi breaking hearts dina dan Allah, am your Afrah

Hannunshi ya kuma sawa a kanshi tare da fadin Dad plz let leave from
Hare bana son ganin wannan mahaukaciyar yarinyar, Tell her ina da wacce zaku bani in aura her name is chioma, ba Dad dinshi ba harta mum dinshi jin ya kira sunan chioma saida suka tsaya suna mishi kallon mamaki tare da tambayar maike damunshi chioma data dade da mutuwa????

Mum dinshi tace David ka manta chioma ta rasu?

What ya furta cikin mamaki tare da fadin mum you said Chioma ta mutu, no no ban yarda ba, munyi waya zanje wajanta ne yanzu ni ban masan mai ya kawo ni nan ba plz mum muje in ganta I don't like this kind of joke plz..... Shuru yayi lokaci daya yasa hannunsa a kansa, tare da lumshe ido Kaman dai dazu, wani irin jiri ne ya dibeshi ya fadi luuuuuu

Afrah cikin mamaki da rudani ta fara kokarin yin magana amma ta kasa saboda jikinta babu kwari lokaci daya jiri ya dibeta itama ta fadi a sume.........




Toh ku biyo ni domin jin shin maike faruwa ne da David? Sannan wani mataki iyayen Afrah zasu dauka musamman yanda mahaifiyar AS da dad dinshi ke wajen Uwa Uba ga AS tsaye shima a wajen... ....... Ya Afrah zata ji in taji cewa an daura mata Aure.........







Maryam Obam

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now