Aysha tace Insha Allahu tare da fita suna tafiya suna hira inda Afrah tace ma Aysha a nan zaki zauna harna dawo koya

Aysha tace a'a gaskiya hostel zan koma zaifi min sauki

Afrah tace ok, har suka karasa wajan motar David dake zaune Yana jiransu wanda ya kife kanshi akan sitiyarin motarshi, daga duka alamu tunani yakeyi

Afrah gaba daya tausayinshi ya kamata, bude bayan motar tayi inda ta ajiye kayyakinta, hakan yasa David dagowa daga duniyar daya shilla wato na tunani tare da juyawa Yana kallonta harta gama saka kayan sannan tama Aysha sallama yayinda shima yama Aysha sallama tayi musu fatan alkhairi sannan suka wuce

Tuki david yake Amma gaba daya zuciyarshi ta kasa nutsuwa wanda ya rasa dalili na farko ga abunda idonshi ya gane mishi yau akan Afrah, da kudin daya gani a hannunta wanda hakan yayi matukar daga mishi hankali duk da Yana kokarin ya tursasama zuciyarshi rashin yarda akan abunda ya gani, tare da son matsa ma zuciyarshi ta yarda da Afrah din Amma ya kasa inya tuna da kudin daya gani a hannunta, bai taba tunanin zaiyi kishi akan mace haka ba, bai taba tunanin zaiso mace haka ba, bai taba tunanin zai tsinci kanshi cikin wannan mummunan halin ba, yasan tabbas son Afrah ya mishi yawa wanda ya tabbatar bazai iya rayuwa ba tare da ita ba.......

Afrah da gaba daya a mugun tsorace take musamman ganin yanda ya tamke mata fuska tare da ganin yanda yake sharara gudu akan titi kaman zai tashi sama, ita kanta ta rasa mai yasa ya mata wani irin mugun kwarjini yau, wanda ta kasa mishi magana gaba daya nauyinshi takeji hadi da jin kunyarsa akan ganin daya mata, duk da tasan Bata aikata komai ba, Amma tasan dole ko waye a matsayinshi Ya zargeta da aikata wani mummunan abu, musamman kudin dake hannunta data tabbata ya gani, Ido ta lumshe tare da fadin oh my God wayyo Allah na kenan a hausance, a cikin ranta ta furta hakan.......

Uwa uba jikinta a matukar mace yake wanda ta rasa dalilin hakan, Ga wani faduwar gaba da gabanta yake mata sosai ta tabbata indai taji irin wannan yanayin sau da yawa wani abu yakan faru sai dai tana rokan Allah a cikin ranta yasa taga alkhairi ko kuma taji Alkhairi .......

Mahaifiyar David ce a tsaye akan Dad din David daya rike sanda mai ruwan zinare sai kaiwa da komowa yake a cikin tankasheshen falonshi wanda iya haduwa ya hadu duk wanda yaga wannan tsaruwan falon yasan na mugun kusa ne, Yana kaiwa da kawowa yana furta David you break my trust akan wata mace wacce ba addininka ba kake gudun mu

Mum din David tace take it easy please karka bari wannan abun ya saka cikin damuwa, muyi magana dashi zai barta I know it nasan my son bazai ki jin magananmu ba

Dad din David cikin fushi yace bazanyi magana dashi ba, and bari kiji in fada miki koya barta ko insa su duka a kashe mun su, domin bazan bari ya sa inji kunya ba ace yarona Yana soyayya da musulma chai God forbid, dole in dauki mataki tun da wuri, na tura ma yarinyar Aljanu but she is lucky sun barta sunyi tsafinsu na musulmai sun kora aljanun, but this time in Bata bar mun yaro ba kasheta zanyi har kahira domin bazan mata da sauki ba, I promise gwara in dauki mataki tun wuri tun kafin labari ya canza domin nasan musulmai akwai yaudara kaman yanda ta mishi tsafinsu ya fara sonta zata iya mishi ya koma addinsu and idan haka ya faru saina kashe duka danginta shima in kasheshi tunda baida kishin addininshi but I know my Son bazai taba barin addininmu ba tunda yasan shine gaskiya and ko love daya fara da ita jikina har yanzu yana bani wani abu ta mishi but I will do anything just to take my son back to me this is a father promise to his son........

Mum din David tace hakane nima inaji asiri suka mishi domin inba asiri ba taya zai juya mana baya, ya gujemu baya kiranmu yaki zuwa inda muke Inna kirashi kullum Yana bani excuse mara amfani, plz kayi komai domin yarona ya dawo gareni I will support you, but plz don't harm my son I beg you, I will support you in any way but I will not support you to harm him, and if you try it I will go against you......

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now