Afrah shuru tayi tana kallonshi, lokaci daya ta rungumeshi tana wani irin hawaye mai taba zuciya, tabbas ina son David sonda bazan iya rabuwa dashi ba, lallai so baiyi mun adalci ba daya bari na kamu dason wanda ban tunanin zan sameshi a rayuwa, kara matseshi tayi a jikinta tana kuka mai dan sauti

David yace Afrah plz stop it, kukanki Yana saka ni jin wani iri, plz ki bari zan baki lokaci kiyi tunani akai I will not....... Katseshi tayi da fadin David in kana sona do what ever da zai saka ka mallakeni, ina nufin komai koda kuwa zaka canza addini..........

Muryan mahaifin David sukaji Yana fadin what??

Kinyi karya yarona bazai taba canza addini ba, you evil, nufansu yayi inda ya finciko Afrah dake manne jikin David ya sakar mata Mari kyawawa har guda uku tare dayin jifa da ita ta fada kan wani karfe goshinta ya bugu jini ya fara zuba, wani irin jiri taji yana dibanta Amma hakan baisa tace zata kwanta ba sai kokarin tashi da tayi, hannunta nakan goshinta wanda duk ya baci da jini, dad din David nufanta ya kuma yi inda ya shako mata wuya Yana fadin saina kashe ki, Afrah gaba daya idonta ya fito waje dan azaba, David ne ya karaso da sauri inda ya fara ture Dad dinshi Yana fadin ya saki Afrah, domin idan wani abu ya sameta to tabbas shima zai kashe kanshi.......

Ai jin haka yasa Dad din David jefar da afrah tare da kallon david din cikin mamaki Yana fadin David just because of her kake fadin haka? Maita maka haka david you are not on your senses, ka samu tabuwa

David cikin zafin nama ya nufi afrah tare da kamota ya dagota inda ya sabata a hannunshi, dad dinshi Yana shirin rikeshi yace Dad don't you dare touch me, idan wani Abu ya Sami Afrah am sure zaka rasani har abada, is better ka barni in kaita a dubata

Dad din sakan baki yayi Yana kallonshi har David din ya wuce inda yakai Afrah emergency and accident nan aka ansheta aka fara dubata, Inda suka ga Aysha a wajan

Aysha cikin tashin hankali take tambayan David maiya samu Afrah??

Amma saboda Yana cikin tashin hankali yama kasa yi mata bayani, magana ma ya kasa balle yayi mata bayanin abunda ya faru

Aysha ganin haka yasa tai shuru tana ta kaiwa da komowa, haka dai har aka gama duba Afrah, inda aka kwantar da ita tana ta bacci domin an hada mata da alluran bacci, bayan dr din sun gama dubata, David ya bukaci a bashi ita domin ya tabbata indai tana nan Dad dinshi zai iya aikata komai, dakyar Dr din suka amince suka bashi ita, inda ya kamota yace Aysha ta Kira mai mota fita tayi ta Kira mai mota aka saka Afrah dake bacci a cikin motar

Kai tsaye wani hotel ya kaisu inda ya kama musu daki harna wata daya, Aysha tace David School fah? Aida can muka je

Yace Aysha plz kibar wanna maganan zaman Afrah a school bazai yuba, coz anything can happen inaso dai yanzu kije ki dibo muku kayanku na sawa, zan zauna da ita kafin ki dawo

Aysha tace ok inda ta fita tare da tunani iri iri a ranta, domin dai ita ta rasa mai David ke nufi, sannan ta rasa maiya faru da Afrah haka

Afrah kam baiwar Allah sai baccin wahala takeyi, Bata san a wace duniyar take ba, har Aysha ta dawo Afrah Bata farka ba, David kam gaba daya ya kasa samun nutsuwa, haka yaita kaiwa da komowa a cikin dakin, aysha gaba daya tausayi taji Yana Bata, domin tasan Yana son Afrah son so, sai dai duk da irin wannan son Bata tunanin zai sameta domin ba musulmi bane shi, sai dai ayi runs a rabu.....

Motsin da Afrah tayi yasa ta tashi da sauri Amma kafin taje har David ya rigata zuwa Yana fadin thanks Jehovah she wake up, sannu Afrah kaita daga mishi alaman yauwa, hannunta tasa a kanta dake faman mata ciwo kaman zai cire don azaba, jin bandeji a kan nata yasa lokaci daya abunda ya faru ya fara dawo mata, kuka ta saki mai ban tausayi tare da kallon David dake kallonta shima cikin tausayi da tsantsar so

Rungumota yayi a jikinshi Yana fadin Afrah am so sorry for what happen, plz forgive my Dad plz Afrah

Cikin kuka tace David plz ka barni am begging you, dama na sani ni dakai bazamu taba samun juna ba, gashi tun kafin aje ko ina na fara gani, I known it I known it hakan zai faru David, addini ya shiga tsakani ni dakai, plz...... Kuka yaci karfinta lokaci daya taci gaba da cewa mai yasa so yamin haka mai yasa so yamin shigar sauri, mai yasa why why, maina aikata haka...... Yes wannan shine hukunci na, tabbas Allah ya jarabceni da son wanda bazan sameshi ba, saboda ya hukuntani akan abunda nake aikatawa na cuci kaina da rayuwa na fara aikata alfasha just saboda ina ganin an Bata mun rayuwa gwara inci gaba....... David bakinshi yasa cikin nata ya fara kissing dinta wanda hakan yasa Afrah yin dif komai nata ya tsaya cak.......

Kissing dinta yake sosai, Aysha kam ganin haka yasa ta fita domin dai taga inta tsaya toh itace dajin kunya dan da duka alamu Bata tunanin sun san tana wajan kuma tana kallonsu

David saida yayi kissing din Afrah sosai, ya tabbatar ta dawo cikin hayyacinta kafin ya saketa, inda ta lumshe Ido tana sauke ajiyan zuciya,

Magana ya fara mata kaman haka Afrah karki kara tunanin bazaki sameni ba, afrah am yours ni nakine haka kema tawa ce, wlh Afrah bazan iya rayuwa ba tare dake ba

Rungumeshi tayi tana kuka tare da fadin David ina sonka, ina sonka, wlh David ina matukar sonka, dan Allah david karka bari a raba mu, da inada iko toh tabbas da zan cireka cikin raina Sai dai bazan iyaba, saboda ina matukar sonka, dan Allah David....... Shuru tayi tana kuka cikin tashin hankali tare da kokarin janye jikinta daga nashi Amma yaki bari domin kara matseta yayi sosai a jikinsa

A hankali ya fara magana shima tare da fadin Afrah bazan taba bari wani ya shiga tsakanina dake ba, koda kuwa mutuwa ne, domin ina tabbar miki indai yau na wayi gari bakya duniyar nan toh ina tabbatar miki Nima zan bar duniya.......

Shuru yayi kafin yaci gaba da fadan cewar ina son ki sani sannan kimin alkawari komai zai faru bazaki gujeni ba, coz nasan daga yanzu zamu fara facing challenge daga iyayena, inaso ki san komai za su aikata ban so ki gujeni plz Afrah

Tace David I promise komai zai faru bazan taba barinka ba....... Shuru tayi komai ta tuna kuma oho ta fara tureshi daga jikinta tare da fadin plz David ka tashi ka tafi am scare gabana yana Fadi inaji a jikina kaman wani abu zai sameni, plz go from here David

Sakinta yayi Yana kallonta cikin mamaki, gaba daya duk ta furgice kaman wacce taga abun tsoro

Cikin tashin hankali yake tambayarta maiya sameta Amma ina ta kasa bashi amsa, lokaci daya ta fara ihu tana Fadin leave from hare or I should kill you inda ta kamo mishi wuya ta shake shi.............










Maryam Obam

GIDAN KASHE AHUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora