Afrah ce zaune tana ta jera kayanta cikin akwati domin a gobe zata koma Skul, domin ci gaba da daukan lectures, bayan ta Gama jera kayan ta rufe akwatinta, tare da kwanciya akan katifan dakinsu, lokaci Daya ta rufe ido, ba komai take tunani ba sai David, Wanda hakan yasa take son ta koma Skul Dan dauriya kawai take tayi bala'in kewarshi, a yanzu ta yarda n ma kanta tana jin abubuwa sosai a game da David din, lallai inda David zai musulunta zatai farin ciki, tuna kalmanshi tayi inda yake cewa bazan Kara tabaki ba har sai na aureki...... Hawaye ne ya zubo mata tare da fadin you are a good Man David, Kai mutumin kirki ne, lallai kana Sona sosai, tabbas kana mutuwar Sona, Mai yasa kazo a Arne Mai yasa baka fito a tsatson musulunci ba? Why why, Allah ka tausaya min kasa wannan bawa ya musulunta...... Tuna farkon haduwansu ta farayi har inda ta zame ta karye inda ya nuna kulawanshi akanta da irin hidiman da yayi Mata, lallai David Namiji ne da babu kushe a tare dashi, sai dai matsalan kawai ba musulmi bane...... Zainab ce ta shigo d'akin inda taga Yar uwar Tata cikin wannan halin...... Taba Afrah tayi tare da fadin Sis lafiya Mai ya faru kike kuka???

Afrah bude ido tayi inda ta kalli zainab tare da kamo mata hannu biyu ta hade tana Fadin Zainab Ina cikin wani Hali, Zainab kin San so........ Shuru Kuma tayi tare da fadin barshi kawai bana jin dadin yanayin yau ne.

Zainab da idonta ke Kan Afrah tace Sis am your sister Karki manta damuwarki tawa ce, Kuma na tabbata akwai abunda yake damunki, in bakiyi sharing dinshi Dani ba, dawa Zaki sharing damuwarki?? Ni Yar uwarki ce nafi kowa sonki......

Afrah tace Zainab Karki damu nasan kina Sona, sai dai ki yarda Dani babu komai kaman yanda nace, tare da shafa na zainab din fuska

Zainab tace shikenan na yarda badan naso ba, dan dai kince nedai kawai

Afrah tayi dariya tare da fadin Kinga tashi muje ki rakani muje kasuwa wata Yar ajinmu ta turo kudi in sai mata kaya

Zainab tace toh Bari in Gama abinci ya kusa sai mu tafi

Afrah tace toh, inda Zainab taci gaba da fadin Kai sis wlh Ina sonki kin ban babbar kyauta na waya

Afrah tayi dariya tare da fadin ai dama nasan waya za'a baki kiji dadi, sai yasa na baki, saura Kuma wayar tasaki ki Fara wasa da karatu

Zainab tace a'a haba dai, ai bazan Bari waya tasa in Fara wasa da karatu ba insha Allah my sis Bari in Duba abinci tare da tashi tabar d'akin

Afrah ci gaba da tunaninta tayi inda take Dana sanin karya Sim dinta, lallai David zai nemeni tabbas zai nemeni, na tabbata Allah sarki David Nima Ina cike da kewarka sai dai Ina kokarin in cireka a raina da rayuwata saboda Ni dakai ba zamu taba Zama inuwa Daya ba har abada...... Kukanta taci gaba dayi inda lokaci Daya ta share hawayenta tare da fadin zanyi welcome back din Sim Dina domin inji muryan David Koda kuwa wannan ne jin muryanshi na karshe da zanji

Shiryawa ta farayi inda Zainab ta kammmala abinci itama tazo ta shirya suka fadama Mama zasu kasuwa sannan suka fita bayan Mama tace karsu Dade

Saida suka Fara zuwa Mtn office tayi welcome back, sannan suka shiga cikin kasuwa jallabiya ta siya da gyale kanana, sannan tasai ma Zainab atamfa Mai kyau tace kawarta ta Bata dubu Goma kudin mota da zata kasuwa ta mata siyayya, ta siyan ma Mama sannan suka dawo gida, Koda aka bama Mama fada tai tayi tare da fadin Damme zata kashe kudin bayan tasan zata koma Skul Kuma tasan suba kudi garesu ba, Wanda zasu Bata harya isheta ba

Nan Afrah ta Fara fadin Mama kiyi hakuri albarka nake nema sai yasa na siya.....

Mama tace Afrah albarka na Koda yaushe Yana tare daku, kullum cikin saka Muku nake, Allah yayi muku albarka ya baku mazaje na gari, da yaran da zasu faranta muku Kuma, duka suka amsa da Ameen

Mahaifinsu ne ya shigo gidan inda sukai Mai sannu da zuwa, sannan Mama take nuna Mai atamfar da Afrah ta siya musu, shima dai albarkan ya saka mata sannan ya daura da gobe Zaki koma Skul koh??

Tace eh Abba, yace toh Allah ya nuna Mana

Ta amsa da Ameen




Washe gari kaman yanda Afrah tace ta shirya da safe domin Bata son tayi yamma, Abba ya fito ya Bata dubu talatin tare da fadin tayi hakuri dasu, ido ta Dan bude tana tunanin Ina Abba ya samu kudi haka harya Bata 30k

Kaman yasan abunda take tunani yace Afrah nasan bama baki abunda kike bukata, Amma kiyi hakuri insha Allah komai zai Zama dai dai, Hjy Fatima ta bani dubu dari 200 jiya da daddare

Afrah tace Allah ya saka da alkhairi Abba

Ya amsa da Ameen tare da fadin Ina zainab maza kizo ki tafi Kar kiyi yamma

Tace toh Abba zainab tana daki..... Fitowan zainab dinne yasa tayi shuru inda take gaida mahaifin nasu

Ya amsa da lafiya tare da bama zainab dubu biyar yace kisai abunda kike bukata

Muryan Mama sukaji tana fadin toh fah yau su zainab anyi kudi

Duka dariya suka saka inda Zainab da Afrah suka fita domin ta raka Afrah garage

Saida motar su Afrah ta tashi sannan zainab ta dawo gida........






Afrah ta sauka a Skul Wanda Kuma a dai dai lokacin David ya tashi tare da Kiran sunanta Afrah.......

Lokacin Mum dinshi ce a wajan inda ta nufeshi da sauri tare da rukoshi tana fadin David David......

Idonshi ya daura Akan mum dinshi Yana mata kallon mamaki ya akayi tazo maiya sameshi? lokaci  Daya ya Fara tuna abunda ya faru....... Hannu yasa a Kai yana hawaye tare da furta Afrah I can't live without you, I so much love you, why are you switch off your phone Afrah why why.......

Mum dinshi gaba D'aya cak ta tsaya tana kallonshi cikin mamaki da kuma tsoro

Lokaci Daya ta Kira sunanshi da David cikin tsawa......

D'ago dakai yayi ya kalleta

Tace who is Afrah??

Ba tare da fargaba ba yace she is the girl that I love, Mum I love her so much and I can't live without her mum......

Muryan Dad dinshi sukaji Yana fadin what?? You can't live without her?? Ok so you can die...... David I have to kill you............. You love Muslim girl how dare you tare da nufan David din cikin fushi.........







Maryam Obam


GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now