Ni Yar asalin garin Kano ce haka mahaifinki Shima Dan garin Kano ne, mahaifinki family dinshi suna da rufin asiri sosai domin duk Yan Boko ne gaba da baya, sannan gidansu duk da irin karatun zamani da suke dashi suna girmama na gaba dasu, mahaifinki ya taso cikin gata da kulawa, shine da na uku wajan mahaifinsu Alh Dayyabu, hjy Fatima itace babba, sai Alh shamsu, sai mahaifinki, sai Yar autarsu zahra'u, Wanda suke daki daya da mahaifinki kenan, domin matan Alh Dayyabu biyu, dayan nada yara uku, Jamila, Adam, sai hadiza, Kuma duka sunyi Boko, Kuma Kan zuri'ar a hade yake, gaba D'aya sun taso cikin gata, Hjy Fatima kasancewar itace babba yasa suke Bata girma sosai, Kuma tana aikin gwamnati ne, bari in takaice Miki labarin nida mahaifinki mun hadu ne a wajan bikin wata kawata Wanda Shima abokin ango ne, inda a nan muka kulla soyayya, tun ban daukan abun da muhimmanci harna fara domin lokaci Daya soyayyarshi ta shiga raina bana wasa ba, haka Shima ta gefenshi, iyayena ba masu karfi bane talakawa ne, duk da wani zubin Ina tsoran alakarmu, Amma Yana nunamin in cire komai ai shike sona ba wasu ba, Kuma shine zai zauna Dani, inda yake nuna min arziki da talauci duk na Allah ne......

Iyayena mu biyu suka Haifa, nida yayana Mai suna Abubakar, mahaifimmu mutum ne Mai hakuri da sanin ya kamata, inda mahaifiyata keda fada Bata da hakuri Bata daukan raini ko kadan, gashi Bata juran wulakanci

Wata Rana mahaifinki yazo mun da maganan zai turo domin ayi bikin mu, danshi ya shirya Ranan nayi murna domin Nima dai Ina da burin Inga munyi aure Dan Ina sonshi sosai, sai dai tun daga Ranan ban Kara jinshi ba, har wajan sati biyu, wata Rana yazo inda yazo a cikin mota na sameshi muka zauna muna magana inda nake tambaya lafiya kwana biyu ban jishi ba??

Shuru yayi ya kasa magana inda na kalleshi Amma da yake dubu ne ban San irin Yana yin da yake ciki ba, na Kuma tambaya Shima shuru can ya jefo min tambaya tare da Fadin Hafsat wani irin so kike mun??

Kai na girgiza alaman ban gane ba, lokaci Daya Kuma nace Ina maka son Dani kaina ban San Ina maka Shiba, Saida ka dauke ma ganina na kwana biyu naji jiki sosai.....

Sheshekar kukanshi naji inda hankalina ya tashi na fara tambaya maiya faru cikin tashin hankali

Yace Hafsat family Dina sunki yarda da maganan aurenmu, Hafsat Ina cikin wani Hali, wlh Hafsat bana tunanin zan iya rayuwa ba tare dake ba, inda lokaci daya ya kamo hannuna ya Dora akan kirjinshi Yana fadin kinji yanda zuciyata yake bugawa, duk da a tsorace nake sai dai soyayya ya rufe mun ido inda cikin halin da muka shiga har shaidan yayi nasara a kammu....... Kukan Mama da Afrah da zainab ya cika dakin shi Kam Abba kukan zuci yake Mai cike da tarin Dana sani.....

Mama taci gaba da fadin shaidan yayi galaba a kammu mun aikata mummunan aiki, bayan na koma gida naita kuka Ina Dana sani, inda na daina fita, Koda mahaifinki yazo bana fita yayi Aiken duniya na daina fita, duk da zuciyata har yanzu cike take da sonshi, Amma na kasa manta abunda ya faru tsakanin mu, ga tarin kunya

Inda aketa Shirin turashi waje a gidansu domin yayi matser dinshi a can, domin ya matsa akan Yana son aurena, Ana cikin haka na fara ciwo da zazzabi sosai ga amai gashi abinci saina zaba, Nan hankalin mahaifiyata ya tashi, Inda muka nufi asibiti gwajin farko ya nuna inada ciki......... Innalillahi wa Inna ilaihira jiun Ranan Naga tashin hankali da baki zabai iya fadaba Ranan nayi Dana sanin zuwa na duniya, inda wannan abun yasa mahaifina ya fara ciwo saboda yace na dauko mishi abun kunya...... Inda Dan uwana yamin dukan kawo wuka akan in Fadi Wanda yamin ciki, ai jin wuya tayi yawa yasa na fad'a, Aiko mahaifiyata Ranan ta nufi gidan inda tayi musu tijara akan dansu yama yarta ciki, Koda aka kirashi Bai Musa ba yace eh nashi ne, Nan jikin kowa yayi sanyi Amma ran iyayensu ya baci sosai inda aka yanke a daura musu aure inta haiyu

Inda naita rainon cikin bana fita ko Ina har ya Isa haiyuwa sai dai Koda yaron yazo Bai zo da Rai ba, haka aka binneshi cikin dare gudun Kar mutane suyi ta magana, Dan muna zargin ba'a sani ba, Saida safe aka sanar da mahaifinku inda ya fadama danginshi Aiko sukace maganan aure Kam babu tunda Wanda ya hada ya rasu, Aiko Nan ya tujire yace Bai yarda ba, inda yace musu dama ya gwada sune yaga yanda za suyi abunda aka Haifa Bai mutu ba....... Gaba D'aya zuri'ar babu Wanda ya damu yaga yaron ko yarinyar inda komai nikeyi da kaina tare da taimakon wasu Dana samu, haka dai akayi aure muka tare cikin wani karamin gida

Kaf dangin mahaifinki babu Mai zuwa gidana, idan suna sha'ani naje wulakanci da Gori Kam inasha sosai, haka Kuma gobe bazai Hana inje ba, Koda na haifeki babu Wanda yazo balle su San kalanki, bayan na haifeki aka saka Miki Fatima muke ce Miki Afrah, na Kuma haiyuwar Yan biyu Amma duka Basu zo da raiba, kafin na haifi zainab.......

Dangin mahaifinki suna ganin kece na Haifa bada aure ba, Kuma bayan auren munyi musu bayani Amma sunki yarda, basa Sona da mahaifinku saboda mu ba masu karfi bane, iyayena sun rasu, inda Dan uwana Shima ya kullaceni yake ganin kaman nice Silan komai

Ana cikin haka Alh Dayyabu ya rasu inda aka raba musu gado, Amma hjy Fatima ta rike na Abbanku, domin mahaifiyarsu tace Kar a bashi sai Nan gaba, kafin ta rasu, yanzu gidan da muke zaune na hjy Fatima ne ta bamu, naso mahaifinku yakai koto domin a bashi hakkinshi Amma yace Kar in Kuma wannan maganan domin hjy Fatima uwace a gareshi domin itace babbar yarsu Kuma ance Babar ya uwa.......

Afrah wani irin ajiyan zuciya ta sauke inda take ta fadin Alhmdlh domin tunaninta ya Zama ba gaskiya ba, Ashe ta hanyar sunna aka sameta, lallai iyayenta sun ga rayuwa Amma babu komai ita tasan kaddara Kuma tasan itace ta fada kansu

Hannun mama Afrah ta kama inda take fadin Mama kiyi hakuri Ni nasan kaddara Kuma nayi Imani da ita, Kuma komai ya faru rubutacce ne daga Allah babu Wanda ya Isa ya canza kaddara, Kuma insha Allah zamu zame muku abun alfahari

Rungumeta Mama tayi tana kuka, Amma gaba D'aya kunyan yaranta takeji dauriya kawai takeyi

Haka Shima ta gefen Abba, toh Amma babu yanda za suyi sai hakuri

Afrah Ranan tace zata koma gida hakan ko akayi suka dawo gida.....

Inda gaba D'aya suka sake, domin sun lura iyayen nasu na cikin wani Hali, Amma suna kokarin kwantar musu da hankali, Koda suka tashi tafiya gidan hjy Fatima Afrah tace ba zata ba, Saida Mama ta nuna tayi fushi sannan ta yarda zata, inda Mama ta roketa akan tayi hakuri karta nuna fushi ko anyi mata wani abu, tace zatayi hakuri inda Mama taita mata godiya tare da saka mata albarka, taso ayi a gidansu tayi hidimar Daya kamata da kudinta duk da tana tsora a fara tambayanta a Ina ta samu kudin

Ranan da suka je gidan hjy Fatima tayi wata bakuwa, kana kallon matar kasan naira ya zauna, hjy Fatima Ranan Bata daure ba faram faram ta amshe su Wanda Afrah tasan ganin matar Nan yasa suka samu tarban arziki, inda tunda suka shigo idon matar yake Kan Afrah har sukai ciki inda ta kalli hjy Fatima tace Amma wannan zuri'arku ceko?? Dan Naga Kuna kama? Hjy Fatima tace eh duka yaran kanina ne da matarshi

Matar tace Amma inda Zaki yarda da....  Koda yake zakiji sako bazan yanke magana yanzu ba

Hjy Fatima Dariya tayi tare da fadin Aida kin fada..... Suna cikin haka aka Kira matar a waya inda ta dauka tace gani Nan fitowa, tare da tashi tana Fadin Kinga na tafi yaushe ne saukar?

Hjy Fatima tace gobe Amma jibi za muyi taro har waje ta Rakata, inda Afrah ta fito domin tana son waya da Aysha taji ya take Kuma Bata son Mama taji irin maganar da zasuyi

Wuce su hjy Fatima tayi inda ta fita waje, AS dake zaune cikin mota Yana Danna wayarshi kaman ance ya d'ago idonshi ya sauka akan fuskan Afrah gabanshi yaji ya Fadi tare da tunanin ya taba ganin Mai wannan fuskan a wani waje, ido ya lumshe Amma ya kasa tunawa lokaci Daya Kuma ya kawar da tunanin inda zuciyarshi take fadin baka santa ba kawai sha'awa ta baka, ka kwashi rabonka kayi gaba....... Jin bude motar yasa ya dawo daga duniyar tunanin Daya afka ganin mum dinshi ne yasa ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin mum na Dade Ina jiranki

Murmushi tayi inda tace kalli can..... Hannuta yabi da kallo inda yaga tana nuna inda Afrah take tana waya tana dariya...... Kallon mum din yayi yace maiya faru?

Mum tace Bata burgeka ba??

Yace noo tare da tada motar yabar wajan da gudu..........






Mutane ne a wajan Mortuary inda ake ajiye gawawwaki, a cikin asibitin shika, inda wata ke fadin wlh dazu naji ihu, kaman akwai Wanda Bai mutu ba ko Kuma wacce Bata mutu ba, Nan aka fara kokarin bude mortuary din domin a Duba a gani............








Maryam Obam

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now