42

747 62 38
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
*DAGA ALLAH NE!*
💖💖💖💖💖💖💖💖

*FATIN MOMMA*

PAGE4️⃣2️⃣

    

   Kamar wanda aka yi musu umarni da kallon dan kaka gaba dayansu suka zubo mishi na mujiya , cikin tsananin , shock , fargabar mai zai biyo hade da tsegumi suka hada baki kamar masu waka
"Huuuh!, 
Mai gado ka zaga?"
Suka karasa maganar cikin yanayi na zuzutawa da ku bilkisun bata ga damar daukar mataki ba zata dauka (hi fans kunsan dai yanda classmate suke a irin wannan tsegumin)

     Cikin rashin fahimta dan kaka ya kalli zahra wacca ta ke cikin yanayi na mamakin daman haka kake !?!,  kallonsa kawai take kamar taga kaho ya fito a kansa ne ,
Ganin kallon da yake yi mata ne na bai ma san mi yayi ba ya sanya zahra fadin
"Yeah baka ji zagi kayi ba ne?"

     Dan dariyar dan kaka yayi da bata wuce ta yake ba jin abinda ya fada pah ashe nan zagi ne!, saboda shikam ta wajen su normal ne don mutum yayi magana ya hada da "yar tselan uwa" ko "yar kusun uwa" musamman idan aka bata maka rai
    "Ah! Wai maganar dana fada kike nufin da zafi ?"

    "Uh!
Da kai baka sani ba?"

    "Nope kawai dai abun ya bata min rai ne , That bitch nasan ko gadon karfe bata dashi shine da wani katon_katon kumatunta a wajen a ake kiranta da mai gadon zinare huh!?!"
Ya karasa maganar da watsawa bilkisu harara wacca take shaka ta cika tayi fam! Da bacin rai saura kiris! Ta fashe , Abunka da yar lukuta

     Sannan ya maida kallon sa kan Zahra , wacce ke tunanin Ah! Lalle wannan he's another idiot
   "Hi zahra nasan yanda take yar lukutar nan tana hawa gadon zinaren zai karye, , , ina laifin ma a ace bilkisu mai gadon karfe , ko gadon katako ehn!?!"

   A fusace bilkisu ta buga desk din dake gabanta hade da fadin
   "Bayan ka zage ni har saida kayi magana akan ballons dina (kumatu) sannan koma kace ni yar lukuta ce,  hakan duk bai isheka ba saida ka bata min suna ehn!?!,
You little thing you're absolutely a dead cake"

    A fusace anty jidda ta katse su da fadin
   "Cut the craps you silly little thing"
Cos duk wannan maganar da suka baifi cikin seconds ba

     Murza ido bilkisu ta fara a shagwabe  mai hade da rigima cikin yanayi na son yin kuka ga babban takaicinta da ba'a barta ba tabi hakkinta cos tasan sau daya tak! idan ta zauna akan wannan yaron yaji nauyinta gobe ko kudi aka bashi bazai sake tsokanarta ba
   "Anty shine pah da tsokana"

   
    "Uh_oh! Sorry my kid,  barni nida shi ne, New comer,  tell her sorry!"
Ta karasa maganar a fusace tana kallon na kaka da yayi tsilli_tsilli da idonsa a wajen kamar aj jijjiga bera a buta
Cos ya tsorata da tsawar anty jidda

    Kamar zaiyi kuka yace
    "Sorry"

     "Hi you little boy is it how to say sorry?
Oya Say it again, bilkisu am sorry"

Kamar mai waka haka na kaka ya maimata da fadin
    "Bilkisu am sorry"

  
     "Is okay,sit down"

    Sannan ta cigaba da kiran suna daga inda ta tsaya
"Fatima ilyas , faty?"

   "Yes maman(ma'am)

    "Fatima El_hassan muhammad?"

Kallon zuhra amina tayi ganin ko irin gizau din nan na alamar taji sunanta ba ta yi ba , bawai don bata ji sunan nata bane Ah! Ita bada wannan sunan ta saba ba
    "Zuhra ke pah ake kira"

  Harara zuhra ta watsa mata tana mai cigaba da harkokin gabanta
       "You little thing menene hadin zuhra da fatima huh!?"

  
   "Zuhra hassan muhammadu?"

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now