#The7sillypupils 43

124 4 5
                                    

💖💖💖💖💖💖💖
*DAGA ALLAH NE!*
💖💖💖💖💖💖💖

*FATIMA ABDULLAHI IBRAHIM*
_(fatin mama, ZOIS)_


Assalama Alaikum ,
Hello fansmily ina mai kara baku hakuri bisa dadewata akan cigaba da wannan littafi, Hakika in bacin kaunarku ga wannan littafi bana tunanin zan karasa shi nan kusa , masu kira a waya da messges da masu mun magana in person duk ina godiya , Ina barar Addu'ar ku akan Allah ya bani ikon kammala wannan littafi...Ameen
💝☺️

Ina kike ne *Aisha Wada Dutse (nana)* wannan page din naki ne kiyi yanda kike so dashi , Hakika kina daga cikin jigon abinda yasa na cigaba da rubuta wannan novel din , Allah yabar zumunci...Ameen Ameen
😊☺️💖💝😍😻

#the7️⃣sillypupils
#the4️⃣idiots

Page4️⃣3️⃣

"...Ze farin ice(the principal)
Bai farin ice(vice principal)
Senior manda(senior master)
Tabo manda(labour master)
Gudu de to you all (good day to you)..."

Yanda na kaka ya dage da dukkan karfinsa yana magana da sunan debate shine abinda ya kashe zahra da burgewa , cike da mamaki na ya burgeta ta kalli sauran mutanan nata tana mai fadin
"Whoa! Na kaka fa ya iya debates ehn!"

Shima cikin nasa yanayin ka burgeni na kaka yusuf yace
"Am telling you sheena"

Yayinda mai girma na kaka ya cigaba da ratattabu bayani akan muhawararsa
"I am share to capport ze motor which ce zat...
(I am here to support the motion which say that...)

Dan shiru yayi cos daman burgar iya nan ce , sannan ya juyo da barin kallon malaman ya kalli su zahra dake bayansa yana mai fadin
"Me ma zance a gaba?"
Shi bai yarda ba sirri yake cos harda wani kara hannunsa a baki not knowing maganar ma a loudspeaker yake

Shiru gaba dayansu suka yi suna tunani , kowa da abinda yake tunani
"Um!..."

Kamar wacca aka fauce maganar daga bakinta zahra tace
" Debate about eating food in the classroom or dining hall , support the motion"

A dan tsorace na kaka ya sake kallonta kamar yanzu ne ya fara kallonta yana mai fadin
"Me zan ce kenan?"
(Fans kada ku manta pah rana ake har yanzu Ah!)

Matsowa kusa dashi zahra tayi cikin rada itama a zuwan sirri ne tsakanin su alhalin ta tsiyaye shi a loudspeaker tana mai fadin
"I am here to support the motion which say that eating food in the classroom is far better than eating in the dining hall for the following reasons..."

"Ban iya turanci ba"
#na kaka kamar zaiyi kuka

"Saika yi da Hausa then!"
#yusuf ya fada cikin izgili na mai na kaka yake dashi ne da Zahra ke yawan kula shi ne ehn!

Kafin wani a cikin su ya sake wata magana na kaka ya juya ga malaman yana mai fara debate din da hausa cikin amon sautin murya da full confidence daya fi na farko
"...Alkalin mushawara(alkalin muhalin)
Mai gilma mai duba cokali(mai girma mai duba lokaci)
Mai gilma mai kicil_kicil da kararrawa(mai girma mai kada kararrawa),
Malamai masu duka da masu saka punishment,
Abokan muhawara wanda nake so da wanda bana so tare da sauran yan uwana dalibai Assalama Alaikum?"

Tsabar shock din abinda na kaka yayi gaba daya an kasa karbar loudspeaker a hannunshi sai kallo kawai da ake binsa dashi cike da tsabar mamaki
"Wa'alaikum salam!"

"Kamar yanda kuka sani suna na Na kaka Alhaji maigari Daga karamin aji biyu na yara Ba(Nursery 2B) ,
Na fito ne domin na kare ra'ayi na; na koma dagargaji bakin masokana akan wani batu mai taken 'cin abinci a aji yafi cin abinci a dakin cin abinci saboda dalilai na kamar haka'..."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 21, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now