DAGA ALLAH NE! 27

834 47 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
*DAGA ALLAH NE!*
💖💖💖💖💖💖💖💖


*FATIMA ZOIS*
Wattpad @
*Fatima Zois*


Dedicated to *MY DEAREST PARENT*


page2⃣7⃣


Saida suka tabbatar da umma ta shiga part din abba sannan suka tura hannatu,
Yayinda kowannensu ke Sake gyara tsayuwa a position din sa domin tabbatar da kyakkyawan  tsaro,
Sai koma kunnensu da suke so su bashi kyakkywan abincin da basu taba bashi ba
cos they can't wait

Cikin sanda da taka tsan_tsan hannatu ta karasa falo inda su zahra ke zaune suna wasa,
Ba bata lokaci ta durfafi inda yaran suke cos itakam! Bata yi zaton zahran tana cikin su ba Duk da dazo taji komai game da abinda umma take sanar dasu baabaA akan zahran amma bata dauke shi serious haka ba,
Indeed ita harta manta ma

Kai tsaye take neman wucewa cikin uwar daki inda tasan zahra tana kwance as usual tana sana'arta wato bacci,

Wani Abu taji ta taka mai santsi da laushi ga koma sanyi duk da haka bata damu ba cos ita burinta kawai shine ta isa ga zahra domin aiwatar da abinda tasan ya kamace ta,

Taku daya zuwa biyu still ta sake ji ta taka abun,
A fusace ta juyo domin ganin ko miye hakan har yake shirin kawo mata katsalandan! A cikin aikin ta Wanda hakan ya sanya ta sunbulewa harta fadi,

Daga hannu tayi zata wanke zuhra da gigitaccan Marin da  yake hukunci akan faduwar data yi
cos ita ta gani a wajen ba tare data San zahra bace
  kawai idonta ya sauka a kan zahra,

Kallo_kallo ne ya wanzu tsakanin zahra da hannatu
Ido cikin ido kowa suke yiwa  juna,
Ita kam hannatu gaba daya ta kasa tabuka komai ganin idon zahra a kanta
Sai taji duk ta rasa dan kuzarin data Dade tana tanadinsa ga irin wannan lokaci data ke jira,
Musamman
Da take ganin wani irin  kwalli da idon zahran ke yi har wani sparkling hannatu taga yana yi,

gaba daya sai taji zahran tayi mata wani irin mugun kwarjini fiye da randa suka fara ganinta,
Ai tuni ta manta da zancen mari saima hannunta daya Kame a sama yayinda take saurin dauke idonta Daga cikin na zahra tana mai cigaba da kallon Abubuwan dake wajen,

Ita kowa zahra mah ta daina wasan data ke yi take ta maida hankalinta kan hannatu wacca har yanzu bata tashi ba,
Cikin wani irin kallo
Irin kallon da yaro ke yiwa bakuwar fuska
ko kallon rashin yarda

A hankali hannatu idonta ya fara zagaye a cikin tarkacen kayan wasan da take tsumu_tsumu a ciki,
Abinda idonta ya gane mata shine ya Sanya  numfashinta daukewa na wucin Wanda aka fi sani da suman zaune

Ashe wacca take nema gata ma gata nan a gabanta!,
Cike da al'ajabi cos abun yafi karfin mamaki tabi zahra da kallo
Sai yanzu ma ita ta lura da yanayin zahran ai,
ganin zahran tayi zaune Daram! Babu wata alama da zai nuna wai yanxu ta fara zama...,
Du_du yaushe suka zo ganin zahran suka ganta nannade a cikin bargo kamar wata jaririya sabuwar haihuwa wai amma yanxu ta ganta a zaune haka!....
What! An Amazing

Idanuwanta ne ya cigaba da rolling akan abubuwanta da take gani a wajen,
Abinda ta sake gani shi yafi bata
mamaki da tsoro fiye da  Wanda ta fara gani,
  wani irin mugun bakin miciji Wanda bata taba ganin irinsa ba a fadin rayuwar ta gani rike a hannun zahra da alama shine abun wasan nata,
Koma Da dukkan alama shine abinda ta taka harta fadi rike

Yayinda su koma ameena zuhra da Muhammad kowanne ke wasansa da kayan toys dake gabansu
Lokaci_lokaci koma su juya kan micijin zahra suma Sudan yi wasansu dashi

Saida ta dauki seconds about 1minutes Wanda da alama sai a lokacin hankalinta ya dawo kanta sannan ta takarkare ta kurma wani uban ihu mai firgitarwa ba bata lokaci koma Ta tashi Daga cikin kayan wasan yaran tana mai cika bantenta da iska!.

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now