DAGA ALLAH NE! 30

988 56 2
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
*DAGA ALLAH NE!*
💖💖💖💖💖💖💖💖

*FATIMA ZOIS*
Wattpad @ *FATIMA ZOIS*

Dedicated to *MY DEAREST PARENT*

PAGE3⃣0⃣

"Ina yini mama...?"
@zahra

Saurin rufe mata baki Muhammad yayi kamar Wanda ta fadi abinda ba sai_sai ba
"Ke anty zahra mamanki ce
Ba tace ita maman magajin baba bace kadai...."

Cike da tsiwa hade da fusata zahra ta cire hannun magajin baba daga bakinta
"Ba umma tace duk da haka itama mamanmu bace,
Eh din! An fada din
Ina yini mama"

A fusace shima Muhammad yace
"Babu abinda zaisa ince wani Mama,
Maman magajin baba ina yini?"

"Shiyasa Sam! Bana son in dinga hada harka da anty zahra da yaya Muhammad cos duk inda suka je sai sun nuna halinsu kamar wasu yara,
Ina yini mama"
@zuhra ta fada cike da takaici da kosawa kamar wata babba alhalin ko maganarta ma bata gama daidaituwa ba

"Uhm!
Ina yini mama?"
@amina ta fada cikin sanyinta

Duk pah wannan Maganar da suke suna daga bakin kopa ko shigowa basu yi suna dai cire sandals nasu ne

Tun daga bakin kopa kowa
Zahra jummai ta fara gani a gaba hannunta rike da wata katuwar Leda wacca daman ta sani wannan ko ba'a fada ba magajin baba aka kawowa cos Indai umma ce duk bayan kwana biyu haka take wannan hidima,
Banda abinci kullum

Duk kyau irin na zahra lokacin tana jaririya saita ga Ashe zahra ba komai bace akan yanxu,
Duk da cewar Uniform ne na makaranta a jikinta Ga hijab Wanda ya mamaye Gaba daya fuskarta in banda hanci da bakinta sai ido babu abinda mutum zai gani,
Koma daman wannan itace shigar zahra cos duk Wanda ya kalli zahra saiya kara kallo sannan ya  saiya tofa albarkacin bakinsa a kanta
Wani lokacin mah har tsayawa kallonta ake
shiyasa ma ake mata wannan shigar

Still wannan kwarjin NATA yana nan Fiye ma da yanda jummai tasanta dashi
Indeed saima karuwa da yayi,
Kyallen idonta kowa tun daga chan bakin kopa take ganin idanun zahran nayi;

"Wannan ido!,Wannan ido!!, Wannan ido!!! Ko!...Koda ban samu damar Hallaka ki bari saina tsire wannan hegen idon ko zan huta ma da shakkarki..."
@jummai take rayawa a zuciyarta

"Ina yini mama?"

"Ina yini mama?"

"Ina...yini...maman...magaji...baba?"

"Ina yini mama?"

"Anty ai ba koda zasu kwana suna gaidaki baki amsa ba
ba zasu daina ba Indai wannan yaran ne"
@umma wacca taga tun dazo sai gaidata suke amma ita tayi Biris! Dasu da alama tunani take

"Hehehe!
Ahe! Lafiya kalau yara ya kuke ya makaranta?"
@jummai ta fada Cike da yake Wanda yasa yellowish din caka_caka hakoranta a wajen suka fito kamar Dorawa

"Ai tunda suka yi miki wannan shikenan koma anty,
Ina yini anty ya mai jiki?"
@umma ta fada cike da fara'a cos bata yi expecting jummai zata Amshi yaran hannu biyu haka ba

Wata dariyar yake jummai ta sake saki kamar bai shirin yin kuka sannan tace
"Ahe!?,
Lafiya kalau
Jiki da sauki."

Ta karasa
Yayinda ta saki baki da hanci tana kallon yaran gwanin sha'awa yanda suke mu'amalarsu,
Ina magajin baba ne haka?
Harma ta manta da Wani gaisawa suke da umma

"Anty zahra ki kawo mana in tayaki rike ledar cos
Nasan kin gaji koh?"
@muhammad ganin zahra sai fama take da ledar hannunta amma don naci taki ta aje

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now