DAGA ALLAH NE! 08

752 51 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖




💞💞💞
*DAGA ALLAH NE*
💞💞💞




*FATIMA ZOIS*




Dedicated to
*MY DEAREST PARENTS*



*HAPPY birthday MY ONE & only* *BABA YAMEEN*😍❤


*Hussy* '''wannan page din naki ne da sauran masoyan wannan novel din ina kara bada hakuri jina shiru na tsawon lokaci'''😍😻
_Da fatan kunyi sallah lpia, Allah ya maimaita ta badin_badada_😍🤲🏻👏🏻



Page8⃣



"Subahanallahi! Jummai mi kike shirin yi haka?" @baba ishaq ya fada a kidime

Cikin rashin damuwa jummai tace"Alhaji naga bihiyar tafy motor gudu ne hiyasa naga gwanda in haye bihiyar ta kaini Ku sai Ku biyo ni a baya." ta fada cikin hausarta ta Fulani yayinda take shirin hawa bishiyar

"Ya salam! Jummai wayye yace miki bishiya tana tafiya Huh!?,ko kingani a garinku bishiyar na tafiya?." @anty maryam cikin nata rudanin cos ita a ganinta jummai ba iya ita kada bace

"Hajiya daman ance komai na binni daban ne hiyasa naga bihiyar mah taku ta binni itama daban ce tunda gahi har sharara irin wannan gudun take." @jummai bata hakura ba, kokarin dai hawa bishiyar take duk cewar ta kasa

"Nan pah wani sabon bata lokacin ya tashi cos jummai ta dage cewar bishiyar ce zata kaita saboda taga yanda bishiyar take wucewa ta cikin motor tamkar walkiya,bata taba kawowa a ranta cewar su suke wuceta ba."

"Da kyar da sidin goshi baba ishaq da anty maryam suka samu damar sanya jummai cikin motor ba don taso ba musamman yanxu da aka kara gudun motor gani take kamar bishiyoyin da gayya suke wannan mugun gudun na rashin hawa su kaita da tayi."

"Haka dai rai a bace jummai tayi wannan tafiyar har Allah ya kawo su gida lpia."

"Tunda jummai take a rayuwarta koda a irin films din da take gani a wayar jauro saurayinta bata taba ganin tsararran gida irin wannan bah,musamman da taga harda step a gidan dadin dadawa taga tunda suka tsaya koh kare babu Wanda yaxo tarbarsu."

"Kardai pah ace gidan yakan kai suka kawota da gaske!? Daman koma ansha fada mata dan binni zai iya yin koma akan kudi ciki kowah harda yakan kai!,sannan jauro ya fada mata irin wannan gidan da take gani a kallo ko a binni ba kowa keda hiba hede na masu yankan kai bare wannan da yafi irin Wanda take kallo a films din." Abinda kawai zuciyarta ta raya mata kenan

Tuni jikinta ya fara karkarwa kamar mazari bata kara tabbatar da abinda take zargi ba saida ta wurga idonta gabas da yamma,kudu da arewa,sama da kasa bata ga alamar dan Adam ba,ai da kyar ta samu damar harhada kalmomin bakinta

"Wayyoh!!! Na higa uku na lalace wayyo innata wayyo baffana,Don Allah kada Ku yanka ni na yarda bama he kun maida ni kyauye ba nida kaina xan koma aradu! Zan koma amma kada Ku yankani."Ta karasa maganar yayin da take kwarara wani irin ihu na tashin hankali tamkar wacca ake yanka ta din gashi baba ishaq da anty maryam sai kwantar mata da hankali suke amma ina ita taki yarda

"A ganinta wannan yar muryar da suke mata ta yaudara ce don su samo damar cimma bukatarsu,daman gashi ansha fada cewar tana da katon kai hakan na nufin wannan katon kan NATA xaiyi kudi sosai kenan!?."

Ai yin wannan tunanin da jummai tayi shi ya kara zuburar da ita wajen bada himma a ihun da take yi kwararawa ko Allah xaisa koda makwabta ne su fito

Jin wannan ihun NATA ne yasa gaba daya mutanen gidan fitowa Wanda basu San mah da dawowarsu ba

"Anty maryam Oyoyoyo!!!." Abinda kawai kake ji daga bakin bataliyar yaran da suka durfafo wajen,

"Sunji dadin dawowarta a badini sosai atleast mai supporting nasu a koda yaushe ta dawo ga koma kyauta da take musu a koda yaushe,"

" idan zasu shiga part dinta sau ba adadi su koma fito ba adadi sai tayi musu kyauta amma pah anty maryam bata daukar raini koma masifaffiya ce ta farko mah amma idan ka shiga harkarta kenan."(
_fans kunsan dai halin masu irin wannan sunan_)

" Yayinda koma a zahiri kowanne ke kokarin xuwa ya karba jakar anty maryam cos abinda ake wah oyoyon yana ciki."

"Turus! Gaba dayansu suka yi Sakamakon arba da katuwar budurwa ta tale baki sai kwarara ihu take."

Kallo_kallo ne ya fara wanxuwa a tsakanin su,wannan ya kalli wancan_wancan ya kalli wannan,kamar an basu order tashi daya suka tuntsire da dariya harda rike ciki hade da buga kaga

Usainah kowah da bata dariya saina mugunta harda kwanciya a kasa saboda tsananin dariya hade da rike ciki

"Anty hassana don Allah kallo wannan katuwar tana kuka harda magina!."yayinda take kai nuninta ga jummai data tsaya sururu! Tana kallonta itama










Managed

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now