DAGA ALLAH NE! 04

1.1K 73 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖


💞💞💞
*DAGA ALLAH NE!*
💞💞💞



*FATIMA ZOIS*



Dedicated to *MY DEAREST PARENT*



Page4⃣


A guje safara da zuby suka yi kan anty jummai cikin tashin muduga ganinta a kwance ta kasa tashi,ta wani baje kamar wani karamin tsauni kafarta daban,tumbinta shima daban ga dan karamin kanta mai yanayi Dana kwallon mangwaro shima a gangare kamar tudu da kwari tana sumbatun

"Na shiga uku na lalace ni jummai yau karshena yaxo hassana ta haihu? Haihuwar mah koma mace! Anya ma kowah boka angama ya turawa hassana abinda yace zai tura mata din?!"


Kota kan maganar da anty jummai take yi zuby da safara basu biba kokarin su kawai shine koda tashi zaune anty jummai tayi amma sunyi_sunyi ta tashi sun kasa

Ganin anty jummai baxata iya tashi da kanta ba yasa Zuby ta rike hannunta tana Ja! Sai nishi take dirgikawa na gajiya kamar wacca take Jan wheel Barrow dubu

Ita koma safara tana turota daga baya saboda zuby taji saukin tashinta zaune amma ina! kamar an jibge buhuhunan kwaki ko motsi bata yi

Zuby data hada gumi saboda Jan da take yiwa anty jummai ga tsananin takaici na ko irin dan yunkurin kokartawa anty jummai ta tashi bata yi kawai dai tana shirgice abunta kamar Wanda sudin dadi suke ji idan suna wannan jan nata


Zuby Bata san lokacin da bakinta ya subuce cike da takaici tace"Gskia jummai masu daukar gawarki sai sun shirya......."


"Allah suturu bukwi! Ahir! Dinku wallah,Zubaidah bakinki ya sari danyen kashi! ai ko mutuwar ce mah taxo na tabbata tayi min alfarma in gama kawar da hassana kai harma da zuriarta gaba daya in dandani dadin zama da miji nikadai ba tare da kishiya ba muji dadin duniya nida mijina tare da yayana."@ anty jummai daga ji har ynxu bakar zuciyar tana kusa


Bata jira amsar zuby ba saboda itama pah tana jin jiki,Cikin azabar ciwo anty jummai tace"safara kije ki turawo min abbanku yanxu_yanxu kice yaxo ina nemansa!."duk da cewar tana cikin wani hali amma hakan bai hanata karasawa cikin izza da bakin mulki ba


Kamar yanda anty jummai ta tarbiyyartar da diyanta NATA,a guje safara ta tafy xuwa part din umma

"Duk dumbin jamaar da take ratsawa tare da wucewa hakan bai sanya safara ta budi baki tayi musu koda sannu ba bare gaisuwa ba, saima wani mugun kallo na isah da kasaita take binsu dashi daga gani ba yanxu ta fara hakan ba."


Kai tsaye! cikin bed room din umma ta shiga babu sallama babu komai kawai ta kutsa kai har ciki ta shige kamar ta shiga dandali tare da tsayewa mutanen wajen kere_kere a kai kamar bata San sudin su wayye gareta ba

"Abba wai kazo inji anty!" Abinda ta fada kenan cikin tsantsar rashin tarbiyya da rashin kunya

"Mummunan kallo safara bata ishi Abba ba bare ya tanka mata,yaji mah da abinda yake damunsa yanxu."


"Hajja da umma harma da el_Hussein sunsha mamakin jin cewar jummai tana kiransa amma yana zaune yaki tashi ya tafy jiki na rawa Wanda gaba daya hassana mah tafy su shiga mamaki."

"Abba anty pah tana nemanka yanxu_yanxu!." @safara ta fada cikin wata rashin tarbiyyar data tafy ta farko

Sautin mari kawai suka ji Tas!!!,"wai! Wai!! Wai!!! Yau an daki yar gidan anty jummai ba kowa bama sai abbanta chap! Yau fa akwai cakwakiya a gidan nan."@umma ba tare da tasan ta fada ba cikin tsananin mamaki da rudewa

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now