DAGA ALLAH NE! 33

914 53 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
*DAGA ALLAH NE!*
💖💖💖💖💖💖💖💖

*FATIMA ZOIS*
Wattpad @
*FATIMA ZOIS*

Dedicated to *MY DEAREST PARENT*

PAGE3⃣3⃣

Ai anty zee bama ta bari zahra ta karasa maganarta ba ta katseta cos tasan yanxu zahra zata jawo mata abun kunyar da baya da karshe
"Ya!..."

Don masifa zahra bata yi shiru ba saida ta karasa maganarta
"...In fito kenan kowa ya kalle ni"

Shiru anty zee tayi kamar ruwa ya cinye ta cos zahra ta bata kunya irin ta disgawar nan ba kadan ba musamman jin yanda mummy, daddy da rukayya suke kananun dariya da wata karamar yar murya alamar ita suke yiwa baso taji don kada su kunnowa Kansu cakwakiya,

Cike da takaici Mara iyaka Anty zee Ta sake fusata
"Zahra!!!...wallahi idan nazo wajen nan ba!?..."

"Anty zee gani nan"
Muryar zahran ta sake ji a chan laundry din, wato duk wannan halokokon! Da take zahran ko irin firgita ta taho din nan bata yi ba huh!?

A fusace anty zee ta fito daga toilet din tare da nufar laundry direct,
Bakam! Antyta  banko kopar da iyakacin karfinta tare da nufar inda zahra take

Itakam zahra data ji an banko kopa harta tsorata cos bata yi tsammanin ganin anty zee ba,
A hanzarce babu shiri ta dauki kayan wanki data gani a wajen ta rufe kirjinta  tare da samun waje ta buya

Cikin borin kunya Irin na bata ji dadi ba zahra tace
"Ya! Anty zee ya za'ai ki shigo inda nike without any excuse huh!?,
baki ganin irin babu kaya a jikina..."

Ko sauraranta anty zee bata yi ba ta  Janyo zahran ta karfin tuwo daga inda ta buya

Cikin tsoro da mamaki zahra ta kalli anty zee din ganin da gaske wai itace zata fita daga ita sai pant
"Anty zee pant ne pah kawai a jikina"

Still dai anty zee Jan zahran take kokarin yi ba tare data saurare ta ba cos tasan indai har tace zata tsaya sauraranta a dai_dai wannan lokaci to! Shakka babu zata iya ballata ba tare data ankare ba bisa ga wannan dumbin abun kunyar data shafco mata!,

Janta kawai take zuwa toilet din yayin da zahran itakowa take ta faman Dakirewa ganin anty zee da gaske fitan zata da ita a hakan,
wai ita ba zata fita ba iya pant ne a jikinta

Wani irin ihu zahra ta saki cike da makirci irin na mashahuran yaran da suka shahara ta bangaren sakamakon daure musu gindi da ake ganin ba zata iya hana anty zee ta fita da ita ba
"Wayyo ni na shiga uku zahran umma!, wayyo ni na shiga uku zahran BAabaa!, wayyo ni zahran Abba wayyo ni zahran haidar...,"

Dan sararawa zahra tayi alamar da ihun nata alamar taji ta ina mummy ko daddy zasu billowa anty zee domin su daukar mata mataki,

Unfortunately for her saita ji shiru sabanin Inda a gidan BAabaa suke tasan sai inda karfinta ya kare ko abbanta

Ba karamin haushi taji ba ganin yar kissar bata karbo ba,A zuciyarta tace
"Hash! Wannan mummy da daddyn halinsu daya da umma"

Ai tuni zahra ta sake sakin wani ihun amma wanda ya bambanta dana farko cos wannan na alamar ta taimako ne tunda taga Tugun NATA bai karbo ba,

"Wayyo mummyn yaya zuhra da ya Muhammad,ki fito ki gani,Wayyo daddy ka fito kaima kaga anty zee...Ya!... anty zee baki ganin  suna gane min nonona! Wayyo harda uwawu na....!?,
wayyo anty ruky Kinga anty zee...wayyo!!!..."

Wani tsaki na takaici anty zee ta sake jerowa
"Yarinyar Saidai kiyi ki gama amma yau din nan ko BAabaa ce tazo Saina yi miki wankan nan ehn!,
Wannan Ba rukayya bace da zata wani biye ki Sai abinda kike so."

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now