41

430 44 16
                                    


💖💖💖💖💖💖💖💖
*DAGA ALLAH NE!*
💖💖💖💖💖💖💖💖

*Fatima Abdullahi Ibrahim* ( _Fatin momma_)

PAGE4️⃣1️⃣

_Assalama alaikum,_
_Bahaushe yace idan laifi yayi laifi saidai mutum yace ya tuba!, Hakan nima ta wajena abun yake nasan nayi muku laifi tho am always like that!...Amma kada ku gajiya ko kara hakuri dani, , , na sadaukar da wannan page gareku masoyan *DAGA ALLAH NE!* especially my wattpadians , thanks_

  
   Aje chalk din dake hannunta miss uwani tayi ba tare data yi yunkurin yin komai ba , Babu wani tashin hankali , rudani,  fargaba ko damuwa ta cire micijin daga hannunta yayinda take aje shi gefe kai daga gani ta saba cos ada idan aka yi mata kofin micijin tsabar tsorata har satin ya gama bata sake dawowa indeed tasha yunkurin barin makarantar amma director ta nemi alfarmar Don Allah ta zauna harma albashi aka kara mata mai tsoka duk da da haka taki , da kyar da sidin goshi miss uwani ta yarda cos a hakan student din suna sonta

   Saboda duk ranar da aka ce miss uwani bata nan wani teacher zai dauke  su abinda ke raba shi da class din miciji da kunama ne in point of fact wasu ma sanadin barin aikin su kenan har abada , ba koma iya maths da quAntitative reasoning suke yiwa haka any boring subject ma babu ruwansu , ko koma idan aka ce sun tsani mutum ,
     ...Babu wanda suke wannan rashin arzikin a class din sai four idiot cos gaba dayansu babu wanda baiyin kofi na zahra ne dai idan tayi maka shine the worst of all
 

     Harhada abubuwan da zata bukata miss uwani tayi up to that time micijin bai tafi ba tana kallon shi yana kallonta cos ita zahra tafi ganewa da har sai miss uwani ta tafi sannan zata maida kofinta if not daga taga babu micijin zata sake cewa "kids lemme finish this examples please", koda wani malamin yazo saita nemi alfarmar "just a minutes don Allah bari na dan karasa " saboda zahra tace
  " Malaman maths basu hadu ba indeed anything calculation gaba daya malaman haka suke kullum suna cikin fadin please just a minutes lets just solve this solution daga nan koma sai randa Allah yayi tsayawar su"

   Ganin dai da gaske micijin bazai tafi bane ya sanya miss uwani kokarin fita cos ita a tunaninta idan wanda yayi kofin yaga tana kokarin ficewa dole zai maida kofin nashi saboda har yau basu san su wayye takamaimai masu yin kofin ba tunda kofin daban_daban ne
"Ba sai kun turo min da miciji ba am
going till next time, Assalama alaikum?"
Ta karasa da daga musu hannu

   Tare suka hada baki kamar abun kirki
    "Wa'alaikum salam"
Suma suna daga mata hannu

     Wani ihun murna da farin cikin gaba daya yan class din suka dauka kai kace anyi musu wani babban albishir ne da miss uwani ta fice

    Kallon zahra dan Kaka yayi cike da mamaki bayan ya gama bin yan class din daya bayan daya da kallo a matsayin sa na new a ransa yana mamakin wacce irin murna ne kowa yan class din suke yi haka akan miss uwani ta fita cos a lokacin da take teaching din babu ko kwakkwaran motsi na enjoyment a cikin wanda suka fi kowa zakewa da ihu suke yi there are just looking at her like a moron

    There are 15 in the class amma student din dake bibiyar abinda miss uwani take a sunyi yawa shine sukai biyar , sauran kowanne sharhuliyar sa yake bare Zahra da yusuf!,  wayannan su karshe ne kwanciya kawai suka yi abin su

    "Jeez!,
Mai yasa kuke murna haka alhalin anty bata gama solving wannan example din ba?"
#dan kaka ya fada yana mai kara tsananta kallon sa ga zahra wacca take saman desk tana tsalle da ihun murna

   Dan kallon shi zahra tayi ta watsar tana mai cigaba da tsalle_tsallen ta ba tare da ta damu ba take fadin
    "Muna murna ne saboda miss uwani ta fita kasan komai na lissafi baya da dadi"

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now