Chapter 18

236 16 4
                                    

**Matar Bature**
**Written by**
R.S.Balarabe.

P19.
kuka ta saki yayin da taga halin da yake ciki, idanun sa a rufe suke dan bangaren kuma hannunsane dauke da drip na ruwa.
Sai kansa da kafadarsa wanda aka zagaye da bandage.
Tunda aka kaisa bai farka ba.

Hannu takai izuwa hannunsa wanda ba drip din ta shafo kwantacciyar gashinsa mai laushi wanda ya kwanta yai kyau.
Ta tusa yan yatsunta cikin nasa sannan ta gamesu duka. Ta dade a hakan can sai ta daura kan nata a hannun nasa.
Momi kuwa dake gefe tabe baki take yi can data ga abin na shirin yawa sai tace."ke malama ki tashi,karki karasa min da. In banda salan iskanci mene na sha-shshafe mai jiki kamar kin samu kan yaro!".
Ta kuma tabe baki Ummi ko ufan bata ce mata ba duk da batajin dadin abinda momin keyi ama itama babu yadda ta iya tunda Anwar din ba danta bane tana sa baki Momi zata gwasaleta dan haka take kame bakinta.
A haka har bacci ya kwashe ta . momi tace. "Zo ki dauketa ,kar ta karasa min da."
Riketa Ummi tayi suka koma dakin da aka aje Aishan.
Washe gari tana tashi dakin Anwar ta wuce direct.
Har yanzun be farka ba. Sai wani doctor da wasu nurses a kansa suna dan duba shi.
A cikin nurses din har da Halimat .
Tana hada ido da it ta wurga mata hara .
Ta je gaban doctor'n ta tureshi."ni kuma tsamin sai mishi allura kukeyi bakuga yana bacci bane?".
Ta kama kugu tana faman girgiza.
Daman sun gama , suka juya zau wuce tasa dan yatsa ta tukiri keyan Halimat din.
Tana jinta aa bat juyoba.

Momi ta jinjina kai ."Ah lalle!,zota ki fita mara kunya ."
Ta juyo tana kallonta




Ta kada idanuwan   ta sannan ta koma kan Anwar,kare masa kallo tayi saida ta zo kan karan hancinsa  sannan ta furta a zuciyar ta "   wannan dan rainin wayon baze farfado ba?".
Juyawa tayi ta dumi Ummi dake zaune kan wata kujerar roba sannan tace. "Ummi, wai baze tashi bane sai faman bacci yake ko sallan ma yaki ya tashi yayi dan rai nin wayon ashe yasan bacci da dadi yake hanani kullum sai yazo tashina wai inyi sallan assuba."
Ummi tace" toh baki ga bashida lafiya bane,ko bakiga jikinsa da rauni ba?".
Ta tabe baki "uhmm na gani toh ai shi jarumine, kinga bari in tashe shi". Takai hannu ta daka masa duka a jinyar kafarsa ba shiri Momi ta mike tana banbami," wai ke wacce irin yarinyace mahaukaciya, ni bansan abinda kika tsinana a zuciyar Anwar ba toh wallahi bazan laminta ba aure zan masa dan bazan bari mahaukaciya ta kashemin daba ".
Aisha taja gefe tana kumbura fuska dan ko a jikinta .
Momi ta juya ta dubi Ummi "kinga   Ummi ki tashi ki tafi da yarinyar nan tunda ta samu sauki ".
Aisha najin haka ta tike karfen gadon da Anwar ke kwance ta rike gam.
Momi ta jefa mata harara " wallahi tafiya zakiyi".
Aisha tace,"  cab di jam ! Nida mijin nawa toh ninace ku auramin shi ba Yaya baturena nakeso ba kuka auramin mai allura wallahi babu inda zani...
Masha Allah🙏🏼
Bazance kome ba dan bakina baze iya furta kome ba idanuwa bazasu iya kallon ku ba 🙈😔
Kuyi hakuri ! Kuyi hakuri🙏🏼🙏🏼 insha Allahu nadawo kenan🌹

Matar BatureNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ