Chapter 15

308 12 0
                                    

**Matar Bature**
**Written by**
R.S.Balarabe.

              P16.
   Yawwa Dr. Anwar," muje office dina inason mu tattauna".
Anwar yace."leave me alone pls. Ina so inga Aisha kabari in na ganta sai muyi maganan  da zamuyi,"..
Dr.Mas'oud ya dafa kafadarsa" karka wani damu tana cikin koshin lafiya amma saide inaso ne muyi magana da kai first kafin ka ganta don  akwai abinda ya kamata ace na tambayeka".
Anwar ya juyadda  kai gefe ji yake tamkar ya tunkude  Dr.Mas'oud din.
Ya  daga hannu ya shafi karan hancin  sa tareda shafo sumarsa sannan ya juyo"okay ka fada abinda zaka fada in kuma ka dade bazan iya jirai tsayuwa  ba!".
Dr.Mas'oud ya kamo hannunsa ya kaisa   Office dinsa.
Sannan suka zauna saida Dr.Mas'oud ya dan nunfasa tukuna yace."Ammm... Dr.Anwar ban sanka da duka ko made ince fada  ba sai de hakuri sai gashi duka jiya aka daura maku aure,me tayi maka hakane ka duketa ?".
Tunda yake maganar Anwar ke masa wani kallon ,
Zaki yaja "Mtseew!,please Dr.Mas'oud yanzun ba lokacin wasa bane ka fada min halinda mata ta take ciki, in kuma surutu zakayi sai in tashi in barmaka gurin".

Dr.Mas"oud yai dan Murmushi"to ga raunuka nan a jikinta naga ma har a kafarta ka sa mata bandage".

"Toh ina ruwanka da abinda ya sameta,malan inzaka fada min halinda take ciki ka fada min in kuma ba haka ba ka barni inje in  duba ta!".

Ya yunkura zai mike Dr..Mas'oud yai saurin riko hannunsa"okay shi kenan zauna sai muyi maganan abinda ya kamata.".
Da kamar bazeyi hakan ba can sai kuma ya koma ya zauna yana huci.
Dr.Mas'oud ya cigaba da cewa."gaskiya ba zan boye maka ba ina ganin kwakwalwarta kamar da matsala, to shine nakeson tambayanka daman tana fama da ciwonne?".
  Sai da Anwar yadanyim tamkar baze bashi amsa ba sai kuma yace."Eh!tana fama da ciwon kwakwalwa kuma ya samo asaline tun tana cikin mahaifiyarta".
Dr.Mas'oud yai dan jim yana saurarensa can kuma sai yace."umm!daman bincikenmu ya nuna hakan sai de kan nata Allah yasa be sami wani matsalan ba sai de inna shawartarka da ku kiyaye gaba."
Yana kainan yayi shiru tareda rubuta ma Anwar wasu magungunan sannan sukai musabaha ya fice.

   Dakin da aka ajiyeta ya shiga Ummi ya samu a ciki tana zaune a gefen gadon ta, itako Aisha harde kafafuwanta tayi tana jijjiga da alama shi take jira.

Aiko tana ganinsa ta mike tai mashi wawan cafka wanda sai da botirin rigarsa daya ta fita.

Bin hannunta yayi da kallo
Beyi mamaki ba,ya ja ya tasaya yana kura mata ido,hannayensa yasa a aljihun wandansa .

Gani beyi wani nuna alamun tankawa ba yasa ta sakeshi.
Ta kama kwankwasa tana rangaji,can kuma sai tai kokarin bashi dariya dan inyace ze tabata zata iyya ballewa.
Ummi kuwa batace masu komeba illa binnasun da kallo.

Yai kokarin riko hannunta tai maza ta kabe hannu tareda sakin kuka.
"Dan iska kawai,kamaidani gun iyayena  bazan zauna a nan ba".
Tanayi tana dukanshi.
Ta tunkudeshi.
Ta kuma cewa."mugu azzalumi,ka maidani gun mama na dan iska me taba mata kawai."

Zafin maganganunta yasa ranshi ya baci besan sanda ya daga hannu ya kifa mata mariba don in beyi wasa ba Zata iya tara mishi mutane.
Yanayin haka yai  saurin jawota  hannunshi na rawa , ya hada kanta a kirjinsa yana lallashinta.
"Kiyi hakuri wallahi bansan na mareki ba pls.Aisha Humairata kiyi hakuri,kimin duk hukuncin da zakiyimin ".
Yanayi yana kuka Ummi kuwa  da mamaki da kunya da suka isheta sai ta bar masu dakin .
Dan ita mamakinta tun da take ta dade bata ga Anwar na kuka ba sai yau,a lalle Anwar an fada kogin so .
Tatun kudeshi sannan ta haye kan gadon can lungu tareda takure jikinta a bango.
Yai kokarin rikota ta dunga bugun hannun.
Da ya gaji ya rabu da ita.
Sannan ya fita a dakin  .
Gida ya koma da nufin ya kawo masu abincin dan sallamansu ba yauba.

Yana tuki wayarsa ta dau ruri JAKA!,aka rubuta a screen din wayar ,yai tsaki ba tareda ya dauka ba sai da tayi ruri har hudu na biyar dinne ya dauka ya kara a kunne ba tareda ya furta komeba.
Daga dayan bangaren aka furta."hello sweetheart! Tun jiya nake ta neman layinka amma baya shiga,wai me yake faruwane tunda kayi aure ka rabu dani gashi jiya kanin mahaifinka suka zo akayi mana baiko,amma naji dadi daka amince da auren mu."
Shiru yayi ya barta tana ta surutanta wanda sam be fahimci inda ta dusa ba.
Cikin nuna halin ko inkula yace."okay !good.".
Daganan be sake furta komeba har ta gaji ta katse wayar.
Mamakin maganganunta suka taru suka mishi katutu a zuciya .

Matar BatureWhere stories live. Discover now