chapter 1&2

1.6K 49 3
                                    

*Matar Bature*

**Written by**
R.S.Balarabe.


http:/Facebook. Com.wattpadhausanovelsonline.

Da sunan Allah mai rahma ,mai jink'ai. Godiya ta tabbata ga ubangijin halittu, daya bani ikon rubuta wannan littafin.
Wannan takardar kirkirarren labarine, nayi shine don ya nid'ashantar da masu karatu.

*jinjina da bangirma!' Mara adadi ga mahaifana, domin da bazarsu nake rawa, Allah ya saka masu da Aljannatul firdaus, Ammin.

Page 1


Wata motace kirar Toyota, gilas dinta tintec can. Take ta hon.
A wani tanka memen gida. Mai gadine yafito da sauri ya wangame gate d'in. Sannan motan tasamu daman shigowa cikin farfajiyar gidan. Ado mai gadi kuwa yana arba da motar yafara washe baki kamar mai tallan maklin, yaja yatsaya tare da kama kugu "yace"indo! indo! har an taso?" Ya rankwafo yana leken motan, duk da bawai yana hangen wanda ke ciki bane.

Ita kuwa Aisha dake kame acikin motan a baya ta galla me harara tareda murguda me karamin pink din lips dinta, kaman yana kallonta.motar ta nufi gurin parkin, tayi parkin, bata bari driver yakashe motarba ta balle murfin motar ta fito.
Yarinyace wacce bazata wuce shekara sha biyar ba., siririya CE, tsawon ta matsakaici, wankan tarwatsa CE. Idanuwanta manyane ba sosai ba, hancin ta dogone kaman karas, bakinta kuwa tsuke yake kaman an zana mata.
Uniform ne na islamiyya, me fari da ash, kasan cewar ranan asabar ne an dauko ta kenan daga islamiyya. Ko rufe murfin motar batayi ba, ta ruga a guje Kamar wacce aka biyota, ta nufi bangaren da ze sadata da main parlour . tura kofan tayi da karfinta, ta bankad'a falon. Tana faman kiran "mama!mama!"
"Keh! Shut up!, wai ke yaushe zaki girmane? Kin shigo ma mutane ba sallama, mahaukaciya kawai".
" Kai!kai!" Yaya Abdul ni kake cema mahau kaciy....a kohh! Tafada tana share majinan da tuni hawaye ya rigashi zuba "wallahi saina fada ma Baba" fewww! Ta wuce. Ko kallonta beyiba, yacigaba da kallon sa. ***Mutun ne wanda besan hayaniya ga jida kai, kuma uwa uba Soja.
Shine Wanda yake bin mata duk da ya girma mata da shekara goma. Mahaifiyarsu, su uku ta haifa. Umar, Abdulkadir wanda ake kira da (abdul) sai Aisha.
Mahaifiyarasu Ta rasu ne alokacin da takeda cikin Aisha.
Saka makon fadowa datayi a stairs.
mahaifinsu, yaji mutuwar matansa ainun. Dalilin dayasa ya Maida sunan ga yarsa.
Likita ya tabbatar ma Alh.musa cewa"diyarsa tasamu matsala a kwakwalwarta" kwakwalwarta ze dunga sizin.

mahaifinsu Alh.musa tsohon soja ne, bahaushe ne haifaffen Dan zariya ne, amma yana zaunane a kaduna . Ya taso cikin daula,shi kade iyyayenshi suka Haifa.

Mahaifiyarsa ta rasu yana da shekara goma sha uku. Yaji mutuwarta sosai , duk da a lokacin yana yaro, amma Halin rashin uwa akwai zafi, mahaifinshi yaso yai harkan kasuwanci ne Amma ya ki, don tun taso warsa yake sha'awan aikin Soja...
Ya auri matarsa ta farko , Wanda Allah beyi ze samu da a gurinta ba sun dauki shekara sha biyar.bayannan Allah yai mata rasuwa.
Sai ya kara aure ya , auri mahaifiyar su Aisha, Allah yayi da rabo a tsakanin su. Allah ya azurta su da ya'ya uku. Itama Allah ya an'shi kayanshi.
Hakika ya fuskanci jarabawaoyi kala kala
Sai da Aisha ta dan tasa don a wannan lokacin tayi shekara biyar.
wataran ya halarta taro na sojoji a Adamawa , a nan ya hadu da haj.Amira, bazawara CE a lokacin don mijinta beyi shekara ba da rasuwa, suka haduda Alh.musa sukayi aure. A yayinda ita Kuma haj. Amira keda d'a, daya . sunansa Ahmed,Koda sukayi aure dangin mijinta suka bukaci data basu dansu ko hakan ze rage masu zafi.
Alokacin yana da shekara goma sha biyar.
Haj.Aimra , farace sol, yar' a salin Fulani gaba da baya.
A yayin da kuma tsohon mijinta buzune.
Doguwace ga haci kaman ze tabo lebenta, gashi kan basena tsaya bayani ba don akwaisu, macace me fara'a dasan yara, hakan yasa take nunama Aisha so da Kaunah.

****
Page 2

Dakin baba ta nufa fuska cabe-cabe da majina. Ko sallama batayiba ta bankade kofar " Baba kaga Yaya Abdul koh..! Wai bana jin magana Kuma wai ni mahaukaciyace.

Shi ya bukaci da su dinga kiranshi da "Baba" duk da dan boko ne wayayye Amma ya tsani al'adar turawa...
Alh.musa yana kid'in shige a tutun dake tsakiyan kaya taccen parlour dinsa.
Sai da ya gama saurarenta tsaf!.
Hakan ba wani bakon abu bane a gurin shi, anjima ma bashi ze hana ta kwo mashi wani korafinba, don ita ko "kala" kace mata in har be gamsheta ba toh tabbas zaku hadu a kotun 'Baba' .
Shiru yayi kaman me nazarin wani abu' sai can kuma, "ya ce'. Jeki kira shi". "Toh!"tafada tana Zunburo baki tareda juyawa kaman wata me Bori....
Da sauri ta isa gurin shi "baba na kiran ka". Ta furta a dakile. Tareda rankayawa a guje, don tasan halin yayan nata. Ba karamin aikin shi bane ya mammaketa, duk da baba ya hanashi.
Sallama yayi. "Baba gani!" Yafada tareda tsugu nawa kusa da shi.
" ka kyauta!, baba yafada cikin kakkausan murya." Ta inda baba yake shiga ba ta nan yake fita ba." Daga yau kar wanda ya kara bata ma humaira rai!' So kuke Ku karasa mun ita? Cikin fushi yake magana.
Shafo kanta yayi tareda jawota izuwa kan jikin shi, sai yaci gaba da cewa.'' Ni inba dadin doctor yace "a sata a makaranta islama ba don kwakwalwanata ta dunga budewa", ai da Sam bazan bari ta dunga fita ba,ko da nan da gate ne".
"Baba kayi hakuri!" Abdul yafurta yana mai sadar da kai kasa
"Fita kaban guri!" Baba ya fada tare da nuna mai kofa, sim-sim ya tashi ya fuce.
Ita ko Aisha sai faman wasa take da furfurar baban na ta,dake sumar sa. Wanda take kira da"kwarkwata". Sam bata San abinda ke faruwa ba. Dan ba jinsu take ba. Hankalinta na ga kwarkwatan babanta.
Kara rungumota yayi, yadan nunfasa, tukuna yace,''Humaira!, yau me aka koya maku a makaranta?, ji yadda kikayi datti da uniform dinki".

"Ni...?
"Eh!, nace me kika koyo a islamiya?"
Dariya tayi sannan ta dan Gyara zama tareda cusa Dan yatsunta a bakinta. sannan tace"baba ai yau ba abinda mukayi. Ohh! Natuna malama kursum ta koya mana addu'an shiga bayi."
" Okay... Toh yanzun koya min kinga ban iyya ba"
"Baba baka iyya ba?, hu'umm!, tafada tana turo baki. " to ai nima na manta! sanda take koya mana ni inna bacci."

"Lah!" Rike baki yayi tare da fadin "Subhanallah!, haka kike yi ko? Bakya son karatu, ko bakya sone kiyi kiba ne?
Duk duniya babu abin da ze firgitar da ita ko yasa ta tai abu, kaman anbato mata kiba. Tana matukar son kiba, kasantuwar ita din siririya CE.Mama na yawan tsokanan ta da "jijiya da rai kashi da bala'i" musammam ma inta mata wani abu ba dadaiba. Takan turo baki ta bata rai, don a rayuwarta ta tsani a kirata da siririya.
Hakan yasa shima mahaifinata ke mata dubara da haka.

Zunbur tayi, kaman wacce aka tsungula,sannan tace "to baba daga yau bazan kara bacci a makaranta ba".
Sallaman mama ne yasa dukkansu dago kai suka kalli kofa.
Mamane tashigo dauke da farantin kayan abinci.
Dire kayan abincin tayi a kan tabirin cin abinci dake ma keken fala., tare da cewa"Aisha kin dawo ne".
"Eh nadawo".
Aisha ta amsa.
"Okay! Toh je ki cire uniform ko?, se kizo kici abin ci"
Da sauri ta mike tai hanyan kofa,
Can sai ta ju yo."mama tareda Babana nake so in ci!''.
"Toh naji ! yi sauri karki manta kiyi sallah!."

Kallon maman tayi tace "mama kin manta munayin sallah ah makaranta!."

Mama dafa kai tayi da hannu sannan tace "Ohh!,hakane na mantane toh yi sauri kije ki cire kidawo.
Rugawa tayi a guje , da sauri take taka matattakalan da ze sadaka da main parlour. Kicibis! Tayi da yayan nata Abdul dake ta faman loma a kan tree sitter hanka linshi nakan abincin da yake ci. Don be wasa da loma....

Vote me on
*wattpad*
@00Ruky.

Matar BatureWhere stories live. Discover now