chapter 24

264 9 0
                                    

**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**


Pg25

Yau ta kasance an daura auren Anwar da Summayyah,  bayan yinin biki ba abinda akayi sai da yamma aka kaita gidan angonta Anwar.
Aisha ce kwance kan three sitter a parlour tana wasa da yar tsanar ta jin horn din mota yasa tai saurin zuwa bakin gate Tijjani mai gadi taga yana kokarin bude gate. Ta rike gate din sannan tace.,, waya aikeka ka bude daman da hadin bakin ka ko.,,
Ta wurga mai harara.
yace. Haba hajiya ni asu wa .,,
Tace .,, toh ka matsa gefe , tunda ba ruwanka.,,
Tana gama fadan haka ta fita waje.
Motoci ne tagani duk sun jero,  nan ko ta coge,  da suka ga bata da niyan matsawa suka fara futowa harda Amarya kokarin bude kofan gidan sukayi. Aisha tace.,, kai! Me zaku shigan mana gida kuyi?,  wayace maku nanne gidan da za, a kai Amaryar?,  toh wancen gidanne.,,
Ta nuna gidan daya hada katanga da gidan wanda duk layin kusan iri dayane baka tantancewa sai da number.
Nan suka fara kace nace zakaninsu Summayya data ga ana kokarin juyawa da ita nan ko ta daga gyalenta daya rufe mata fuska tace.,, nanne gidan !.,,
Tana nuna shi da dan yatsan.
Drivern Anwar ya fito ya bude gate din duk suka shiga ciki.
Rugawa daki tayi ta haye gado tana kuka sosai ta kankame yar tsananta wadda itace a koda yaushe take zame mata uwa kuma uba.
Bayan sun  ajiye Amaryarsu duk aka watse sai Salima data rage suna jiran shigowar Anwar in yaso su karbi kudin ganin Amarya.
Har shadaya na dare babu shi babu alamunsa.
Salima tai tagumi tace.,, to wai ke haka ze runka miki shuru ya manta dake,  kinga tafiyata nikam dare nayi inyaso mayi magana ta waya.,,
Tamike sukayi sallama sannan ta wuce .
Sai Shabiyu tukuna yashiga gidan zama yayi a parlour sam ya rasa abinda ke masa dadi tun safe rabon da ya saka wani abu a cikinsa kuma hakanan bayajin ze iya cinkome dan jin miyon bakinsa yake tana masa daci.
Kafafunsa ya mikar idanunsa a rintse , firgigit yayi sadda ya tuna da Aisha,  a kasale ya mike ya nufa dakinta , tun daya daura hannunsa a marikin kofar yakejin shashshekin kukanta nan yashiga ya sameta kankame da yar tsanan ta tana kuka. Bakin gado yasamu ya zauna nan ya tallabo kanta ya daura kan cinyarsa ya kai hannu kan kumatunta yana share hawayenta ga mamakinsa sai kuma bata hanasaba.
Sam taki tayi shiru,  tafin hannunsa ya daura kan bakinta da nufin ya rufe mata bakin aiko takai masa cizo ba shiri yaja hannunsa ya rike yana duba hannunn nasa bako karamin cizo tayi masa ba dan  saura kadan ta yaga masa naman hannunsa.
Yace.,, Aisha cizona kikayi fah.,,
Ta wurgame harara kana ta juyadda kanta gefe  sannan taci gaba da kukanta .shiko tagumi yasha ga wani bacci dake damunsa.
Summayyace ta fado dakin daga ita sai yar singlet iya gwiwa. Tun da ya kalleta be kara kuskuran kara juyawa ya kalleta ba dan kyama take basa sam bata birgesa.
Cikin tsiwa tace.,, Aww ! Ashe tare kake da yar iskan nan ka barni inata jiranka.,,
Nan Anwar ya tunzura yace.,, keh!  Wacece yar iska?  Yar iska ya wuce ke, mara kunya inba rashin kunya ba yaune ranan da zaki kasance cikin kunya amma jibeki,  toh, bari in gaya miki kallo daya nake miki da akuya.,,
Idanun Summayyah sukai ja .,,  lah!  Yaya Anwar ni kake jifa da irin wadan nan magan ganganu.
Rai kwafa sannan tajuya ta koma dakinta  Tsakiyan gado ta haye ta fara kuka sai ta mika hanu ta jawo yar jakarta ta ciro wayarta cikin kuka ta latsa numbern haj.ladidi. bedade yana ringinba ta dauka nan ko ta zayyane mata sa insan da sukayi da Anwar. Haj.ladidi tace.,, toh ke me abin tada hankali a nan bayan bokanmu ya ce da zaran kin kusancesa kome zeyi daidai kinga ki kokarta ki shawo kansa kuma ki daina nuna masa bakyason matarsa inyaso da zarar ya yarda dake kinga shikenan,  kuma karkiyi wasa da maganinnan kamar yadda boka yace ki zuba a ruwan wankansa.,,
Ta jinjina kai sannan sukayi sallama.
Anwar kuwa dakinsa ya wuce yasha baccinsa.
Bayan yayi sallan asuba ya dawo ya shiga dakin Aisha, da kyar ya tasheta ta shiga bayi dan tuni idonta a bude suke kintashin ne batayi ba dakin ya zauna ya ciro wayarsa yana duddubawa bayan ta fito ta haye gado ta kuma lullube jikinta da bargo . juyawa yayi ya kalleta fuskarsa cike da mamaki yace.,, Sallan fah ?,,.
Ta jefa mishi harara.,, baza'ayi ba. ,,
Kame bakinsa yayi yai shuru dan yasan dalilinta tunda tasan kome.
Dai dai yana duba wayarsa  kira ya fara shugowa na Tijjani mai gadi.ya dauka kana ya kara a kunni. Ya sanar masa da zuwan mai aikin da ya umarce shi daya kawo masa.
Mikewa yayi ya fita. Matashiyace tana ganinsa ta duka kasa tana gaidasa bayan ya amsa tace.,, Alhaji sunana Mairo.,,
Ya jinjina kana ya dubi Tijjani yace.,, ka fada mata Albashinta ko ?
Tijjani yai saurin fadin.,,Eh Alhaji.,,
Mika hannu yayi aljihunsa ya ciro dubu talatin ya mika mata sannan yace.,, ga wannan albashinki na wannan watan sannan duk aikin cikin gidan ya rataya a wuyanki,  nasan ba sai na ambatomiki ba  tunda bayau kika fara ba.,,
Cikin ladabi Mairo tace.,, Eh hakane Alhaji.,,
Yace.,, biyo bayana innu namiki wasu guraren ayyukanki.
Suka shiga ciki ya nuna mata Kitchen da store da wasu dakuna dakuma bayan gidan.
Sannan daga karshe ya nuna mata wani daki dayake dauke da katifa sai toilet yace.,, nanne dakinda zaki runka kwana .,,
Har kasa ta kuma komawa tana masa godiya.
Sai kuma ya kara dacewa.,, yanzun innaso ki hada mana break fast amm,  zakuma kina ba mai gadi.,,
Yana gama fadan haka ya koma dakin sa.
Nan ko tashiga kitchen tafara .
Nan da nan ta soya dankalin turawa da kwai sannan tai farfesun kaza sannan ta tafasa kayan tea tasa kayan kamshi.
Ta fito dasu ta jera a diningT.
bayan wasu minutes Anwar ya fito ya shiga dakin Aisha ai ko batayi jayayyaba ta biyoshi dan ba dan karamin yunwa takeji ba.
Nan ko suka zauna suka faraci saiga Summayya ta barbado turare  tasha less maroon  takuma coge dan kwali ta zubo da attache din gashinta tana rakwarkwasa ta zauna a gefen Anwar sannan ta bude kulolin ta diba abinda zata diba ta faraci.
Bayan sun kammala Anwar ya mike da nufin komawa dakinsa  aiko tabiyo bayansa daidai zejuya ya rufo kofarsa ta fado dakin yace.,, keh ! Lafiyan ki? .,,
Ta langawabe murya. ,, haba miji na saikace ba matarka ba kawai ninashigo ne mugaisa .,,
Yaja tsaki sannan ya koma bakin gado ya zauna duk turaren data balbala amma warinta yakeji ji yake tamkar yayi amai .
Wani turare ta ciro a hannunta wanda besan ta shigo dashi ba. Ta fara fesawa a jikinta takai hannu zata fesa mai ya tunkude hannunta.

,,wai ba gaisuwa kikace zamuyi ki tafi ba.,,
Be ankaraba ta fesa masa turaren wanda bokansu ya umarcesu dasu fesa masa domin da zarar yashaki turaren shikenan sun gama dashi.
Ai ko tundaga lokacin yaji kansa najuya masa sai kuma ya tsinci kansa da san kamshin warinta dayake ji da tsanarta ya nemesu ya rasa...

*Follow
Vote
Comment
share*
On Wattpad @00Ruky.

Matar BatureWhere stories live. Discover now