Chapter12

361 15 2
                                    

**Matar Bature**
**Written by**
R.S.Balarabe.

          P13
Mama ce ta bude kofar sannan ta   shigo,  tana ganinta ta ajiye wani ajiyan zuciya, ganin hakan yasa ta wurga ma Anwar harara tayi hakanne ganin yadda yake kallon yana nazari tamkar me neman wani abu  a fuskarta.

Rangaji takeyi sosai a gadon la'akari da hakan yasa  mama tace" ah fitsari kike jine haka bari in dauko miki Poo".

Hade rai Aisha tayi tana tutturo tareda turo idanun ta tace,"  Poo kikace  Allah ya kiyaye in hau  poo,sai.kace  jaririya kuma ma  a gaban wannan mutumin. Allah bazan hauba".
Tana fadi tana kuka, yau  kwanansu hudu a asibiti bata cikin hankalinta sakamakon ciwonta da ya tashi sai yau ne ta dawo dadai don haka batasan da wani hawa poo ba.
" bazaki  hau bako!, to shikenan  bari Anwar ya dauraki a keken ki inyaso sai in kaiki bayi tunda kinki hawa poo din" mama ta fada tana dubanta.

Mikewa   Anwar yayi yana   fadin" mama ni zan wuce gida  in kuna bukatan wani abu   sai ki fadamin inzanzo gobe sai in taho maku  dashi".
" A'a bakome Anwar, Allah ya saka maka kana kokari, kai tafiyanka kawai Allah ya bamu Alkhairi".

"Amin!" yace tare da jan kofar  ya fita.
Motarsa ya bude sannan ya maida ya rufe key yayi dadai lokacin wayarsa ta dau ruri, ringing din momi yaji wato mahaifiyarsa cikin hanzari ya daga yana fadin ," Assalamu Alaikum!".
Ta amsa ba yabo ba fallasa " inna wayanka ya shiga tun da safe nake faman kira amma switch off!,kayi tafiyar ka kwana biyu kace  min yau gashi kusan sati daya kenan uban mai kakeyi da bazaka dawo ba? Toh ina so gobe ka kamo  hanya kasan batun aurenku da sumaiyya ya kamata ace kun hadu kafin ai maku baiko. Saboda   haka ka tabbata ka dawo gobe".
Tana kai   nan ta katse wayar.
A hankali ya cire wayar dake manne a kunnensa tashin hankali suka bayyana a zuciyarsa,
shi yamanta da zaman wata wai sumaiyya don rabon daya ganta tun suna wasan kasa.
Dafa kansa yayi wanda yake sara masa gashi dollensane ya kama hanya gobe sanin halin mahaifiyar tasa yasa  baze iyya jada maganarta ba macece mai tsatstsauran ra'ayi inta fada magana ta fada kenan.

Da sassafe ya kimtsa kayayyakinsa tareda yin masu sallama kafinnan ya kira Ahmed da mama itama ta jinjina daga karshe tai mashi Allah ya tsare.
Har mota Baba ya rakosa sukai masabaha sannan ya koma ciki.
Abdul ya rungumesa " gaskiya zamuyi missing dinka".
Anwar yayi murmushi" karka damu   Abdul", sai kuma yai shiru kamar me  nazarin wani abu, saida yadan  nunfasa tukuna  yace," sai anjima". 

"Okay sai anjima ka sauka lafiya".
Abdul yafada yana daga masa hannu shikuma   Anwar yaja motarsa yai gaba.
Cike da  kewa  suka rabu.
Sautin karatun qur'ani ne kawai ke tashi a motar har Allah yasa ya isa lafiya.
Batai masa magana ba a ranan kasantuwar yadda taga ya gaji.
Washe gari da daddare bayan ya dawo daga office.
A dakin ta ya zauna yana cin abinci.
Ya sani sarai jiransa take ya kammala cin abincin  gani haka yasa ya fara tsakuran abincin tamkar wanda besan ci ita ma ta lura da hakan tace,"  sannu Anwar in baka cine ai saika maida inda ka dauko ko ,toh ni ba wannan  ba ya maganar Sumaiyya gobanne zakaje ku zanta kamar yadda na fadama nanda sati uku za ayi baikonku kuma bawani ranaku za a sa masu yawa ba wata biyu ne don  bansan bata lokaci saboda haka tun yanzun ka fara shiri!".
Abincin da yakeci tai kokarin tsaya masa a makogaro da kyar ya iyya hadiyewa ya bude murfin goran ruwa ya sulala a makogaronsa saida ya kusan shanyewa  sannan  ya  dire goran tare da rufeta da murfinta.
Ya dago ido ya kalli mahaifiyar tasa a ransa yana fadin"anya momi tasan so kuwa anya tasan radadin son wanda baka so kuwa son wanda ka  tsana a rayuwa?,da ace ta sani da batai kokarin tilasta mashi son wace yake tsana a rayuwarsa ba taya ze iya zaman  aure da wannan kucakan yarinyar marakunya wacce bata ganin girman na gaba da ita!".
Momi ta katse shida "   bakaji ina magana ne ?".
Ya girgiza kai
Tace,"Ah!,lalle Anwar na lura kwana biyun nan ka na wasa da maganata ,cewa nayi gobe zakaje gidansu ku zanta kuma zan sami Alh. Muyi maganan!".
Bece mata uffanba lura da cewa ta gama maganar yasa ya tashi jiki asullube.

Matar BatureOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz