Chapter14

301 11 0
                                    

**Matar Bature**
**Written by**
R.S.Balarabe.
       

           P15.

   Wani irin ihu ta saki mai tayar da hankalin duk wanda yake gurin
Ta saki kuka," sace ni kayi ?,mugu   azzalumi, wallahi ka maidar dani  gidan mu .
ka saceni saboda kayimin Allura toh wallahi baka isa ba!".
Ta na kainan tai kokarin fita daga fallon ,ta ruga waje zatai gate .
Anwar ya bi bayanta a guje tana gudu iya karfinta, gashi gate din gidan akwai dan tazara, bata sani ba ashe akwai dutse a gabanta ,ta buga wani wawan tuntube da kafarta ta karaya ,ta fadi kasa tana kurma ihu sosai.
Yai hanzarin zuwa kanta yana salata, hannunsa na rawa ya taitayota sannan ya daura kan cinyarsa. ga gefen goshinta dake dan fidda jina kasantuwar ta fadi ta kaine.
Tana kuka tana ihu ta tureshi tana kokarin mikewa amma inna  kafarta ta kasa.
ciccibanta yai ba tareda yace mata komeba sannan ya shiga da ita parlour ya maida kofan ya rife tareda sa mata ki ,ya jawo key'n  ya tusa a aljihun wandansa sannan ya kai hannunsa fuskarsa  ya jawo gilas din ya rike a hannunsa sannan ya haura dakinsa.
Ya dawo hannunsa dauke da   akwatin tai makon gaggawa
( First Aid Box).

Ya diresu a gabanta, ya bude tareda ciro kayan aikin.
Yakai hannu izuwa goshinta tai saurin bige hannun ."wallahi karka tabani  ai daman na sani kai kayi   ma mama wayo kace zamuje dinmer ashe nan zaku kawoni ,kilama gidan yankankai ne".
Be biye ta tata ba ya haye kan ruwan cikinta ya matse hannun saida ya gama goge jini yai kome ya dawo kan kafar shim ya gyara inda taji ciwo wanda a dan yatsanta babba sannan ya tashi , in   banda kuka ba abinda take.
Yana kammala kome ya maida kayan.
Jim kadan sai gashi ya dawo ya sauya kaya izuwa wasu shadda me gajeren hannu Ash.
Ya samu guri ya zauna kan hannun kujeran da take zaune sannan yace."Tashi muje gurin cin abinci kamin Allah yasa mu sami mai aiki ,nasan rabonki da abinci tun jiya ko?".
Yana maganar tamkar me tsoro, don ya sani sare yunwace da kewa yasa ta dan natsu  haka inba haka ba ai ba karamin hauka zatayi masa ba.
ko tankashi batai ba sai kuka. tanayi tana share kwalla.
Yai shiru yana kallonta hakika har cikin ransa yanajin ba dadi ga kukan da takeyi yanasa zuciyarsa najin wani iri.
Jiyayi kamar ya lallasheta amma yana tsoron abinda zeje ya dawo  sanin halinta.
Sai can wata dubara ta fado masa.
Cikin tattausan murya wacce ta kara ma muryarsa kawa,yace," toh Shikenan Matar Bature tashi muje in kaiki gurin mama,in kuma kika ci gaba da min kuka shikenan!".
Da kamar bata jishi ba sai kuma can ta wai go tana kallon sa.
Tai tsuru tana kallansa.
Ya mike yabude kofa sannan saita biyo shi.
Yadan waigo tareda kura mata ido, suka hada ido .
Ta juyadda kanta gefe tareda turo small lips dinta.
Yace."kije ki canza kaya ko so kike mama karta ganeki gashima da alama MatarBaturen ma batayi wanka ba!".
Ta juyo ta kalleshi sannan ta wurga mashi sababben harararta wanda inda sabo ya saba shi har hararar ta fara birgeshi.
Takuma turo baki sannan tace."to ai banda kaya."
Ya kamo tsintsiyar hannunta da nufin zuwa dakinta. jiyayi tamkar ya rike rular don
siranta, ya saki dan murmushi,
Suna tafiya yana wasa da dan hannu .
Lura da hanka takai mishi tsunguli a tafin hannunsa ya juyo ya kalleta ta kara jefa masa harara tareda murguda mai baki.
Hakan da tayi yasa yaji tamkar yacigaba da tsokananta ko dan ta sakemai hararar da take matukar burgeshi.
Haka suka wuce daki  ya bude wardrobe ya ciro doguwar riga pink mai kyau.
Sannan ya kuma dubo wasu takallma a kasan wardrobe din pink shima wanda ya kayatu da wasu stones masu matukan kyau.
Ya kara kai hannunsa izuwa gefen mayafai ya jawo mata wata gyale sannan ya dire matasu a gabanta ya maida wardrobe din ya rufe.
Ita ko da take bakin gado bin kayan tayi da kallo sannan ta daga kai ta kalleshi fuskar nan a murtuke. Shima binnatan yayi da kallo daga  karshe ya fara takawa don barin dakin,har ya kai bakin kofa ya daura hannunsa a marikin kofar sai kuma ya juyo.
Yace."kiyi sauri ki saka su,ina jiranki a parlour!".
Yana gama fadan haka ya jawo kofan.
Har yafita waje sai ya tuna da wani abu,ya dawo sannan ya laiko dadai lokacin tana kokarin tube kaya.
Cikin sairi yace."amm..kiyi sauri..karki manta kiyi sallah inyaso sai in jiraki."
Yana gama fadan haka yai saurin fita.
Hakan kuwa tayi don bata son abinda ze hana taje taga mamanta da babanta.
Saida ta yi wanka da alwala  tai tsap sai kuma ta duba bataga hijabin da zatai sallah dashiba.
Fito wa tayi daga daki izuwa waje inda yake a cikin mota ta sameshi ya fito da kafa waje da wayarsa a hannunsa.
Tsayawa tayi a gabanshi tamkar me neman taimako tai narai narai da fuska.
Ya dubeta yace."Me ya faru Aisha har kin kimtsane?".
Ta karkadame kai tareda turo baki, can tace ."Hijabi!".
Yai murmushi tukuna ya mike suka koma dakin ya  kara dubo wa sannan ya bata ya fita  tayi sallan sannan suka kama hanyan zuwa gidan su Anwar.
Tana ta murna wai ita a nan dole gida ze maida ta. Bata saniba bama a kaduna take ba.
Saida taga sunkai dadai wani gida yayi horn sannan ya juyo ya kalleta suka hada ido, ita de tasan nan ba gidansubane kuma ma beyi kama da hakan ba.
Tace."ina ne nan?, wani gidan yan kankai ne ka kawo ni kuma?".

Matar BatureWhere stories live. Discover now