Chapter5

583 24 5
                                    

**Matar Bature**

**Written by**
       R.S.Balarabe.

                   P6
Ahmed ne zaune a office, yana jujjuyawa , watan shi biyu kenan A kaduna,gabaki daya ya gaji don ranan sunyi aiki sosai,duk dade kullum aikin iri dayane. Kallon agogon hannun sa yiya,6:00pm. Ya gani , mikewa yayi , tattaro wasu ta kardu yayi, yadan yi packing din dinsu  tareda sasu cikin file, ya ajiye a cikin wani safe.daukan key dinsa yayi ya fita.
           Gida ya wuce, Aisha ce ya samu a parlour, a bakin fridge ya sameta tareda kujera ta zauna, ga wani Ac. da ta kure, rawar sanyi yaga tanayi, tsayawa yayi , yana kallon haukan yarinya uwa yar kauye.fad'i yayi a zuciyarsa''yarinyannan banda ciwon  hauka , babu wani abu dake damunta kuwa!".
   Wucewa yayi ya barta a gurin, dakinsa yashiga, yai wanka tareda alwala, canza kaya yayi ya sauya dawasu brown T-shirt da jens , ya wuce masallaci domin yin sallar margrb, addu'a yayi da ya idar. ya dawo koda ya dawo be ga Aisha ba dakin mama ya wuce be gantaba, da alama tana toilet ne.
juyawa yayi izuwa dakin abdul , can ya tuna ashe ya tafi zariya sai gobe zai dawo.
tunawa yayi da sahibar sa.

Dakinsa ya koma, zama yayi akan kujerar dake gefen dakinsa, dauko wayar sa yayi tare da dialing din number'n ta , ba jimawa ta dauka "hello, dear". Ya furta.
 "Ya kake?, hmm! Kasan mai yayana, Albishirinka!". Rufe fuska tayi kamar tana kallonsa.
Yace "Goro!".
Dariya tayi sannan. Tace," Baba ya ce...."
Shiru yayi yana sauraron ta, can yace ," yace mai?".
Juya eyesball dinta tayi.tace," ahmm baba ya ce  za' a sa ranan aure..n mu ".
Dariya yayi sosai can kuma ya bone, har ransa yaji dadi hakan, daman an musu baiko,
Sun dad'e suna hira , har saida isha'i, tukuna sukayi sallama, ya kashe wayar,sam ya manta cewa be ci abinciba , banda cake din daya ci a mota kamin ya dawo gida.
Mikewa yayi ya wuce dakin mama, ihun kukan Aisha yaji, kamar wacce ake yanka naman jikinta,   har ta dan bashi tsoro don be taba jin tayi hakan ba, can yace," koh ciwon natane ya tashi?", can ya kuma cewa " toh ai  bata taba yin hakan ba!".
sallama yayi ya kutsa kai ya Shiga, doctor nazir ya gani wato likitansu wanda kezuwa dubasu a gida, tare da allura a hannunsa
Ganin Aisha yayi a 'kasa daga ita sai riga da underwear , zanin a cen gefen sai faman kurma ihu take, dariya taso ta kubce masa.
"Yawwa! Ahmed, dan Allah zoka rike ta, kaga tun dazun ake fama da ita". Mama tace.
Kallon Aishar yayi tun daga sama har kasa , jinjina kai yayi yace," toh me ke damun ta?".
Mama ta amsa da," wallahi zazzabi ta tashi dashi yau, nayi zaton jikin nata zaiyi saukine,naga tayi amai ne shine na kira Dr.Nazi, don ya dubata, ka ganta nan.. Don Allah zoka riketa".
Kara kallonta yayi a karo na biyu, shi kyama ma take bashi, da kyar ya iya dauko ta, akayi mata alluran.
Koda aka gama mata alluran bata bar kurma iyu ba, kara kwanciya  tayi a jikinshi.
Juyawa tayi ta kalli mama.tace," mama kiban baby NA".
Dariya mama tayi tace," ah lalle Aisha zafin  alluran ne haka, ko harkin warke?, toh, ni yanzun bansan inda kika ajiye babin naki ba".
doctor'n ne ya katse mama da cewa," insha'Allahu hajiya zata ji sauki,ammm, sannan kuma zan sa mata drip , saboda jikinta na bukatan ruwa sosai ,gaskiya".
" drip?,kuma doctor!, kana ganin allura ma da kyar fa akayi mata, okay".
Mama ta fada.
Zaro kayan yayi yace,"a nan za a sa matane?".
Mama ta ansa da,"Eh doctor...".
Caraf Aisha ta cabe
" A'a!", ta fada tana turo baki, sai wani rangaji take a kan cinyan Ahmed tamkar ta samu lilo.
" ni a dakin yaya Bature zan kwana!".
"Eyye". Mama ta fada
"Toh ai ke ba matar sa bace, kinji Humairata kiyi hakuri kinga bakida lafiyane".
Dago kai Aisha tayi da kyar sannan tace,"lah, mama kefa kikace ni matar bature me!, babu wani karya kikeyi". Daga ido tayi ta kalli Ahmed sannan tace," ai ni matarka ce ko?".
Ji yayi kama ya saki kafarshi ta fadi kasa,don haushi, wani makaki yaji a wuyar sa" Allah ya kiyaye".
Ya fada a zuciyarsa.
Mama ta dan kyafta me ido  ta kalleshi tace," toh shi kenan Ahmed dauketa kakai ta dakinka itama ai matarka ce".
Ko nuna yaga sign din beyiba, balle ya motsa daga inda yake.
  "Ta dubi doctor'n tace ," Dr. Bari muje dakin nasa sai a sa mata a cendin, in ba hakaba gaskiya bazata bariba, dade ace Abdul na nanne shine kadai zeiya da ita.

Matar BatureWhere stories live. Discover now