Chapter 17

292 15 4
                                    

**Matar Bature**
**Written by**
R.S.Balarabe.

               P18.

Mutumin yayo kanta. Tana kainan ta tashi daga mummunan mafarkin da takeyi Anwar da   ya dawo yana shirin shiga dakinsa shima ba karamin razana yayiba dan ihun har cikin kwakwalwar sa.
A guje ta fito daga dakin shi kuma yana kokarin shiga.
Kansa ta fada tana kuka."zai biyoni."
Tanayi tana nuna dakin da dan yatsanta
."waye !". Ya fada.
Ta kara kan kameshi gam ya riko hannunta da nufin shiga dakin. ta saka mai ihu ba shiri ya dawo baya . dubanta ya taya yi shide yasan yai ma gidan sauka balle ace akwai wani abin tsoron a ciki.
Kan kujera ya ajiyeta shikuma yashiga dakin yai dan dubeduben sa bega kome ba.
Yadawo  ya kamo hannayenta biyu yace."Aisha! Gaya min   me kika gani dodo kika gani."
Ta hade mishi kafada  alamun ba zata amsa ma maganarsa ba.
Ya kuma cewa
"To mene?".

Ta kuma dage kafada.
Yace."toh ai shikenan bari in kira dodon kiga sai ya tafi dake gidanshi koh."
Ai tanajin haka ta sauko daga kujeran ta kankameshi tana kuka.
Cikin kuka take fadin."Ba dodo bane ni ka maidani gida bazan kara kwana a gidanka ba!".
"ai  shikenan    sai in kaiki gidan dodon koh.!"
Bata tankashiba sai kuka da takeyi.
Dakinshi ya dauketa sukayi dakyar ta yarda ya ajiyeta a  bakin gado wai ita tsoro take ji.
Wayarsa ya dauka suka fita waje iskan gurin yana hurasu ga kukan tsintsaye gurin gwanin ban sha'awa da birgewa.
Ya kwala ma Tijjani maigadi kira bai bata lokaci ba yazo gabansa tareda russunawa.
Yace."ina ajiyana? ina fatan dai kana kulamin da ita."
Tijjani yace."Eh,ai yanzunnan na gama bata abinci ko in dauko tane?".
Anwar ya shafa karan hancinsa yana duban kasa kana yace."uhm,dauko ta inaso in   ajiyeta a cikin gida kasan kishiyar mata tace".
Ya fada yana duban Aishan da murmuhi wanda kalamunsa yasata saurin dubansa.
Ba bata lokaci sai gashi da Aku.
Ya taho da ita Anwar yasa hannu ya karba.
Ya mika ma Aisha ta ki karba tana bata rai.
Yace ."ba  zaki ansa ba,ko bakya sone?".
Ta hade giran sama da kasa tana turo baki sannan tace."ba kishiyata bace ni bani san  ta, kuma ma ba wannan ba tafa fini kyau kalleta karama kuma jikinta duk kwalliya ni kuma banidashi ,kuma tanada fiffike!."
Ba karamin dariya taba Anwar ba har yana rike ciki dan dariya.
Itako abin sai ya kara bata haushi ta, fashe da kuka.
Yadda yaga ta dauki abinda gaske yasa ya ajiye Akun ya kama hannunta yace."Haba Aisha keface uwar gida ita kuma amarya?".
Ta watsa mai harara."ni ban santa."
Tana fadin haka ta koma daki ,ta harde kan kujera tareda rungume hannayenta a kirji ta kuma ci magani.
Bayanta yabi saida ya kai Akun dakinsa ya ajiye sannan ya komo parlour.
Zama yayi kusa da ita dariya na shirin kwacemasa.
"Wasa fa nake miki,nakine fah na sayo miki dan ta dunga debe muki kewa ,in kuma bakyaso sai in maida   ko in bayar."
Tace."babu wani matarkace ,to in da gaske kake me yasa ka kaita dakinka?".
Dariya ya kuma kwace masa, ta fige hannunsa tana kuka ta ruga dakinta harda saka key.
Ranar kam bata fito ba.
   Bayan kwana biyu tana wasa a garden gurin ya zame mata gurin wasarta haka zata hada kasa ta kwaba da ganyen da suke fadowa tana wasa dasu.
Ranan ya kama weekend.
Anwarne ya fito sanye da kananun kaya mai gajeren wando. Yana matukar san shigannan.
Tsayawa yayi a bayanta hannunsa cikin aljihu, juyowa tayi ta kalleshi sannan ta maida kallonta ga hannunsa da yake aljihu saurin mikewa tayi tareda  boyewa a bayan bishiya a tunaninta allura zai dauko dan ta  sani ya hanata wasa da kasa.
Har yau wai fushi takeyi dashi,

Binta yayi, shi a tunaninsa batason ganinsa ne.
Hannun ta ya riko ,ta saki kuka mai sauti wanda saida yaji zuciyarsa ta buga ,ya tsani yaji ihunta ko kukanta hakan ba karamin tarwatsa zuciyarsa yake yiba .
Durkusawa yayi a gabanta yana dubanta.
"Haba Aisha ta, abin begena ,ni naga sai kiba kike kinyinkyau Aisha ta kinada kyau."
Sai kuma tayi murmushi jin kalamansa ya tabo mata inada yake mata kaikayi . tace,"Yaya Anwar na kusan kamo..."
Shiru tayi sai kuma tace."wannan matan, na kusan kamota kiba?."
Cikin rashin fahimtar inda ta dosa yace."wake nan."
Ta turo baki."Aunty Saudat mana!".
Karkada kai yayi"Uhm !,kin kusa kila ki fita,ama fa baki kaita ba."
Ta bata rai."amma ai nafita kyau tana cen tana zama da yaya Bature nima in na koma gida ,gidansa zan koma."
Yanajin haka ya bata rai a ransa yana  fadim."ai sai inga ta yadda zaki koma din."
A fili kuma sai ya bita da murmushi.
Hannunsa a nata suka shiga gida.
Wayarsace ta dau ruri . ya daga ba tareda ya furta kome ba saidan tsakin dayayi.
Magana yake kasa kasa bai dade ba ya kashe wayar.
Hada ido sukayi a yayin da ya juyo.
Ya saka mata murmushi itako ta kuma bata rai.
 
     Bikinsu shida Sumaiyya ya rage saura Sati guda momi kam  shirinta takeyi tamkar bai bata aureba shide nashi bada kudi ,duk kayan akwatuna ita tai siyayyansu da itada  kanwarta.
Momi ce zaune a parlour bayan ta dawo daga kasuwa duk ta gaji,ta daga waya ta kira Anwar kira daya ya daga saida suka gaisa tukuna tace."Anwar wai ka manta da batun auren kune har yanzun baka kama mata inda zata zauna ba?kasan dai ba zan bari ka hadata da mahaukaciya ba ! Dan haka tun wuri kasan yadda zakayi . kuma ma ba wannan ba kudi yanzun basuda yawa a hannuna saika karo ai kasan ba  akwatin kana nan yara zamuyiba dan so nake ai mata akwatunan yar gata akalla ayi mata dozen biyu ,dan haka ka kara turo da wasu kudaden."

Matar BatureWhere stories live. Discover now