chapter 28

255 10 0
                                    

**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**

Pg29.

... Ina so  in aure ta , domin hakan kade ze hanata komawa mummunan rayuwar ta ta baya..,,.
Tun da ya fara maganan kan Saudat a kasa dan bakin ciki da kishin da ya riga da ya mamaye mata zuciya ya hanata ta dago kanta balle ta iya furta wani kalma,  bata yi aune ba taji hawaye sun gangaro daga kuncinta sam bata damu data gogesu ba dan basune a gabanta ba.
Ji tayi yasa hannu ya goge hawayenta sannan ya cire Safiyaht dake hannun ta ya ajiyeta a kan gado.
Kana ya komo kan Saudat, maganarsa tayi mata nawi a zuciyarta.
Can ya nunfasa yace.,, wallahi Saudat in kikace ba kyaso ni me fasa wane , bazan so abinda ze bata miki rai ba.,,
Tabbas da zata ce masa ya fasa zeyi amma saide kash bazata iyaba don itama haka tana son mijinta kuma bata san abinda ze bata masa rai sannan kuma bataso ta haramta alkhairin daze kaisu duka ga shiga  Aljannan balle  kuma ta haramta abin da Allah ya  halasta tabbas ta sani intayi haka bata kyauta ma  kanta ba.
Can sai tasauke ajiyan nunfashi ta dago kanta sannan ta rungumo mijinta cikin kuka ta furta.
,, na amince mijina.,,
Ahmed yaji dadin hakan sosai nan ko suka shirya abinsu...

A ban garen Aisha kam yau ta tasho da matsanan ciwon kai satin ta guda kenan bata shan maganin ta duk da Allah ya kiyaye da tuni ciwon ya tashi.
Kwance take tana birgima kan gadonta sam bata san tanayin hakan ba nan ta saki kara wanda duk ilahirin gidan sai da ya amsa. Ba shiri Anwar da Sumayyah da suke daki suja fito don duba ko waye jin sautin daga dakin Aisha ke futo wa hakan ya basu daman  shiga dakin.
Nan ko suka same ta  ta canza kamanni tana ganinsu ta diro daga gadon ta je can lungu ta buya da alama tsoronsu take  ji.
Summayyah taja  tsaki.,, mtseew! .,,
Daman  wannan mahaukaciyannan ce duk kikabi kika tayar mana da hankali!.,,
Nan ko ta saka kukan munafunci.
Jikin Anwar na rawa ya  kamota.,, me na kuma kuka?.,,
Tace.,,gaskiya taban tsoro mijina,    yanzun saura kadan babyna ya Zube wallahi,   ni gaskiya bazanji dadi ba in baka hukuntata ba koma kawai ka saketa tabar gidan in  ba haka ba wallahi bakai ba da' a gudannan.,,
Anwar yace.,, okk shi kenan zan koreta amma  bazeyiwu in sake ta   ba.,,
Nan ta  tunkudeshi tana sake kurma wani kukan da ba hawaye.
Cikin rawar murya yace .,, toh shike nan my sumy , na..na.nna saketa..,,
Summayyah ji tayi tamkar an watsa mata ruwan sanyi a zuciyar tanan nan ta tabe baki.,, saki daya?,  gaskiya yayi kadan kyanshi uku .,,
.,, ai dayan ma ya isa,  dan haka kira tijjani yazo ya fitar da ita nima ta isheni .,,
Summayyah ta  rungumeshi suka koma dakin bayan wasu minutes tafito waje ta kwala ma tijjani kira cikin rawar jiki yazo ya duka kasa. Tace.,, kashiga ciki dakin wancen mahaukaciyar kakaita can bayan gari.,,
Da sauri tijjani ya bude baki yace.,, hajiya bayan gari kuma?,  ziyara zata ai da mai gadi aka kira sai ya kai....,,
Sautin maganarsa ce tagushe wanda karar marin da Summayyah ta kifeshi dashi ya maye gurbinsa , nan ya rike kuncinsa
Tace.,, har na isa in bada umarni a gidannan wani yace min ba haka ba!, toh ka gaggauta

Aikata abin da   na umarce ka da kayi in kuma ba haka  ba a bakin aikin ka! .,,
Nan ya jinjina kai ya shige ciki har dakin nata Mairo na kicin tana lekensu tausayinta ya kamata jira takeyi Summayyah ta bargurin tabi tijjani ta kaita gidan ta.
Haka yajata  har waje ya dunga tafiya da ita har deda yaje gun da ba mutane sannan ya saketa a gurin ya barta.
Mairo taso ta fita amma Summayyah na falo,  bata bar parlour din ba saida taga shigowar  tijjani sannan ta wuce daki nan Mairo ta yafi gyalenta ta saci kafa ta fita.
Duk ta lelleka ko zata ganta   amma bata ganta ba har aka fara shirin kiran sallahn magrib haka nan ta hakura ta dawo.
Tijjani ya lura da  Mairo amma tsoron sharrin Smmayyah yasa be sanar da ita inda ya ajiye taba.
Haka Aisha ta dunga yawo kwararo kwararo .
Yara suyita binta suna tsoka nan.
Haka tai sati biyu cir a waje sanyi zafi duk a kanta sai de ta kwana a bola.
Sai de tana samun abinci kasantuwar ganin ta yar karama , mutane na tausaya mata hakanyasa sai su siyo mata bread wasu kuma su bata abinci .
Yanzun haka da rana ta tashi tana tafiya kanta duk ya bashi ga tarin goruna da duk inda taga gora saita tsuguna ta dauka,  tana cikin tafiya wasu yara suka biyota wani yasa tsinke ya cakuli keyanta nan ta juyo sai ta saki kuka sannan tace.,, ni, ni matar bature?!.,,
Iyakar maganan take nan in tayi nisa ne take ambato sunan Baba da  Mama.
Saboda haka tasa ta zama duk unguwar da anganta sai adunga kiranta da Matar Bature,  inko wani ya kirata dasunan taki sai ta bashi ktautan gora guda daya.
Wata rana taba zaune kan bola inda ta saba zama wani dan matashin saurayin yazo ya tsuguna gabanta hannunsa dauke da kudi ya mika mata  takai hannu zata karba,  sai yaja hannun ya mike ya fara tafiya , ita ma tabi bayanshi har ya jata  wani kango haka yashiga tabishi ya  riko hannun ta tai kokarin kubuce watayi ya sake kamota tasa hannu ta gan tsara mai cizo a hannunsa,  ba shiri ya sake ta ya kama hannunsa dake fidda jini,  da gudu tabar gurin .
Gudu take yi so sai sam bata ganin gabanta har ta fada kan kwalta.
Wata motace babba black inkaga motar tamkar tana nun fashi.
A take ta take birki wanda yasa hankalin duk ilahirin mutanen duka yo kansu suna kallon ikon Allah 2inches ne tazarar motar da jikinta wanda in daga nesane zakayi zaton motar ta bugeta ne.
Nan Aisha ta kan kame jikin ta, ba abinda jikinta keyi inba  rawa ba.

Wani mutum ne ya bude motar ya diro da kafarsa   nima kafarsa kawai nake iya hange zan iya ce maku naga kamar takalminsa black ne wandon kuma shadda white daga inda nake ina iya hango yadda shaddar ke kyalli sai dan kafarsa daya futo fari tas amma kunsan me gashin daya kwanta a kafarsa lub lub.

Not edited!   Afwan pls.

*Follow
Vote
Comment
share*
On Wattpad @00Ruky.

Matar BatureWhere stories live. Discover now