Chapter 16

295 15 0
                                    

**Matar Bature**
**Written by**
R.S.Balarabe.

P17.

Da kyar ta bude mai sannan ta ruga dakinta a guje.
Murmushi yayi.
Sannan ya wuce parlour yasa mai aiki ta kawo masa abinci
batal jima ba sai gata ta dawo
Ta duka."na gama shiryawa".
Sannan ta wuce saida ya dan jima tukuna yaje dakin Aisha.
A kan gado ya sameta ta lullube kanta da bargo.
Ya kira sunanta.
Har sau biyu tana jinshi taki amsawa sai ma kara rufe kanta da tayi.
Yace."Aisha zoki ci abinci kinsan baki sha maganinki ba!".
Ta kara dukunkunewa.
"In kuma baki tashi ba kinsan ina da allura..".
Ai be karasa ba tai saurin mikewa tana wulka idanu.
Ya kyalkyale da dariya."kin ganshinnan a aljihuna inbaki tashi muntafi cin abincin ba sai in miki.kinganta nan.".
Ya fada yana nuna mata alluran a cikin leda.
Ba shiri ta mike suka je gurin cin abincin.
Da kyar ya samu taci sannan ya mika mata maganin batai gardama ba ta shasu, da yake ta ga allura.

Bayan mako uku ya kama ranan asabar da sassafe ya kimtsa ,gidan momi ya wuce .
Saida ya gaisa da Alh.madu sannan ya wuce dakin Ummi suka gaisa ta tambayi Aisha. Yace
"Tana nan lafiya kalau.".
Saida suka taba hirarsu sannan yaje dakin momi sallah ya same ta tanayi, a bakin gado ya zauna .
Tana idarwa tai addu'ointa sannan ta mike tareda cire hijab dinta da murnanta ta dubeshi wanda ya bashi al'ajabi .
Suka gaisa harda tambayanshi Ashi.
Yace"tana lafiya kalau."
Tace."ka gaida min ita.
Yace "toh zata ji.".
"Yaushe zaka koma gurin Sumaiyya ,kasan an maku baiko".
Ya juyo yana dubanta."wani baiko kuma momi ".
Tace ."Eh!,kaida Sumaiyya ba ,ko bata fada maka bane ai nace ta fada maka da bakinta."
Cikin mamaki yake fadin."wani kalan baiko kuma ,Kuma ba a sanar dani ba!".
"Eh ai na zata haka akeyi ,tunda ai naga kaida har aure aka daura maka tukunan na sani toh bari in gaya maka an maku baiko nanda mako guda za a sanya rana ,haba Anwar mahaukaciya fa ka auro ai in baka rabu da ita ba baka ki kara lafiyayya ba. Kuma wata daya za a sa dan bansan bata lokaci ka tashi ka bani gurin ban buka tan ganinka a kusa dani ."
Bece kome ba ya bar dakin ,dakin Alh.madu ya shiga ya zayyana masa kome ga mamakinsa sai kuma bai nuna bai san da maganan ba.
Yace."Eh hakane daman ban fada ma bane ,amma kayi hakuri kabi umarnin mahaifiyarka insha Allahu za'a ayi nasara, ya Aishan da fatan ba ita kadai ka bari a gida ba."
Murya a kasale yace."A'a ba ita kade bace akwai masu aiki."
Ya mike"Dady na zan tafi".
Alj.madu yace."toh ka gaida min diya ta".
Yace."zataji insha Allahu."
ya mike ya wuce .
Da kyar ya iya tuki izuwa gida dan kansa na wani sassara masa.
A parlour ya sameta tana faman raira kuka.
A gabanta ya tsuguna yace."Aisha me ya sameki ko bakida lafiya ne."
Ta girgiza mai kai,"ka maidani gida in dauko baby na ,ta dade bataci abinci ba mama tace in mutum ya dade beci abinci ba ze iya mutuwa ka maidani in dauko ta."
Za'ki yayi a ciki ciki duk wannan kurma ihun na yar tsanane.
Yai murmushi yace."karki damu gobe zan sayo miki wata ."
Ta hade kafada "ni de tawa nake so . kuma ni na gaji zan koma gida ina son ganin babana da mama da kuma yaya Bature."
Tana kainan ya hade rai ya tsani yaji tana anbatan sunan nan duk da shidin wanda take kira dan uwansa ne amma ya rasa gane dalilin damuwansa akan hakan.
Mikewa yayi ya nufa dakinsa.
Gadonsa ya haye be jimaba bacci mai nawi ya dauke shi.

Aisha dake parlour ta mike, dakin Anwar ta wuce ta sameshi yana bacci.
Tai dubi izuwa kwantacciyar sajensa.

Ta shiga toilet dinsa ta samu clipper wanda yake aske gemu dashi ta shafo sabulu
Ta dawo sannan ta zauna a bakin gado
Saida ta shafe kan tas da sabulu.
Jin kamar motsi a kusa dashi yasa ya bude ido yana dubanta,tai saurin boye hannayenta.

Ya zata tana wasantane hakan yasa yai ma kansa alkawarin gobe zai siyo mata yar tsanar.

Takoyi sa'a dan saida ta aske tsakiyan kan wanda ba lalai ya lura ba. Da ta gaji tamike sannan tasa gashin da clipan a dustbin tare da wanke hannayenta.
Washe gari da sassafe ya tashi ya wuce office dan an masa kiran gaggawa.
Da yamma Dr.mas oud ya shigo office dinsa tun daya shigo yake faman murmushi .
Ya samu guri ya zauna.
Yace."Dr.Anwar yaushe ka zama guy ban sani ba hmm!,lallekam ko makenkyaro ne ya fito maka.?"
Anwar sam be fahimci inda ya dosa ba.

Matar BatureWhere stories live. Discover now