Chapter 31

766 34 14
                                    

**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**

Pg 32



Yau ya kasance ranar Alhamis' Ammi da Aisha suka sauka a kasar India tare da doctor wato Dr.Shu'aib  da  yake ya kasance gobe za, a yi mata aikin , wani babban asibitin mahaukata dake birnin India yayin da suka shiga aka tarbesu izuwa wani daki,  da yamma suka barta suka koma hotel saboda ba'a kwana da patient.

Ya kama yau jumma'at babban rana yayin da aka samu nasaran yin ma Aisha aiki  sai da tayi 24hrs   tukuna ta iya farfadowa daidai lokacin wata baindiyar nurse tashigo  domin  duba ta cikin sa'a ko tasame ta  ta   farfado nan doctors sukayo kanta suna dubata  har da Dr.Shu'aib ,
Da sauri ya kira Ammi tashigo jikin ta na rawa ya dubeta yace.
,, I think hajiya aiknnan beyi ba!.,,
Ammi ta zaro jajayen idanun tashakuro wiyan Dr.Shu'aib.
,,Dr. Karya kake yi wallahi karya kakeyi,  kai kace min zata warke...!,,
Cikin sanyin  jiki ta sake shi tana shesh  shekin kuka.
Sai da ya gyara wuyan sa kana yace.
,, bawai ina nufin bata warke bane mun samu nasaran akan kwa kwalwarta da take season, but bazata iya tunawa da kome ba!..,,
Da sauri Ammi ta dago da kanta , Ta shara rama Dr.Shu'aib mari.
,, wallahi irin ku baku can canci aikin likitaba, ku kashe patient ku kashe majinyacinsa ... Toh ai daman ni abinda nake bukata kenan ta warke amma ta manta da kome.,,
Tana gama fadin haka ta karasa gaban Aisha dake kwance sai faman kallonsu take,  sauran doctors din kasantuwar bajin hausa suke ba yasa suka ma Dr.Shu'aib  congratulation suka fita.
Ammi ta shafo fuskar ta.
Muryar Aisha kasa kasa tace ,, a ina nake?  Suwaye ku?  Me nayi maku? ..,,
Ammi tayi murmushi.,, ni Mahaifiyarki ce wannan kuma dr.  ne sai yayanki yana gida.
Aisha tayi murmushi   bayan wasu minute  ta koma bacci.
Dr.shu'aib yace.,,Hajiya inason magana dake.,,
Ammi ta dubeshi tana kokarin gyara zoben gold dake hannun ta tace .,, ina jinka Dr.
Yace.,, wani hanzari ba gudu ba,  aduk sadda ta hadu da wanda tashaku sosai dashi wato mahaifinta ko mahaofiyarta ko wanda zata tuna dasu.,,
Ai ta lumshe ido kana ta bede .,, karka damu Dr.,,.

Sati daya sukayi sannan suka komo Nigeria lokaci Aisha ta gama shakuwa da Ammi dan kallon mahaifiyarta take mata , tun da Ammi ta fadamata yayanta na Nigeria yasa Aisha ta kagu sukoma don ta ganshi.
Driver ya kawo su gida,
Zayyid ne kwance akan maleliyar gadonsa . suka shiga ciki Nafi tai masu sannu da zuwa sannan ta fita waje ta anso kayansu tashiga dashi .
A parlour suka zauna Nafi ta dubi   Ammi tace.,, Hajiya in.. Daman inaso ne in fada maki Zayyid tun da kuka tafi be fito daga dakinsa ba balle yaci abinci.,,
Ammi ta zaro ido.,,  be ci abinci?,,
Ta mike ta nufa dakinsa sannan ta kwankwasa.
Shuru be bude ba can tace. ,, Zayyid bazaka bude ba,karka bari raina ya baci.,
Aisha ta biyo ta tana fadin.,, Ammi meya samu yaya,  beda lafiya ne?.,,
Ammi ta dubeta.,, yayanki baya jin magana .,,
,,Ammi bari in mai magana nasan  inyaji muryana zefito.,,
Takai hannu tafara kwankwasa kofar kafin tabudi baki tai magana ya murza key yaja kofan yatsaya yana jifan Aisha da harara.
Ta rungumeshi tana fadin.,, yaya na!,,
,,waye yayan ki? .,, yafada cikin fada.
Ammi ta jefa masa hararar da ta shigar dashi taitayin sa




Ammi ta riko hannun ta sannan tace.,, oho in kaso ka fito.,,
Ta cire key din dake kofan sannan ta ja Aisha suka koma daki.
Bayan sunci abinci suna zaune a dakin Ammi.
Aisha na kwance kan gadon Ammi tana faman latsa waya sai can ta jefar da wayar tana kallon Ammi.
Tace.,, Ammi me yasa yayana yake fushi dani ko nayi masa wani laifine?, kuma bayason ganina Ammi kibashi hakuri.,,
Ammi ta dan nunfasa kana tace.,, wayace maki yana fushi dake?,  kawai shi haka yake bai fiye sakin fuska ba...,,
Dai dai lokacin Zayyid yashugo dakin yana kokarin daura wristwatch a hannunsa .
Kaftan ne a jikinsa brown sai hula da takalmi black,  kowani kalan kaya yasa yana masa kyau gashi fari .
Ammi ta dube shi tai murmushi don aduk sadda taga yayi kalan shigar sai taji hankalinta ya kwanta.
Tace.,, my handsome Zayyid so masha Allah.,,
Ya dubi Ammi yana murmushi yai kokarin yin mata shagwabar da ya saba amma tunawa dayayi akwai yar da ya  tsana yasa ya basar kawai.
Ya samu guri ya zauna sannan yakai kallonsa ga Aisha wanda itama shi din  take kallo.
Ya wurga mata harara.,, keh!  Tashi ki fita inaso inyi magana da Ammi.,,
Ammi ta zaro ido.,,  ah lalle to sannu,  ka manta sunan tane da zaka runka kiranta da keh!,  to bari in tuna maka sunan ta ZIYADAH!.,,
Ya kuma tabe baki a ransa yanajin daci.
,,  wai ji Ammi daga tsintan yarinya ta fifita ta akai  na!  ..,,
Ammi ta katse tunanin sa da fadin .
Yawwa so nake insa Ziyadah a makaranta so a cikin countries dinnan wanne ne kaga yafi.,,
Zayyid ya zaro idanu sai kuma ya maida lura da hararar da Ammi ta jefa masa wanda be sansu ba sai zuwan Ziyadah.
,,China.,,
Ya fada a gajar ce. Ammi ta jin jina kai .,, ina so ka fara mata processing din tun yanzun...,,
Sai kuma tai shuru ta dubi Ziyadah  tace.

,,Ziyadah jeki wajen Nafi kice ta baki ice cream.,,
Da saurin tako bar dakin.
Zayyid na binta da kallon yatsina.
Ammi ta d'aka masa duka a cinyar kafar sa.
Tace.,, ina ma magana kanacen kana wani shirmen.,,
Ya shafo kwan tattun sajensa ji yake tamkar yayi kuka amma babu hali.
Ammi taci gaba da cewa.
,,sannan kaje ka sami govr. Schools inaso ayi mata certificate na cewar ta kammala karatun secondary sanan ayyi mata waec kuma a tabbata taci sannan ka nema mata babban school dake China domin anan nakeso tayi karatun inyaso anan kamin ta tafi zan sata a islamiya kuma ina bukatar kane monin me lesson wanda yasan abin da yakeyi.,,
Zayyid yajin jina kai .,, Ammi!,  wai kinsan diyar ko su waye!…,,
Beyi aune ba yaji takai hannu bakinsa ta kwabe bakin.
,, kull!  Kar in karajin kafurta Ziyadah ba ya' ta bace!  Daga yau Ziyadah ta zama ya' ta.,,
Ya mike yana kokarin fita daga dakin  ammi tace.
,,kuma kayi abin da na saka! .,,

*Follow
Vote
Comment
share*
On Wattpad @00Ruky

Matar BatureWhere stories live. Discover now