Chapter 19

243 13 0
                                    

**Matar Bature**

**Written by**
** R.S.Balarabe**

Pg20

Matar bature 20

**Matar Bature**
**written by**
**Rokayyah s. Balarabe**


Pg20

Bacci dosai ya kwasheta akan kujera wanda kanta shunfide a kan shiyan kafarsa  momi kuma na zaune kan sallaya bayan tana lazumi yayinda  Ummi kuma ta wuce gida dan kawo mucu abinci, momi ko ji take tamkar taje ta tunkude Aishan sai de da alamu tamkar  shakkanta take,  kwafa  tayi sanna ta firta a  zuciya,, mahaukaciya,  babu abinda  ze hanani in aura masa Summayah wllhi,, .
Nurse halima  ce ta turo kofan da wasu nurses din a  bayanta,  hannunta sanye a cikin irin rigarsu ta  nurses sanye take da baby hijjab hannu takai kan wuyan Anwar tana duddubashi hakan yai daidai da farkawan Aisha , idanuwanta ne sukai kan halimat din dake kokarin rike hannunsa don tayi masa allura. Da jajayen idanunta ta wurga mata harara gami da riko hannun Anwar  din
,, toh sannu munafuka yar  iska,  me zakima mijina,,.
Momi ta daka mata tsawa ,, keh!,, .
,,momi  wllhi tun dazun taketa so ta tabashi taganshi dan kyakkyawa to wallahi bazan aramiki shiba yaya Anwar nawane ni kade ,,.
Sai kuma tayi shiru kaman me nazarin wani abu tukuna tace.
,,sai dai in kinason yaya bature tunda shi ba mai allurabane so kike ki auri yaya Anwar  bayanke kina allura toh ai sai kudinga coccoke junanku,, .
Nurse halimat bata san sadda dariya ta kubucemata ba harda rike ciki da kyar ta iya saita kanta Aisha kuwa datiyar   tata mamaki ta bata sam ita bataga abin  dariya a maganarta ba hasali a gurinta tamkar shawara take bata.
Nurse halimat tace.
,, toh shikenan madam , nibazan kwace maki mijiba, mijinki mallakinkine kuma naki ke kade,,.
,,toh meyasa keke tabashi?,,.
,, saboda in duba lfiyn sa kobaki so ya tashine? ,,.

Murmushi Aisha tayi da sauri ta gida kai tana fadin  ,,eh !,, .
Tun daga lokacin suka shirya sosai saida daddare cikin iko na ubangiji Anwar ya farka dayake Aishan na bacci momi kuma taje raka   wasu da sukazo dubasu bayan kamar 10mins. Momi tadawo bata lura da ya farfado ba zuwa tayi da nufin tada Aisha gani ta dannesa don tamaida cinyarsa tamkar pillow. Lura da hannunsa na motsi yasa tai saurin kai idanunta ga fuskarsa, tai murna sosai daganin ya farka ta daga hannu sama tai hamdala ga ubangijin talikai.
Lura tayi dakamar yanakokarin sonyin magana yasa takai kuninta ga bakinsa kamar me rada yafurta kalman,, ruwa,, .
Da alama kishin ruwa yakeji sosai ta dauko roban ruwa na swan ta tada kansa ta bashi yasha.   Yasha sosai .
Da sauri tafita don kiran doctor ba jimawa suka dawo tare da wasu nurses biyu na biye dashi yai masa wasu dube dube.

Sam ta manta da lamarin Aisha dake kwance a cinyarsa aiko takai hannu ta daka  mata wani wawan duka bashiri ko tai hanzari mikewa.
Tsaki taja idanunta jajur, can kuma sai ta mike ta shige toilet da alama fitsarine ya matseta fitowanta keda wuya sukayi ido biyu da Dr.Anwar mamaki da farinciki faal a zuciyarta.
Da kamar zata rungumesa sai kuma ta fasa .
Daidai kusa da kafadarsa ta tsaya sam takasa masa magana ,tun dataga ya farfado sai tayi tunanin ko aikin nurse halimat ce.
Da yamma Aisha ce keta faman yin masa tausa , murmushi kawai yake iya binta dashi bai cika magana sai de inzeyi yanayi yana nishi hakan yasa doctor yace a dunga bashi  abinci mai gina jiki da wasu kayan marmari , jikinsa kam ya kara kyau sosai dan har a ciccire masa bandages din dake jikinsa. Daidai kunninsa takai bakinta tana mishi magana tace,, yaya Anwar kadungayin istigfari zakaji ka kara karfi kuma zaka warke sosai , ni nakosa mu koma gida kuma matarka tanacen tanata jiranka,, .
Mamakin maganganunta yacika masa zuciya aranshi yana fadin ,,anya wannan yarinyar mahaukaciyan gaskene ba pretending take masa ba?,,.
Kafeta yayi da ido tamkar me san ganin wani abu a fuskarta.
kishiyar da ta fadi yasa ya tuna a Akunsa da kuma wasan daya taba mata hakan yasa ya saki murmushin da be shirya ba.
Dakin aka turo, juyawan da Aisha tayi sai tai ido biyu da Baturen ta . tai tsalle ta fada kansa tana murna da ganimsa. Duk da anwar nacikin ciwo hakan behana kishinsa tashi ba jiyaye tamkar ya cakume shi dan kishi yai saurin hada rai.
Da kyaur yasamu ta sauka a jikinsa fuskar Anwar ko a murtuke.
Ahmed yakai garesa yana fadin sannu, tsabaragrn kishi ya hana Anwar ko kallonsa. Ahmed ya lura da hakan duk da shima dafushin nashi ya shigo don anki a sanarasa da hatsarin Anwar din sai shekaranjiya.
Ummice ta shigo hannunta dauke da basket na abinci ta diresu akan wani kujera.
Tq dubi Ahmed dake tsaya tace.,, ah mutan kaduna Ahmed yaushe ka iso,,.
Yace.,, saukansa kenan,,.
Suka gaisa sosai tana tambayansa su mama yace ,, duk suna lafiya suma sunanan kan hanya..,,.
Ya karasa maganan yana waigawa jin shigowar mutun .
Wata budurwace ta shigo dakin kanta dauke da gashindoki tana sanye da wani blue din riga da jeans sai kuma after dress dake jikinta kanta kuma ta lullube da gyale black amma berufu sosaiba . cin cingom take yana bada kara daka ganta kaga yar club  fuska kam yasha mai harya kone.
Tana zuwa bata tsaya ko inaba sai dadai kafafun Anwar ta dan matsar dasu ta zauna jikinta na gogan nashi.
Aisha ko naganin tayi haka.



Matar BatureWhere stories live. Discover now