chapter 29

286 9 0
                                    

**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**

Pg30

Fitowa yayi daga motar yai dai dai da sautin tsakin sa . fari ne tas badan naganshi da caftan ba zan iya cewa balarabe ne na gani na fada , dogone yanada fadi , ganin gashin da ya kawanta a kansa yasa na fara shakka ko balarabanne !.
Ko secs beyi ba ya  koma motar yana kokarin rufe murfin motar wata mata dake gefensa.
Cikin fad tace.Zayyid baka da hankali ne baka duba ko wani abu ya same ta ba?,    fita kaje ka duba ta.,,
Ransa  be so ba amma  haka nan ya   fita ,  ya   tsaya a gabanta amma ina warin dake tashi da hamami yasa bashiri ya juyo.
Ya kuma shugowa  motar yana kokarin tada key.
Ta daka masa tsawa wanda ba shiri ya kashe motar.
Tace.,, me yake damun kane  Zayyid,  na hanaka wannan dabi'ar ta kyaman mutane amma bakaji .,,.tana gama fada ta fita ta riko hannun Aisha wanda inka ganta a  tsaye a gurin zakayi zaton ta  sandarene dan firgici ko motsi bata iyayi ba.
Ba musu tabi matar da ta  rike mata hannu,  matar ta bude kofar baya ta  saka ta sannan  ta maida ta  rufe. Kana takoma motan itama.
Wanda  ake kira da  Zayyid kuma  bazaka iya ganesa  a  yanzun ba yadda ya hada giran sama  da na kasa.
Tsaki ya kuma ja kana yace.,, Ammi  mahaukaciya  ce fah! .,,
Ammi'n  ta  gallame  harara .,, toh seme mahaukaciya ba mutum bace,  tada mota mu tafi.,,
Haka  ko akayi yatada suka koma gida.
Wani tangamemen gida   suka nufa layin GRA ne gidan ya hadu matuka.
Bayan sun  shiga harabar  gidan momi ta  fito
Tasa dan yatsanta akai sannan ta  rimtse idanunta kana ta dubi Zayyid tace.
,,  Zayyid kaina na sara  min bari in shiga   ci,  ka shigo da new baby na inyaso ka fada ma Nafi ta gyarata tsaf sannan ta  shigo da ita sashena.,,
Tana gama fadan haka ta shige ciki.
Zayyid ko dake jingine da mota hannunsa a aljihu , haushi ya kamasa da kyar ya iya hadiye yawu dan  ji yayi makogaronsa na masa zafi, nan ko haushi da tsanar yarinyar .,, wai new baby!.,,
Yafada can kasan makoshinsa yanajin haushin kalaman Ammin sa a ransa.
Ba yadda ya iya haka ya bude mota hannun sa a hancinsa ya tsaya yana kallon ta.
Itako tai narai narai da ido ya  daka mata tsawa wanda saida yan hanjinta suka kada yace.,, dallah mala  ki fito,  kin tsaya kina kallona.,,
Tanason ta fito amma tsoronsa ya hanata fitowan.
Nan yakoma cikin gidan ya kwala ma Nafi kira wato mai aikin gidan. da gudu kuwa tafito ta tsuguna a gabansa.

Ya nuna motarsa da hannu yace.,, akwai wata girl a cikin motata ki futo da ita ki mata wanka ki gyarata sannan sai ki kaita sashen Ammi.,,
Nafi tace.,, toh! .,,
Ya wuce dakinsa sai dayayi wanka dan ji yake jikinsa na tsamin yarinyar.
Haka ko Nafin tayi ta shiga da ita bayi tai mata wanka ta wanke kanta.
Tasauya mata kaya sannan tasa hijab suka fito ta zaunad da ita a parlour.
 

Sannan taje dakin Zayyid ta kwankwasa.
Ya  sauya kaya izuwa T shirt sai top sannan kuma wando wanda be wuce gwiaarsa ba saikuma facing cap sannan black glass.
Budewa yayi Nafi ta duka   kasa tace.,,na gama shiryata saura nakaita saloon a  gyara  mata kanta.,,
,, toh ina ruwa  na konine driver? .,,
Ta girgiza kai .,, naga baya nanne shine nace ko zaka kirashine ? .,,
.,, matsamin anan,  keh!,  bari in gargade ki kada ki kara jinginani da yarinyar nan .,,
Yana gama fada ya maida kofarsa ya rufe.
Ta tashi ta fito waje nan ta sami drivern tai mishi magana sannan suka wuce bayan 2hrs suka dawo.
Ta wuce da ita sashen Ammi.
Ammi na parlourn ta tana tasbihi,  Nafi ta kaita gaban Ammi.

Ammi tace.,, Masha Allah new baby na, kinyi kyau.,,
Ta kalli nafi.,, kinga Allah ya bani diya mace , daman inata rokon Allah gashi ba nakuda  nasamu.,,
Sai ta koma ga kallonta ga Aisha dakketa faman zaro idanu.
Tace.,, ya sunan ki? .,,
Shuru batace da ita kalaba.
Ammi tace.,, gobe ki shiryata mu tafi asibiti adubata sosai.,,

A bangaren gidan Ahmed kam ya sanar da su baba, kuma duk sunyi amanna  da haka, koda Ahmed kesanar da malamin makarantar su sai yace she ze tsaya a wakilin ta.
Abu yai nisa har aka sa   rana.
Saudat   na kitchen goye da Safiyaht Ahmed ya shugo ya duddubata be sameta ba hakan yasa  ya  duba kitchen ai ko yasameta   tana faman yanka latas.
Ya runguma hannayen sa a kirji yayin da ya jingina da bakin  kofar  yana kallon su.
Jin jikinta bai bata ba yasa tai saurin juyowa suka hada ido.
Cikin shagawaba tace .,, Dadyn Safiyaht kaban tsoro.,,
Yai murmushi kana yace.,, kin manta Angon Uwar gida Saudat nake fah.,,
Ta wurgo mai harara tana tabe baki.,, uhm!,  kai de ka fadi gaskiya,  kace dai Angon Amarya mai jiran gado ko da yake ni ko sunan ta banci albarkacin   sani ba.,,
Tai saurin dafa   kansa.,,  kashh,  namanta ashe ban fada maki ba,  afwan  uwargida ta.,,
Ya fada yana hada tafukan hannayensa.
Tace.,, yanzun din ma ba fadamin zakayi ba.,,

.,, No!,  sunanta Aisha..,,
..,, wow!, ashe mutumiyata tayi takwara.,,
Yashafo cikin sa.,, kinga niba wannan ba yunwa nakeji,  kawo Safiyaht sai kiyi sauri.,,
Nan ya karbeta suka koma daki...

Da sassafe   Anwar na shirin tafiya office  Summayyah na zaune kan kujera ta hade giran sama da kasa sai faman hushi take. Haryakai bakin kofa sai kuma ya dawo,  yai zipping jakardake sanye a kafadarsa yacuro wasu kudade masu yawa kana ya mika mata.,, gashi sai ki kai ma mai jegon,  banason ranki yana baci my Sumy.,,
A yatsune ta karba kudin tana juyasu a wulakance.,, nawane wannan?.,,
Yace.,, dubu talatin.,,
Ta watsa masa a fuskarsa. ,, dubu talatin kadai,  wato salan kawayena su rai nani kenan!, to in bazaka ban dubu hamsin ba babu inda zani.,,
Ba shiri yakara curo wasu dubu ashirin kana ya mika mata.
Ta karba  a wulakance sannan yai sallama ya wuce.
Yana fita ta daga waya ta kira kawar ta akan sushirya su koma gurin boka.
Nan ko ta shirya tai ficewarta...

*Follow
Vote
Comment
share*
On Wattpad @00Ruky.

Matar BatureWhere stories live. Discover now