Chapter 6

483 16 0
                                    

**Matar Bature**

        **written by **
R.S.Balarabe.

           P7

Abu ta shigo dauke da uniform din islamiya
Aisha kuma na kwance a jikin mama ,sanye take da singlet tareda wando amma  bai kai guwiwa ba sai wasa da yar babinta take,mamane ke faman yin mata magama akan ta tashi su tafi islamiya, tun da taji sauki.
" ni ban ji sauki ba!".  Ta fad'a cikin shagwaba.
"Toh shi kenan,
d'agani tunda ba kya son makaranta".
Mama ta fad'a tana ture ta.

Tashi tayi ta haye kan gado harda rufa, dariya mama tayi don tasan 'kalau take." Toh shike nan bari in kira Dr.Nazir".
Mama ta fada tare da dauko wayarta, ba shiri Aisha ta mike, kuka ta saka,ta turo baki tana shureshuren kafa.
," ai shikenan tunda ba kya  son zuwa islamiyar sai ki kwanta kinga in Dr. Yazo sai yai miki  alurorinnan ,ko ba haka ba!".
Mama ta fada tana kara wayarta a kunni kammar maishirin kira.
Ba shiri Aisha ta jawo kayan islamiya ta saka duk da ranta be soba. Abune tace kiyi sauri karkiyi latti ga  shamsu  can na jiranki. Wato driver dinsu shike kaita makaranta dan matashin saurayi ne., harararta tayi.tace"to inna ruwanki, duk kin ishe mutane". Ta fada tana kallon mama," mama ki kore ta ta koma kauyensu".
Mama tace," in koreta kuma?, to shikenan isauri ki tafi, inkin dawo zan baki chocolate".
Tsalle tayi ta diro daga kan gadan, cikin murna tace," sai na dawo"
     Mama tace,  "Yawwa Aishata karfa ki manta kije ki ma baba sallama, kada yayi miki fada irin na rannan".
" Toh!".
Kumma banda neman tsokana a makaranta da kuma bacci, kinji ko!".
Toh, ta kuma cewa sannan ta fice.
Dakin baba ta wuce , dubawa tayi bata ganshi a parlour'n shiba, dakin ta shiga, samun shi tayi yana bacci, bubbuga kofa tayi tana kiran sunanshi, bemasan tanayi ba don yai nisa sosai a bacci. " karka tashi d'in saura inna dawo kace ban fada ma  ba!". Ta fada tana turo baki kamar yana ganin ta,hakanan ta gaji ta tafi.

Aiko suna isa makarantar suka tadda har an kulle gate don karfe uku ake zuwa dot!  Don in mutum yai latti sai de ya koma,
Shamsune ya juyo ya kalleta sannan .yace ," kin gani ko , kinyi latti!".
"Toh basai mu koma ba, daman bason zuwa nake ba". Ta fada tana wasa da gefen hijabin.
"A'h! Bazamu koma ba!, rannan sai da Alhaji yai min fada ,don haka fito muje ki basu hakuri". Ya fada yana kokarin bud'e murfin motar.
Hararan shi tayi ta gefen ido , itama ta fita.

Wani malami suka samu shine matai makin mai makarantar  ana  kiransa da malam mahmud,  sukayi musabaha , kallon Aisha malamin yayi sannan yace," Aisha musa koh!".

  Bayan malam shamsu ta buya kamar mai laifi.  shamsu yace," eh malam , kuyi hakuri malan ta danyi rashin lafiya ne...".

" kai!, wallahi malan karya yake! Na warke yazun satina daya da warke wa".
Cikin mamaki shamsu ya kalleta, don shi a ganin shi ya kareta ne, don ta bashi mamaki dukda bayau suka fara ba sun saba amma na yau yafi bashi haushi.
  Malam mahmud idon shi a kan Aishan yace "toh  mai ya hanaki zuwa da wuri? ".
Shiru tayi tana kallon shi, don tasan a nan bata da gaskiya.
"Toh tunda haka ne gaskiya muna so muga mahaifinta!, duk da ance mana tana da matsala a kwakwalwa amma tana rashinjin da ya wuce iyaka don sati ukun da suka wuce sai da tayi fada da wata abokiyar karatunta harta kai da ta ji mata ciwo".
Cikin mamaki shamsu yace," fada kuma malan?, toh wallahi ba'a sani ba , amma insha Allahu zan fada a gida , amma dan Allah malan kayihakuri ta shiga yanzun , insha'Allahu zan fada".
Girgiza kai malan yayi sannan yace," A'a! Gaskiya bazamu bari ta shiga ba yanzun don 'ka'idar makarantar ne inhar  ka wuce lokacin da ake shiga koda da minti biyar ne , bama bari ko waye ya shiga, don haka ka koma da  ita har sai mahaifinta ya zo sannan".
   Kuka Aisha ta fara don tasan inhar baba yaji sunyi fada  kashinta ya bushe.
  Komawa  sukayi  cikin mota, shamsu ya juyo ya kalli Aisha.yace,"kina fada ko?"cikin kuka Aisha tace ,"yaya shamsu  dan Allah kar ka fadama baba  zai zane nine".
"Ohh, yau nine yaya ko? Kuma kinsan yayaAbdul na gida".

Matar BatureWhere stories live. Discover now