chapter 26

250 10 0
                                    

**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**

Pg27





Sai yanzun  Aisha ta farfado daga suman da tayi jikinta yai tsami sosai , kanta taji ya fara juyawa sosai kasantuwar ta wuce lokutan shan maganin ta har so biyu,  da kyar ta iya motsawa ta kama bakin gado ta rarrafa ta hau da kyar. Jikin ta ko duk shedan bulala ga kuma ya karkarceta sosai , kuka ta saki mara sauti mai ban tausayi ,matsa nancin ciwon kanta yana kara karuwa duk bayan sec.  Ta kai hannu ta dafe kan, fuskar ta kife akan gado hawaye kawai suke iya zuba.
Kofan dakin aka bugo da karfi,  da kyar ta iya daga kanta domin ganin wanda ya shugo. Summayyah tagani ta kama kugu tana jefa mata harara.
Jin kan nata yai mata nawi yasa ta mayar dakanta.
Wani tsawa   Summayyah ta daka mata wanda saida yan cikinta suka motsa bako shiri ta dogo kanta.
Summayyah tace.,, ki tashi kije ga wanki can na mijina kije kiyi su.,,
Ta karasa tana jifanta da harara.
Ganin Aishan bata da shirin  mike wa yasa taje ta cakumo rigarta ta jawota ta fadi kasa,  haka ta jata har bayan gidan ta sa kafa ta turata tsakiyan kayan wanki.
Tace.,, maza ki wanke su kuma ki gama ga wanke wanke can shima inkin gama akawai wankin bayi .,,
Taja tsaki sannan tabar guri.
Mairo na hangensu ta window , ta bata tausayi harsai da tayi mata kwalla ganinta karamar yarinya.
Nan ko ta fito daga kitchen ta dauko washing machine ta jona bayan ta tara ruwa a pampo tazuba ruwan ta debi wasu kayan tasa kana tazuba Omo  ta kunna.
Sai ta dawo gefenta ta daga hannunta tana mata sannu sai kuma a lokacin ta saki kuka mai sauti ta  iyayin hakanne kasantuwar jin ciwon kannata ya ragu.
Cikin kuka ta daga kai ta dubi Mairo tace.,, dan Allah ki maidani Kaduna gurin baba da mama, wayyo Allah na yaya Abdul kazo ka daukeni mu koma gida...,,
Takarasa tana kuka . in banda hakuri ba abinda Mairo ke iya cemata.
Mairo tayi wanki ta dauraye Aisha kuma tayi shanya.
Bayan ta gama ta dubi Mairo tace.,,   dan Allah yunwa nakeji ki dan ban abinci inna tsoron kar in shiga yaya Anwar ya kara dukana.,,
Mairo tace.,, toh bari in debo miki.,,
Mairo ta shiga kitchen ta fito hannunta ba kome ta yarfa hannun tace.,, hajiya Summayyah ta kwashe abincin na duba kuma gurin cin abincinku naga tana gurin saide kanzo in zaki ci.,,
Da sauri Aisha ta gid'a kai alaman eh.
Mairo ta koma kitchen din ta kankaro mata kanzo ta kawo mata . hannunta narawa take ci dan wani wawan yunwa ke addabar ta .sai da ta cinyeshi tas har tana lashe kwanun ta dubi Mairo tace babu saura.
Mairo ta girgiza kai tace.,, shikenan babu,  danasani  na ajiye nawa dazun naji almajiri yana bara sai na bashi.
Aisha ta sa hannu ta share kwallan da take gangaro mata dadai lokacin aka fara kiraye kirayen sallan Magrib.
Next

Jin an fara kokarin tada sallah yasa ta leka  parlour ta window ganin Anwar na shirin barin falo yasa tasan zeje masallacine. Da sauri ta sarsarfa tana kokarin shiga dakinta taji an daka mata tsawa , jikinta na rawa ta juyo.
Summayyah ta wurga mata harara.,, munafuka ina zaki?,  wayace maki kin gama aikin ki?  Toh,  akwai wankin bayi kuma in kin gama zaki gyara dakin Anwar kafin yadawo daga sallah.
bata da zabi illa taje tayi abinda Summayyah ta umarceta da tayi da kyar ta iya wanke bayin bayan ta gama ta gyara gadon , kasantuwar bata iyaba kuma bata sababa yasa gadon ya kara baci har gwamma yadda yake. Tayi iya yinta ta bar sauran sai ta kama shara tana cikin yi Summayyah ta shigo .
Tace.,, Kai!,  me haka?,,  wannan wani irin wula kanci ne,  ince ki gyara gadon shine zaki bata!,,
Ta jawota ta fara dukanta takota ina dukanta take, haka Aisha ta dunga kurma ihu. Mairo taji su amma tana tsoron Summayyah kartazo ta hada da ita don haka sai ta kama kanta.
Cikin kuka Aisha take mata magiya.,, Dan Allah kiyi Hakuri Sumy.,,
Ji haka yasa ta dakata da bugun da take mata ta kama kugu.
,, lalle   wato leken mu kikeyi ko?,  wato har wani sumy kike kirana ?.,,
Aisha ta girgiza kai,   ta cafko kunninta ta murda.,, to daga yau Anty Summayyah zaki runka kirana,  kuma kar na karajin kin kirani da Sumy,  wannan mijina kade ze runka  kirana da sunan nan,  kinjini ko!,,
Aisha ta gid'a kai hannunta kan hannun Summayyah da take murda kunnin. Can sai kuma ta saki .
Ta nuna gadon da dan yatsanta tace.,, inaso ki sauya zanin gadon kuma  ki wanke wanda kika cire.,,
Tana gama fadin haka tajuya ta bar dakin.
Nan Aisha ta zube tana kuka, haka nan ta mike ta sauya zanin gadon da wani bayannan ta kammala sharan ta dade sosai tukuna ta gama.
Ta fito parlour ta samesu suna manne da juna.
Sim sim ta shige dakinta ta haye tsakiyar gadonta kana ta jawo yar tsananta ta kankameta a  kirjinta tana kuka tace.,, babana baya sona , mama kema ba kya sona,  me yasa zaku kawo ni nan saboda ba kwasona?...,,
A haka har bacci barawo ya sace ta.

A bangaren gidan Ahmed kam anyi suna an rada ma baby Safiyat, Saudat ta koma gidanta yayinda Ummi kuma sati  daya tayi ta koma Adamawa,    Saudat  na zaune tana ba Safiyat mama Ahmed ya shigo ya zauna daf da ita ya kafeta da ido tamkar me karantar halittun fatar ta,  ya sakar mata murmushi,
Sai kuma ya kauda idonsa a kanta yana kallon Safiyaht yasa hannu ya shafa kanta, yace.,, toh duk abinki  ba zaki kai momin ki kyau ba .,,
Saudat ta bugi hannunshi.,, kadena tabamin yarinya tunda sanda nake haifarta ba tayani kayi ba.,,
Ya bude baki yana kallonta. ,, toh shikenan momin Safiyaht ayin hakuri,  yanzunde ba wannanba daman inaso in sanar maki na samu aiki a NNPC...,,
Taja tsaki.,, ina ruwana tun da kudin in an samu badani za'aci ba yan matanka kake ba !.,,
Maganarta tayi masa zafi ainun amma haka ya jure .,,okk,  ban fahimceki ba budurwa koko mata yan iska? .,,
Ta wurga mai harara.,, aww baka sani ba to karuwanka nake nufi Ahmed,  na gaji da rashin mutuncinka wallahi,  bazan iya ba !.,,
Ahmed ya gimtse idanunsa yanajin maganganunta suna masa zafi, cikin bacin rai yace.,, ba kina  magana akan ko wacece ke yawan kiranaba, toh zan gayamaki amma ina so ki sani ni Ahmed....

*Follow
Vote
Comment
share*
On Wattpad @00Ruky.

Matar BatureDonde viven las historias. Descúbrelo ahora