Chapter 22

262 7 0
                                    

**Matar Bature**
**Written by**
**R.S.Balarabe**



Pg 23

Guyi hakeyi akan maleliyar gadonsa yana tunanin kwanakin da ya rage a daura masa aure da Summayyah,dan tunranda suka gama magana da Daddy ,ya shigarda maganan auren har aka sa rana kwana goma yau kuma gashi saura kwana uku jiyake tamkar ranar mutuwar sace ke matsowa.
Karan kofa yaji da alama shigowa akeyi. Aisha ce tashigo tanemi guri kusa dashi sannan ta zauna tai shiru, jira yake tace dashi wanni abu amma ga mamakinsa sai taji batace komeba.
Juyowa yayi ya dubeta idanunta duk sun kumbura . yayi mamaki sosai yace.,, me kuma ya same ki?,, .
Ta dago jajayen idanunta tace.,, ba kaki maidani gurin babana ba.,,
Wani tsaki ya doka sannan yajuya abinsa a ransa yana fadin.,, bakida matsala ne shiyasa.,,
Shureshi ta farayi da kafafuwanta yai buris da ita can kuma daya gaji sai ya tashi tsam ya koma capet tareda pillow'nsa  nan ma bata barshi ba ta diro kasan a lokacin tasa kuka mai kara wanda saidayaji tamkar dodan kunninsa ze balle.
Ya mike daga kwancem da yake sannan ya tsura mata ido, cikin tsawa yace.,, wai dame zanjine da aure....,,.
Sai kuma be karasaba yai shiru sannan yabimaganar da tsaki. Yamike ze fita daga daki sai kuma ya jiyo. ,, ina yar tsanan ki.,,
Jin yanayin maganar tasa sai taji kamar ze bugeta,  tai narai narai da ido zatayi kuka.,, nima bansan   inda take ba.,,
Mudi  ya nufa da nufin daukan key'n  motarsa,  saurin tashi tayi daga inda take a tunanin ta wani abun zeyi mata . ficewarsa yayi daga gidan.
Itako tunda ta jingina da bakin gadonsa a kasa bata kara motsawa bacci barawo yai awon gaba da ita.
Bacci takeyi sosai har mangaruba tukuna ya dawo samunta yayi tana bacci dan haka sai bai tasheta ba duk da mangaruba yayi yai wuce warsa massallaci sai bayan isha' tukuna ya dawo.  Baccin ya sameta take tayi , ya tasheta .,, tashi kije kiyi sallah!,,.
Yana gama fadin haka ya koma parlour , bayi tashiga tayi alwalanta tafito tai sallah sannan tafito parlour'n samunsa tayi ya kwanta kan three sitter.
Hannun dauke da remote yana duba wasu tashoshi.
Ya jawo wani babban gwali sannan ya bude ya ciro katuwar  yar tsana.
Tsalle tayi tana murna sannan ya mika mata, ta ansa tacee.,, yaya Anwar nagode.,,
Murmushi yayi mata sai kuma ya bata rai.,, kinga na saya miki yar tsana banasan rigima da kukan banza, kinji ko!,,
Ya fada yana kama kunninsa.
Ita kunnuwan nata ta rike da hannayenta ta gida kai.,, bazan kara ba,,.
Ta bashi dariya sosai dan haka yasashi yin dariyan sosai.

A bangaren momi kuwa shirinta takeyi sosai dan tuni ta sayi akwatuna dozen biyu,  ta kashe kudi sosai kuma ba ko kwandalan Anwar a ciki.

Kwance take a gadonda ranta fess jitakeyi tamkar yanzunne zata fara aurarwa.
Wayarta ta daga ta kira mahaifiyar Summayyah.
Momi tace,, hajiya ladidi ya ake ciki,,.
Haj.ladidi amsa da.,,  wallahi lfya qalau Hajiya gyarn jikine da akewa amaran zamani wllhi duk hankalin Summayyah ya tashi wai ita a dole sai nabata kudin gyaran jiki, nikuma bandasu shine nace ai lalli ma ta isa koh.,,
,,haba haba haj.ladidi lalli fah bama dadin ji,  kishiyafa zata tarar,  haba kawai gayamin kudin gyaran jikin inyaso sai in biya.,,
Haj.ladidi takai hannu suka tafa ita da yar tata summayyah.
Tace.,, uhm toh wai dubu dari ne, sai kuma wai kudin makeup tanata kiran Anwar din yaki dagawa ni wallhi hajiya duk tabi ta tadamin da hankali yanzun hakama kuka taketa famanyi ko abincib azziki taki ci.,,

Momi tace.,, toh shikenan ki turomin da account numbar dinki sai in tura miki  dubu dari biyar sai ki lallaba nima kudin hannuna duk sun kare,shikuma Anwar ki bata hakuri zan kirashi inji dalilin dayasa baze dunga daukar wayar matarsa ba,  tunda  duka saura kwana biyu ai tariga da ta zama matarsa.
Haj.laddi tace.,, toh badamu sai anjima.,,
Bayan sunyi sallama haj.ladidi suku kuma tafawa da Summayyah.
Haj.ladidi tace.,, ke wallahi boka yayi aiki,  matsiyaciya,  kinga shalelta inkinje ki tasa kudi karkibarshi koda da biyarce,  uwarta haka tayi ma babanmu.,,
Ta saka hannu a bakin zaninta sannan ta ciro wasu kudade  ta mika mata.,, kinga wannan dubu hamdinne ki kai ma malamin mu, tunda wasu nakan hanyar zuwa. Maza dauki gyalenki ki tafi ba bata lokaci.,,
Ansan kudin tayi sannan ta dauki gyalenta ta yafa ta fita.
Gud'a haj ladidi tayi.,, kudi sunzo muci kudi mubar kudi,,.
Momi nan   take ta daga waya ta kira anwar a  Office dinsa yake ya dawo kenan daga duba patient lura da yayi wayarsa na kawo haske kasantuwar ya  saka ta a silent. Duba wa yayi sunan Momi ne yafito a screen din wayar dan haka yadaga yana sallama, a gaggauce ta amsa  kana ta fara mishi bambami ta inda take shiga ba ta nan take fita ba sannan tace.,, maza ka tura ma Summayyah kudin lalle, tun ma ba'ayi auren ba to wallahi karka  kuskura ka batamin rai inba haka ba zan gamu dakai.,,
Tana gama  fadin haka ta katse wayar.
Samm ya kasa gane inda Momi ta dosa kwata kwata ta sauya daga Momin da yasani Mominsa me sonsa da kaunanarsa wacce kome yakeso kokari take yi taga ya sameshi sai gashi yau itace take kokarin yin masa mafi abinda ya tsana a rayuwarsa kuma ta keson ganin tashin hankalinsa da dagulgula rayuwarsa.
Wasu hawaye yaji sun cika masa idanu yai kokarin taresu amma kash sun ruga zuviyarsa aiwatar wa .

Tdugunawa yayi a kasa ya fara rera kuka tamkar karamin yaro wani irin tsanar Summayyah yakeyi wanda baki baze iya misaltashiba sai dai ita zuciyar , ita kade tasan irin radadin da dacin datake ji.
Dunkula hannayensa yayi ya buga akan makeken table din dake gabansa,  ba abinda yafi mishi ciwo illa sauyawan Momi sam ta canza.
mikewa yayi ya shiga toilet ya gyara fuskarsa futowarsa daga toilet dinne aka fara nocking kofar,, come in!,, .
Ya  furta   kana ya zauna akan  kujeear sa,Nurse halimat ce ta shigo hannunta cikin aljihun rigarta sannan  ta zauna a daya daga cikin kujerun dake office din , murmushi ta farayi sannan tace.,, Dr.Anwar ya jikin.,,
,,lpy normal Alhamdulillah.,,
Ta kuma wani murmushi .,,amm,  ya madam..,,.
,,lafiya!,, ya fada hakanne a dakile dan besan maganarsu ta tsawaita,ya mike yana kimtsawa.
Itama ta mike .,,Dr. Sai an jima.,,
Tana gama fadan haka taja kofan.
Bayan ta fita da seconds shima ya fita    gida ya koma.
Tun daga dosowarsa ya farajin sautin ihun Aisha sosai sautin ke futowa,horn  yayi amma ba'a  budeba dukda sautin  ihun nata na kara karuwa,  tunawa da yayi ita kadece a gidan sai mai gadi yasa ya hanzarin futowa daga motar bema ko tsaya rufewaba da karfi ya bangaji kofar gate din ...



Godiya me tarinyawa da jinjina ga masoyana, ina jinjina   maku da hakurin   da kukeyi dani 😍 har kulum takuce me kaunan ku akoda yaushe.

¢¢Karfa ku manta kuyi following dina
Keep on voting✨
Keep on comments ✨
It really makes me feel... 💃🏻💃🏻⭐ kun gane ai😀¢¢

    * Wattpad*
    * 00Ruky*

Matar BatureWhere stories live. Discover now