chapter 23

264 10 0
                                    

**Matar Bature**
**written by**
**R.S.Balarabe**

Pg24


Summayyah ya gani a tsaye a kanta tana faman murde mata kuni ita da kawarta Salima dake gefe tana faman zugata.
Hannu ya daga yakai mata wawan mari a kuncinta wanda saida gurin ya amsa. Ta juyo ta dube shi da jajayen ida nuwanta cikin tsiwa tace.,, yaya Anwar ni ka mara!,
Tsaki yaja kana ya kai hannu ya jawo Aisha da jukinta ya cika da raunin dukan da Summayyah tayi mata.
Summayyah ta gida kai sannan tayi kwafa ta fice daga gidan itada kawarta.
Sunyi kokarin su nemi mai adai daita sahu amma kasantuwar unguwar GRA ne yasa sam baka gani abinhawa sai jefi jefi.
Nan suka gaji suka fara takawa , wani mai adidaita sahu ya shigo layin ya ajiye wata mata nan sukayi ciniki drop ya kaisu har gida tun a hanya take kuka har suka isa gida fuskarta ta kumbura tai suntum jikin haj.ladidi ta fada tana sake kwarma wani ihun. A gigice haj.ladidi tace.,, lafiya ? Me ya sameki, waya taba minke? .,,
Kawarta saliman ce ta cabe da.,, munje gidan Anwar ne wai kawai dan ya ganmu muna dukan banzan matarsa shine ya kashe mata fuska da mari.,,
,,mari?, toh ze gane bashida wayao, mara kunya fitsararre, rabu dashi yau ai kamar gobe ne daga gobe an daura aure shike nan dasun shigo hannu shida uwarsa zasu gane basuda wayo,kinga kiyi shuru mutane na zuwa kar su gane mu.,,
Summayyah ta mike sannan ta koma daki Salima ta bi bayanta.

Jikin Aisha yai jina jina sosai Anwar kuma na kokarin yin mata dressing a goshinta kuka takeyi sosai. Bayan ya gama ya maida kayan aikin sannan ya bude fridge ya ciro Maltina ya bude ya mika mata, taki karba.
Ya kara mika mata.,, kinga kisha in ba haka ba zan miki allura,,.
Da sauri takai hannu ta fara sha , saida ta sha kusan rabi tukuna ta ajiye.
Tunawa da yayi ya bar motarsa a waje yasa ya koma ya shigo da ita, lokacin da yake kokarin shugowa da ita harabar gidan yasa ya tuna da dayar motar tasa mai tsadan gaske, jinjina kai yayi kana yai parking dinta Sannan ya dawo parlourn
Kusa da ita ya zauna tana bashi tausayi yarinyar, duk da ita din abin tausayine ta taso ba uwa ga lallura da take fama dashi gashi an dauketa ankaita can wani gurin inda shima wani kalubalenne ga kuma wata kaluballen me daci wacce take shirin fuskantarta.
Tagumi yayi yana kare mata kallo nan ya lura siririyace sosai . Idannunsa yakai kan matsakaicin lips dinta, sai a lokacin ya lura kyau takeyi inta turosu.
Sai kuma ya fara tunanin shagwabanta ya tuna yadda take juya idanunta harara take yi amma kamar me lumshewa. Murmushi yafarayi sosai wanda bemasan yanayi ba.

Jiyayi ta dunguri kumatunsa.
Ta turo baki.,, dariya kake min koh.,,
Takarasa maganar dakuka.
Nan hankalinsa ya dawo jikinsa shi sam besan murmushinsa tafitoba a tuna ninsa iya zuciyarsa ce kawai.
Nanko ya dake. Ya mike ya kunna Tv
Yana kokarin duba wasu chanal tace.,, MBC3 zaka sa.,,
A ransa yace.,,ai daman nan nake nema sarauniyar rigima.,,
Yana saka chanal din yakoma yazauna sam be gane komai amma ga mamakinsa sai yaga hankali kwance take kallonta.
Nan yakuma gyara zama ,gabansa yai mugun bugawa Lokacin da ya tunada gobane za'a daura aurensa.
A bangaren Momi kuwa tuni mutane sun cika gidan anata hadahada,
Momice tana kidinshige a akan gadonta ta jawo wayarta ta latsa number'n Inna mai aikin su Anwar.
Ko fara kara batayi ba ta daga wayar cikin ladabi ta gaida momi.
Momi tace.,, da fata ba kina gidan Anwar ba.,,
Ina baki na rawa tace.,, A'a Hajiya wallahi tun randa kikace inbar gidan ban kara zuwa ba inama gida yanzun.,,
Wani murmushi Momi tasaki tana kara gyara rikon wayar.,, yawwa haka nakeso , yanzun inaso kizo nan gidana akawai aiki.,,
,,toh hajiya ga ninan zuwa, Allah ya kara arziki.,,
Momi ta kashe wayar ta ajiye a gefe.
A ban garen gidan Ahmed kuwa Saudat ce ta tashi da matsanan c ciwon ciki Mama na toilet jin muryanta yasa tai saurin fitowa tana ganin halinda take ciki tai hanzarin kiran driver suka wuce asibiti bayan awa daya ta sambalo baby girl fara soll ,kamarsu daya da Ahmed.
Sai washe gari aka sallamesu , Ahmed yai mata huduba har yanzun basa magana.
Ahmed ya kankame yarinyar a kirjinsa yanajin wani natsuwa da son yarinyar na kara karuwa a zuciyar sa.
Saudat ko duban inda yake batayi balle tasan da abinda yake. Wayarsa ce ta dau ruri nan ya ajiye babyn a gefenta sannan ya wuce . kuka ta saki ji takeyi ta tsanesa sosai.
Ummi ko tayi murna sosai. Aisha na bacci yunwace keta addabarta nan ta tashi, waje ta fita gurin tijjani mai gadi.
Yana zaune da radio a kunninsa yana ganin ta, ya mike ya fara gaidata.
Tace.,,yunwa nake ji.,,
Yace.,, hajiya to bari naje in sayo miki a can kasuwa,,.
Ya kama hanya ze tafi sai kuma ya juyo.,,hajiya, Inna me yafaru shuru har yanzun bata dawo ba.,,
Tace.,, toh ni zaka tambaya, ni ka tafi kayi sauri inajin yunwa.,,
Fita yayi ta nemi bakin bishiya ta zauna ga iska dake ratsata ta koina wani kadan gare ya sauko daga bishiyan ya fado kan kafarta da ihu ta miki lokacin kuma Amwar ya dawo.

Yai horn ba'a bude ba sai kuma ya jiyo sautin ihunta nan ma ya razana a zatansa Sumayyace ta kara dawo wa. Ba shiri ya foto daga motar wannan karon ya kulle bude kofar da zeyi daidai itama tana kokarin futowa sukaci karo nan ta rungumeshi ta matse jikinta sosai.
Yace.,, me yafaru Summayyah ta zo ne.,,
Ta girgiza kanta tana kuka tace.,, kadangare ne .,,
wani tsaki ya saki.,, toh kadangarenne kike ma kuka .,,
Sai kuma ya saki dariya.,, to sake ni kin shake min wuya.
Lokacin mai gadi ya shigo hannunsa rike da leda na shinkafa da wake Anwar yace.,,ina kaje haka ka barmin gida ba kowa.,,
Yace.,,kasuwa naje sayo ma Hajiya abinci .,,
Ya ansa ledan ya bude sannan ya mika masa .,,ansa karka kara kawo min abincin kasuwa gidana.,,
Da rawar murya ya amsa da .,,toh Alhaji.,,
Sai ya juyo ya dubi Aisha dake manne dashi yace.,, kekuma saukamin daga jiki.,,
Lura dayayi batada niyan sauka yasa ya kaita mota suka shigo tare.
A kan kujera ya direta, kuka ta saki tana shure kafafu.
Yace.,, toh meya faru kuma, nasan yunwa ke damunki ko? .,,
Ta jinjina kai.
,,toh jirani inyi wanka inyi salla sai muje restaurant muci abinci koh.,,
Nan ta saki murmushi. Bayan ya kimtsa tsaf haka ko akayi suka tafi restaurant bayan sun dawo ya nemi tijjani daya dubo masa mai aiki. Da yake da yamma suka dawo yakama Saturday weekend.
Fita yayi waje yana shan iska bayanda ya rage kayan dake jikinsa T-shirts ne a jikinsa da kuma gajeren wando wanda yadan wuce gwiwarsa da kadan.
Fitowa tayi ta sameshi a tsaye yana kallon bishiyar mangoro yai ya'ya sosai gashi sun nuna.
Bayanshi taje tai tsalle ta tsunguli keyansa. Ya juyo ganin itane yai kokarin kamota ta ruga yana binta nan yai mata tarko ya kamota.
Dukkansu sukayi dariya sosai yakejin sonta da kaunan ta na kara karuwa a zuciyarsa .,, ko yaushe zata zama cikarkiyar matarsa?,, ya fadi a zuciyarsa , ya furzar da iska.
Tijjani ko dake can bakin gate zaune sai faman washe baki yake...

¢¢Comment,Vote & Share¢¢
*Wattpad*
@00Ruky.

Matar BatureWhere stories live. Discover now